WA AKE BA SARAUTAR MADAKI A KASAR ZAZZAU?

MADAKIN ZAZZAU
Sarautar Madaki a zazzau ta samo Asali ne daga Mulkin Habe, amma su Habe suna kiranta Madawaki kuma ita ce sarauta mafi girma cikin sarautun Hakimai, 'Ya'yan sarki, kuma shi ne shugaban rundunar mayaka. Ba'a nada Sarki ko cire shi sai da yardar Madaki. Kuma shi ne jagoran Hakimai a kowane irin taro kamar gaisuwar fada ko gaisuwar Shekara. Amma a mulkin daular fulani an sami bambanci inda sarautar Madaki sai Babban dan Sarki kurum ake ba wannan sarauta. Wanda ya fara wannan sarauta A Mulkin daular Fulani shi ne Malam Yamusa, Sarkin zazzau, a zamanin Malam Musa, Sarkin zazzau kuma daga kansa ne Madaki ya fara sarki kuma darajar wannan sarauta ta daukaka ta zama muhimmiya a wannan masarauta ta zazzau. Bisa tsarin Mulkin Fulani, Madaki shi ne Babba cikin 'ya'yan Sarki, kuma shi ne shugaban 'ya'yan Sarki duka. Sarkin zazzau Malam Yamusa, shi ne ya gaji Madaki ma kaye na Habe, a zamanin Sarkin zazzau Malam Musa.



KIRARIN MADAKI
" KACI KACALA,
GOJE UBAN FADAWA,
ABUBBUGARI SANDAN FADAN SARKI,
KODA MASO ZUBAN JINI
KODA MASU SHASSHAWA
KARI KIKI BABBAR LAYA
WANDAWA DA KAI AKA GAYYA
DAN UBAN GABASAWA."
Wadannan kalmomi na kirarin Madaki, duka kalmomi ne na jaruntaka a kan yaki saboda saravar asalinta ta mayaka ce.

Post a Comment

0 Comments