BULLOWAR FULANI LARDIN ZAZZAU

BULOWAR FULANI LARDIN ZAZZAU, KAFA GARIN KINKINAU DA KYAUTAR DA DAJIN DOKA ( Dajin da aka kafa Garin KADUNA)
.
Ance wai Fulani sun shigo Lardin na zazzau domin neman wajen kiwon shanu. Gabar kogin kadduna ya ba su sha'awa kwarai da gaske. Saboda sun ga ciyayi koraye shar, rani da damina.
.
Rukunin Fulani na farko sun kafa ruga a wani wuri dab da bakin kogin Gabas da Kakuri Kurmin Gwari. Kamar Kakuri , babu hakikanin lokacin da suka zo suka kafa. Rukunin Fulani na biyu sun fito daga garin Bebeji ta kasar Kano, karkashin wani Bafillatani mai suna Aliyu Magajin Jammu a cikin farkon karni na Goma-sha bakwai, ana jin lokacin da Ishaku ke sarautar Zazzau.
.
Aliyu Magajin Jammu ya baro Bebeji tare da iyalansa da barorinsa da garken shanunsa ya yiwo kudu har zuwa wani wuri mai katon dutse ( kusa da tsohon filin Jirgin Saman Kaduna) da ke kusa da Afaka. A kusa da wannan babban dutsen, sai Aliyu Magajin Jammu ya kafa garken shanunsa, sannan ya koma cikin garin Afaka da zama, ya kuma sa wa wannan sabon garken  shanunsa suna "KARINA".
.
'Ya'yan sa da barorin sa sai suka shiga aikin su na kiwo a Karina, sai kullum su tatsi madara su kai wa Maigidansu da yake zaune a garin Afaka. Cikin kankanin lokaci sai arzikin Aliyu Magajin Jamma ya bunkasa sosai. Shanu , awaki da tumakai sai hayayyafa suke yi. Karina ko sai ta zama alkarya jamaa suna zuwa suna zama
.
Ganin yanda arzikin wannan Bafillatani ya tayar wa da Hausawan Afaka hankali sosai, sai suka shiga shawarwarin yanda zasu bulloma wannan Al'amari. Sai suka kaiwa sarki korafin su cewa ga wani bako nan idan baa koreshi ba arzikin sa zai bunkasa har ya zama yazo ya mallak kasar gabaki daya.
.
Wanda ke sarautar Afaka a wannan lokacin shi ne sarkin Afaka Mai Babbar Hula. Shi wannan sarkin ana yi masa lakani da Mal Babbar Hula domin idan ya sa wata hula tasa, to ko wanene ya saurara masa. Idan yaga dama yana iya yin wa garken shanun tsawa shanayen su bace. Idan haka ta auku sai bafillatanin ya kawo goro sannan zaa bashi izinin ganin shanun sa.
.
Sarki Mai Babbar Hula ya shahara a zamanin sa sosai don kowa ya taka, to ya taku ba a garinsa Afaka ba har da Makwabtansa. Amma labarin da sarki ya samu game da Aliyu Magajin Jammu ya tayar masa da hankali kwarai dagaske, saboda haka sai ya kirawo wannan bafillatani ya umurce shi da ya bar masa garinsa , ya tafi duk inda yake so ya kafa gari a cikin kasar Afaka, amma dolensa ne ya bar garin acikin hanzari.
.
Samun wannan umurnin sarki ke da wuya, sai Aliyu Magajin Jammu ya ta kwashe koma tsantsa da iyalan sa ya shillo , ya yiwo kudu da afaka har ya zuwa gabar kogin kadduna inda ya kafa sabon gari. Garin Karina da ya baro sai ta ci gaba da girma a hankali.
.
KAFA GARIN KINKINAU
.
Da Aliyu Magajin Jammu ya taso daga Afaka ya zo gabar Kogin Kadduna sai wajen ya kayatar da shi domin kuwa akwai isasshen ruwa da ciyayi koraye shar. A wannan waje ne sai ya kafa Sabon Gari.
.
Da zuwan Fulani wannan sabon guri, sai Magajin Jammu ya ce a sa wa wajen sunan baiwarsa Keke. Sai aka sawa wannan wuri " Unguwar Keke". Fulani suka manta da abin da Hausawan Afaka suka yi musu, suka ci gaba da hidimomin kiwo , a hankali sai sabon garin nasu ya tasamma girma.
.
KYAUTAR DA DAJIN DOKA
.
Sarki Mai Babban Hula ya yi nadama daga bisani game da korar Bafillatanin da ya yi na nuna hassada ga talakan kasarsa kuma ma bako wanda yazo daga nesan duniya neman arziki,  sai ya shiga shawarwarin yanda zai yi ya gyara zumuntan sa da Aliyu Magajin Jammu, don Haka sai ya Bashi kyautar DAJIN DOKA.
.
Sarkin Afaka ya ce da Aliyu " Allah ya kawo ku sabon wuri (watau unguwar keke" waje me albarkar ruwa da ciyayi, saboda ka samu wuri isasshe don kiwo na baka jejin da ke gabas da wannan Gari ( Dajin Doka)" . Aliyu ya yi Godiya da kuma nuna farin cikin sa da wannan " Muhimmiyar " kyauta da aka yi masa
.
Babu muhimmanci ga wannan kyauta da akayi na Dajin Doka a wannan Lokacin, saboda dajin doka bashi da kyau saboda cike yake da manyan itatuwa da namun jeji iri-iri. Duk da haka wanda ya yi kyautar da wanda aka yi Wa kyautar babu wanda ya fahimci muhhmmancin sa sai zuwan Turawa. A wannan daji ne kuma dajin Magajin Jammu, turawa suka kafa wani babban gari mai suna Kaduna.
.
Anyi gudun gara an fadama zago , mutumin da aka kora a garin Afaka saboda tsoron kada ya mallake garin, sai gashi wanda yayi korar ya mai kyautan waje me matukar mahimmanci . Sai gashi Ya mallaki duk sauran kananan garuruwa da manyan garuruwa bana cikin lardin zazzau ba ma duk lardunan Arewa baki daya.
.
Da Unguwar Keke ta Habaka sosai sai sunan garin ya koma " KINKINAU" . Wannan gari ya shahara kwarai da gaske a zamanin sa. Ta bunkasa da manyan  Malamai Hausawa Da Fulani Adanda sukan zo daga nisan duniya. Galibinsu sukan zo daga Zariya. Akwai dakin shari'a da gidan Alkali inda manya manyan masana shari'a ke zuwa daga zariya. Garin kinkinau sai ya yi ta bunkasa ya yi kusan fin duk na makwaftan garuruwa.

Post a Comment

0 Comments