ANTASO DAGA DUNGURUN

,AN TASO DAGA DUNGURUN ZUWA  KADUNA, SABUWAR HEDKWATA.
.
Tun da yake an kammala dukkanin muhimman ayyukan da aka shirya, akwai isassun giaje da ma'aikatu da ofisoshi, sai aka shiga shirye shiryen tasowa daga dungurun zuwa Kaduna.
.
A Dungurun an kwaso duk wani kayan gwamnati mai ameani, kamar giajen katako da dai sauran su. Babban abin da ya kawo jinkirin tasowar daga Dungurun, barkewar yakin duniya na daya. Amma cikin shekarar 1917 kusan duk an tare a Kaduna ne.
.
Gwamnatin mulkin mallaka, ta taso zuwa kaduna a ranar 16 ga watan nuwamba na shekarar 1916 , ma'aikatar Fidaburdi a ranar 26 ga watan Nuwamba suka taso. Amma ma'aikatar Safiyo da Baitulmali da sakatariya sai a karshen shekara suka iso. Wadanda suka taso daga basani su ne ma'aikatar laeiya da ta 'yan sanda.
.
A cikin karamin lokaci, watau wajen misalin shekaru hudu (1912-1916) an shiga manya manyan gine gine a kaduna. An yi wadannan gine ginen cikin rahusa , saboda arhar aikin lebura da Turawan suka samu. An kashe eam 116,150.00 wajdn gina garin kaduna kafin a tare baki daya.,

Post a Comment

0 Comments