TAKAIRACCEN TARIHIN MARIGAYI IYAN ZAZZAU 1950-2020
An Haifi Alh. Bashir Aminu Iyan Zazzau a 26th December 1950 a rimin tsiwa dake birnin Zaria. Maigirma Iyan Zazzau Da ne wajen marigayi Maimartaba Sarkin Zazzau Mal. Muhammad Aminu daga gidan Sarautar Katsinawa a Zazzau.
Yayi Karatun Allo (Alqur'ani) da na Addini a birnin Zaria. Ya shiga makarantar Kwaleji ta Alhuda Huda dake kofar Doka Zaria daga shekara ta 1964 - 1968. Ya shiga Kaduna Polytechnic inda ya sami Diploma a Accounting And Auditing daga shekara ta 1970 - 1971. Ya shiga Jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria yayi Digiri a Accounting a shekara ta 1972 - 1975. Ya ketara kasar Ingila Jami'ar Kent Canterbury domin yin Masters a M. SC Finance a shekara ta 1982.
Maigirma Iyan Zazzau yayi aiki da Gwamnatin Jahar Kaduna a matsayin Accountannt daga 1970 - 1975.
Yayi aiki a kaduna state Polytechnic a matsayin Chief Finance Officer daga 1976 - 1979
Marigayi Maimartaba Sarkin Zazzau Alh. Dr. Shehu Idris CFR Allah ya gafarta masa yayi ma Alh. Bashir Aminu Sarautar Iyan Zazzau a 23rd Febuary, 1979 kuma hakimin Sabon Gari Zaria.
Iyan Zazzau ya Zama Shugaba a Boards of both state and Federal Government Parastatals and Companies tun shekaran 1980. Ya zama Shugaba a Board of Aviation technology Zaria, Jahar kaduna kar kashin Ma'aikatar Aviation ta Kasa daga shekara ta 1990 - 1994.
Ya zama Darakta a kamfanoni Da da yawa a fadin Nigeria.
Ya Halarci Samina Kala kala a kasar Nigeria da kasashen waje Kamar Ingila, Amerika da shauran kasashe.
Yana da mata 4 sannan ya haifi yaya maza da mata guda 33 biyu sun rasu saura 31
Allah Ya jikan sa da rahama yasa ya huta Ameen ya Allah
0 Comments