AYYUKAN DA SARKI KE GABATARWA KODAYAUSHE

AYYUKAN DA SARKI KE GABATARWA KODAYAUSHE
.
1. Tabbatar da zaman lafiya tsakanin Jama'ar kasa ta hanyoyi daban daban.
.
2. Tabbatar da zaman lafiya tasakanin 'yankunan mulki da jama'arsa.
.
3. Warware rikice rikicen iyaka a tsakanin 'yankuna.
.
4. Warware rikice rikicen addini a tsakanin jama'a mabiya addini ko akidar addini daban daban.
.
5. Ziyarar yankunan gundumomin mulki don gane wa ido halin da suke cik'
.
6. Ilmantar da jama'a kan wasu shirye-shirye na gwamnatin Tarayya ko ta jiha domin talakawa.
.
7. Taimaka ma gwamnati wurin harkar karbar kudaden shiga.
.
8. Gabatar da koke koken jama'a ga gwamnati.
.
9. Halartar taruka wanda za su kawo hadin kan jama'a da kawo ci gaban kasa zuwa makoma nagari.
.
10. Raya al'adun gargajiya don kada wasu lalace ko su bace.
.
11. Bai wa gwamnati shawarwari a kan harkokin da suka shafi jama'ar kasa na yau da kullum.
.
12. Ayyukan masana'antu na gida da na waje don kawo ci gaba a kasa.
.
13. Bai wa jama'a hakkinsu a kan shugaban da suke so ya mulke su.
.
14. Wakilin jama'a tsakanin su da gwamnati, haka kuma wakilin gwamnati tsakanin ta da jama'a.
.
Duk irin wadannan ayyukan ne masu wahala da ili dora alhakinsu a kan sarakuna kuma su ne suka tsaya akan haka. Saboda haka a koda yaushe ya kan raba hankalinsa biyu ne, daya na tare da shi, daya na wajen ayyuka da aka dora masa. Kuma ko da yaushe ba ya samun sukuni har sai ya ga ya kammala wannan aiki, a kodayaushe daga daya cikin wadannan bukatuwa ya taso, sai ya yi iyakacin kokarinsa ya ga ya cimma nasara a kan abin domin nauyi ne da ya rataya a wuyansa.

Post a Comment

0 Comments