Wannan sarauta ta Iya ta samu asali ne daga Habe Kuma sarauta ce ta mace a wancan Lokaci. Wannan sarauta ta iya ana ba da ita ce ga Matar sarki ko Uwar sarki ko 'yar Sarki kuma aikinta a wancan lokaci, shi ne ta lura da sha'ani da shirye-shiryen aure a fada ko aurowa ko idan an 'yanta baiwa zuwa ga aure duk dawainiyar da za a yi ita ce za ta lura da haka.
.
Sarautar Iya a wannan tsari na mulkin Fulani ya Bambanta da tsarin Habe ko da yake an taba samu sau daya cikin daular Fulani a zamanin Mulkin Malam Musa Sarkin zazzau, inda ya ba babbar 'yarra sarautar Iya, kuma iya ta farko a Daular Fulani. Amma yanzu sarauta ce ta 'ya'yan Sarki kuma tana da Hakimci mai Girma. An daina ba da ita ga mata.
.
KIRARIN IYA
DAFKARIRI TOKAN YAKI,
IYA CE MAKAMA KAFA GA SARAKI
IYA CE MAKAMA KAFA GA 'YA'YAN SARKI
DN UBAN GABASAWA.
Wannan shi ne kirarin iya. Ana nuna matsayinsa da karfin sarautarsa kamar haka: Dafkarari tofar yaki. Ma'ana, karfin da ba ya tabuwa ko a kau da shi, a wurin yaki. Haka kuma Iya ce makama kafa ga saraki, iya ce makama kafa ga 'ya'yan Sarki. Ma'ana, idan ya ce to haka za a yi ga bukatar mutum, haka kuma ga 'ya'yan sarki. Wannan iko na Iya na da alaka da asalin sarautar saboda kasancewa sarava ce ta Uwar Sarki, shi ya sa aka sami wannan Kirari.
.
KARIN BAYANI: wannan sarauta ta Iya tana daya daga cikin manyan sarautun 'ya'yan sarki yanzu a daular mulki na fulani na zazzau. Kuma 'ya'yan Sarki da dama daga kowane gidan sarautana Fulanin zazzau sun yi ta saboda irin daukakarta.
0 Comments