BULLOWAR GWARAWA (GBAGYI)
.
Akwai kabilu iri-iri a Yammaci da Kudancin Lardin zazzau. Gwarawa watau kabilar Gbagyi suna da dangantaka da bangaren ko sasin kogin kadduna domin tun safiyar fari suka bullo zuwa wurin suka zauna a 'yan kauyuka masu dama a kasar afaka.
.
An ce wai kabilar Gbagyi su ne mazaunan farko a kasar Barno sun bar kasar barno saboda Juyin Islama, inda suka watsu zuwa kasashe kamar su Katsina, Zariya da Birnin Gwari. A wani kaulin kuma an ce Gbagyi sun tafi Abuja bayan da Sarkin zazzau ya kafata. Shi Abuja dan Sarkin Zazzau Muhammad Makau ne wanda Fulani suka kora daga Zariya A lokacin Jihadin Shehu Mujaddadi Usman. Shi Abuja mutum ne gajere mai tsawon kafa biyar da rabi ( 5' 6'') kakkaura ne kuma ajur. Saboda jansa ne ake ce masa 'JATAU' , wani lokacin kuma ace masa "ABUJA". Shi Allah yayi shi jarumi ne, don Haka ne ake masa kirari da " JATAU SHUGABAN GARI MAI GANUWA KO FAGEN FAMA KAI KE FARA FITAR DA JINI"
.
Abuja ya kafa garin da ya sawa sunan sa Abuja ranan Lahadi goma ga watan sha'aban 1825. Gbagyi sun tafi sun zauna can garin Abuja. A nan wurin inda Sarkin zazzau na 62 watau a sarautar Habe akwai kabilu masu yawa kamar Gbagyin Genge da Gbagyin Yamma da kabijar Koro da Gade da kamar yake. kabilar Gbagyi sunfi sauran kabilu yawa, amma sai kabilar Koro suka danne su. A wannan zamani, lokaci ne na yake-yake tsakanin kasar kansu, a wannan wajen sai suka tashi a tutar babu, domin ba su da kasar kansu. Sabaoda rashin mallakar kasar kan su ne sai suka zo daga baya bayan kura ta lafa suna masu neman izinin zama ba domin nuna fifikon karfi ba.
.
Duniya a tsaye take a wannan lokaci mallakar kasa sai da karfin tuwo. Wannan dalili shi ya sa sai ka gansu a kasa wadda ba mallakinsu ba. Wadda kuma a kowace shekara sai sun biya harajin kasa . Idan ba a ba su izinin zama ba sai sukan tattara ina-su ina-su su ci gaba.
.
Saboda yawan kabilar Gbagyi a lardin Abuja da kuma rashin samun kasar kansu, sai a hankali suka watsu, galibin su suka yiwo cikin kasar Afaka suka kafa garuruwa da dama. Akowace shekara sai su kai harajin kasa ga Afaka.
.
Tarihi ya nuna acan lardin Neja yankin da ke karkashin Zazzau kafin shekarar 1908, kabilar Gbagyi basu mallaki kasar kansu ba, amma suna da garuruwa a wurare masu yawa a cikin lardin.
A wani kaulin kuma an ce Gwaraman da da ke zaune a gabar kogin kadduna Gbagyin Yamma watau " Gbagyi Wyi" . Su wadannan kabila sun fito daga Birnin-Gwari , asalinsu Kuta-Fika ne wadanda suka zo daga kasar Barno inda suka zauna a kuta a cikin 1600 A.D . Daga nan ne suka watsu wurare masu yawa.

0 Comments