Makarantan Kwaleji na Barewa da ke, Zaria, an kafata tin a shekarar 1921 , wanda ya kafata shine gwamna janaral na najeriya a wannan lokaci wato Sir Hugh Clifford.
.
Itace makarantan Gaba da firamare na farko da ta yaye manya manyan kusoshin najeriya da dama. Ta yaye Prime Minister, ta kuma yaye Head of States na najeriya guda biyar , Gwamnoni sama da Ashirin, ministoci da 'yan majalisu, Manyan Gwamnonin
Bankin Nigeriya uku, da dai mutane manya manya sanannu ana najeriya daga cikinsu harda Sultan na Sokoto.
.
Kafin a fara kiranta da BAREWA COLLEGE ana kiranta da Government College, Zaria, an fara kiranta da BAREWA a shekarar 1971.
.
Via: Kassar Zazzau a jiya da yau
0 Comments