WANENE DR MAMMAN SHATA?

WANE NE DR. MAMMAN SHATA?

Kasancewar tarihi abu ne mai Matukar Mahimmanci dangane da nazari musamman fagen ilumi Wannan dalili ne ya haifar da yin tsokacI a kan tarihin Mamman Shata duk la cewa abune me matukar Wuya kawo Cikakken tarihin Shata gaba daya.

A cewar Dr. Ibrahim Kankara a hirer da aka yi da shi cikin shirin ZABI DA KANKA na Rediyon Freedom Kano, a ran 31 maris 2010 " An haifi Lawal (Dr) Mamman Shata a shekara ta 1923, shekarar Mutuwar  shanu kamar yadda Hausawa ke mata lakabi a cikin garin Musawa da ke janar Katsina a yau, sunan Mahaifinsa Ibrahim Yaro Ruruma, sunan Mahaifiyar sa Lariya.
Dr Mamman Shata ya taso ne ya sami iyayensa suna kiwon shanu domin asalin Kakanninsa Fulani ne da suka taso daga sanyinna ta jihar kebbi a yau.

Masana Sun nuna Mamman Shata yakan Je kiwon ya dawo sannan ya je
Makarantar Allo (tsangaya) da dare. Ya fara karatu a wajen 1928 a makarantar Malam Ahmadu. Daga nan sai Makarantar liman Dan Dauda, Sa'annan kuma dukkanninsu makarantun dare ne.

Masana Suna  cewa tun a wantnar lokacin aka fahimnci zakin muryar Mamman Shata domin a wake suke yin karatun, masana sun aiyana tasirin har cikin wakokinsa. 
 Misali a cikin wakar sa da yi wa Hajiya Indon Musawa inda ya ke cewa:-

"Ta yi kwance kamar kumsa
Ta dan Karkace Kamar Ruhu'a
Ga dan fadi kamar Basin lallan hari"

Masana sun nuna tun a wannan lokaci, Shata na karatu  yana tunanin niman na kai saboda haka a wajen 1932 sai ya fara yan  Tallace-Tallacen kayan masarufi, babbar sana'ar sa da aka fi sanin sa da uta , ita ce tallar goro. Anma ko kafin ya fara wannan sana'ar ya yi tallar alewa. Yana da wani ubangida mai suna Tunau mai Alewa wanda kan dora masa tallar alewa domin ya kai kasuwa ya sayar a karshe ya sami abin tabawa. Bincike ya nuna aamari kan yi irin wadannan sana'oin wadanda a kan dauka a ka, kamar au alewa da goro a cikin Baka. Ahi goro sukan rika sayar da shi a kwarya-kwarya. Sukan rika rera wakoki iri daban daban don jan ra'ayin mai saye a yayin talla.

Sani Baban Musa Shine mutum na farko da ya fara ba wa shata tallar goro Lokacin babu basukar  balle mota, duk attajirai busa jakuna suke zuwa kasuwa, Masana sun nuna cewa tun a wannan lokacin Shata ya kware a rera wakoki iri daban daban. Shi yasa ma yakan fi kowa cinikin goro a kasuwa, ko kuma alewa. Masana Sun nuna cewa wannan lokacin ne Lawal  ya zama Shata sai dai akwai ra'ayoyin daban daban dangane da asalin kalmar "Shata". Wasu na da ra'ayin cewa lokacin da yake tallar alewa, idan ya zo ya iske mutane a kasuwa sai ya yi rawa ya yi juyi, sannan ya miko wa jamaa alewa ya ce "Sha ta". Amma bayani mafi inganci shi ne wanda ya nuna cewa wani mutum mai suna Baba Magaji Salamu, dan uwan Shata ne wato Basanyinne ne. Shi ne ya sanya masa suna Shata. A nan ma bayani ya rarraba kan dalilin da ya sa masa sunan.

Wasu na ganin wai idan Mamman ya aamu kudi ya kashe, idan Magaji ya tambaye shi "Ina Kudi?" Sai ya ce "Na yi shata da su". In an ce "Menene Shata"  sai ya ce "Na kashe". A wannan lokacin babu wannan kalma shi yake amfani da abarsa. Daga nan ne Magaji ya daina kiransa Mammalo sai dai Shata. Har Magaji Salamu wanda Allah ya yi wa rasuwa a 1996 ya bar duniya bai daina yin masa kirari da "SHATA-KUDI-MIJIN-MAIDAKI" ba.

Zamu cigaba Gobe Inshallah ku kasan ce damu

Head of Admins Kasar Zazzau
Abdullahi Yahaya
#15august2021

Post a Comment

0 Comments