BULLOWAR BARE - BARI LARDIN ZAZZAU da KAFA GARIN BARNAWA. Da samuwar GIDAN MALLAWA da GIDAN BARE-BARI
.
Bunkasar zazzau da mulkinta sun zo karshe bayan da Bare-Bari suka mulkin zariya ba tare da yaki ba a shekarar 1734! . Zariya wanda ta mallake kasashen Hausa sai ga ta kwaram karkashin mulkin barno.
.
Daga wannan lokacin sai ta koma kai harari ga Barno a kowace shekara, watau dai sai da ta dandana irin mulkin mallakar da ta saba nunawa sauran kasashen Hausa.
.
Da mulkin zazzau ya koma hannun Barno, sai shehun Barno ya aiko da wakilansa guda biyu, daya zuwa gidan Sarautar zazzau, daya kuma zuwa babbar kotun shari'ar zazzau. Duk wani abin da zai wakana a wadannan wurare sai da izinin shehu. Kowane sarki idan za a nada shi, to wakilan Shehun Magajin Malam shi ke nada su. Aikin Magajin Malam ne nada sarakunan zazzau, watau dai shi ne wakilin Shehun Barno mai kula da nadin Sarauta.
.
Haka kuma mai kula da sha'anin shari'a a babbar kotun zazzau mai suna Kacalla, aikinsa ne na tabbatar da duk ayyukan shari'a a kotun zazzau, Shehun Barno na samun isasshen rahoto. Magajin Malam da Kacalla su ke tabbatar da mulkin Barno a Birnin zazzau. Haka dai zariya ta ga wannan mulkin mallakar har Bullowar Jihadin Fulani. A wannan zamani an ce wai rukunin Bare-bari na da yawa sun shigo lardin Zazzau, da yawa daga cikinsu sun zauna a zariya.
.
KAFA GARIN BARNAWA
.
A lokacin da Barno ke Mulkin zariya, watau bayan shekarar 1734, wasu rukunin bare bari karkashin wani malami kuma waliyin Allah sun zarto kudancin zariya inda suka zauna a rugar fulanin da ke gabas da kakuri. Wannan rugar fulani ta samu shekaru masu yawa da kafuwa kafin zuwan bare bari kamar yadda aka yi bayani a baya.
.
Shugaban wannan rukuni sunan sa Malam Kilba. Babban malami ne sosai, cikin hanzari gari ya tashi haikan aka canzama wajen suna zuwa "BARNAWA" saboda bunkasan sa sanadiyyar zuwan Bare Bari. Wannan gari ya samu sunan sane daga Barno ( wato dai Barno- Barnawa , kamar yadda ake cewa Kano - Kanawa).
.
Wannan gari tayi tashe sosai, ya zamana Hausawa, Fulani da Bare Bari suna zuwa neman karatu wurin wannan Malamin.
.
A lokacin da shehu Mujaddadi Usman Bin Hodiyo ya bayyana ance wai ya aiko wa Malam Kilba yana bidar sa wajen Jihadi. Amma wannan Lokacin Malamin ya tsufa sai ya aika masa da manya almajiransa guda biyu a madadin kansa. Sunan Manyan almajiransa Musa Bamalli Da Yamusa . Wadannan manyan almajira Allah ya ba su hazikanci da ilmi da fasaha da kwarjini ga kuma dimbin karatu.
.
Ance Malam Bamalli da Malam Yamusa sun Bar Barnawa zuwa wajen Shehu Usman Mujaddadi a cikin farkon Shekarar 1804. Sun karfi tutar jihadi daga wajensa a wannan shekara, an kuma bukace su da zuwa zariya. Malam Musa Bamalli a matsayin Madaki watau kamar matsayin Sarki, Malam Yamusa kuma a matsayin Madaki. Sun nufo zariya domin Yin Jihadi watau daukaka Kalmar Allah.
.
Musa da Yamusa sun taho zariya da askarawan Jihadi dari uku da talatin da uku (333) , sun auka wa zariya da yaki Ranar sati goma ga watan Zul-hajji 1804 A.D. A safiyar wannan rana ce Askarawan shehu suka gwabza da zage-zagi.
.
Wanda ke sarautar zazzau a wannan lokacin shi ne Sarkin zazzau Muhammadu Makau. A wannan ranar Sarki Makau da jama'arsa suna bayan gari wajen sallar idi. Bayan da aka idar da salla, sai sarkin ya samu labarin cewa ai Fulani sun mamaye zariya. Gashi basu yi shirin yaki ba kuma badaman su koma cikin zariya domin dakko kayan yaki, a hakanan suka gwabza , daga karke dai sarki Makau ya gudu, watau dai an ci Zariya ke nan. Sarki Makau ya yi fama da Fulani, amma daga karshe sun sami immasa a cikin shekarar 1825 A.D
.
Malam Musa Bamalli sai ya zama sarkin zazzau na Farko a mulkin Fulani, shi ne kuma ya kafa gidan Mallawa ( MALLAWA DYNASTY), a sarautar zazzau. Ya yi sarautar zazzau cikin 1804-1821.
.
Bayan rasuwar sarkin zazzau Malam Musa Bamalli sai Madakin sa Malam Yamusa ya hau gadon sarautar Zazzau. Shi ne ya kafa gidan Bare bari a sarautar Zazzau (BORNO DYNASTY), Shi ma ya yi sarautar zazzau cikin 1821-1834.
Allahu Akbar! Barnawa babban gari na a wannan lokaci, Almajiran Malam Kilba wadanda sukayi karatu a Barnawa duk sunyi sarautar zariya wanda ta mallaki makekeyar kasa da kabilu iri iri. Irin wannan sabon salon hari na far wa jamaa bayan sallar idi ya sa sauran garuruwa nadama. Ganin yadda aka yi wa sarki Makau, tin daganan sai ya zamana suna idi a cikin gari ko kuma idan zasu fita sufita da shirin yaki.
.
Garin Barnawa ya cigaba da bunkasa har zuwan turawa inda jama'a suka fara fitowa wajen gari suna zama, ta hakane SABUWAR BARNAWA Takafu
.
Ance wani Malami Limami mai suna Mal. Rabi'u shi ne ya kafa sabuwar barnawa. Bakatsine ne ya fara zama a kano. Alokacin da turawa suka bullo ya fito waje ya gina masallaci ya hada tsangaya ya zauna, ahaka ahaka mutane nafitowa har gari ya bunkasa sai aka samai suna SABUWAR BARNAWA.
.
Lokacin Sarkin zazzau Ibrahim garin sabuwar barnawa ta kafu. Ya rasu lokacin Sarkin zazyau Ja'afaru.
.
A 1948 sarki Jafaru dan isiyaku yanada Muhd Lawal Sarautar Barnawa.
0 Comments