DUNGURAWA DA LAYUKAN DA SUKA KAFA
.
LAYIN KWANTAGORA
Wbnda suka kafa wannan layi su ne: Babbar Gari da sarkin fawa Muhamman da kwasau da kokari Dan Malam da sharu Tunku da sarkin fawa dangero da gambo mahauci da Audu keffi aboki fari da Galaima kwantagora.
.
LAYIN PRINCE EDWARD
Wadanda suka kafa wannan layi su ne:-
Sarkin Alaro Malam isa da Audu na malam da jatau yola da kwakwalagi da mista Amawo da Mista nortey da Malam nuhu sarkin Makera mai Damisa da bako mai Mota da Babban Bawa malam Aminu ilori da malam Ta'idu da sarkin Hakuri da Mista sagoe Mai Burodi da daddy foto da Abubakar bamaiyi da Malam sharif da Barankaca da Gambo direba da adamu wushishi da Madam kashi kano da Habiba zariya.
.
LAYIN HADEJA
Wadanda suka kafa wannan layi su ne:- Bukar mandara da mai Dariya da Garba Tela da Shehu Mai siyasa da Mista Ladipo da ungulu Dan sarkin Lakwaja a Madaki wushishi.
.
LAYIN KANO
Wadanda suka kafa wannan layin su ne:- Sarkin hausawa Babale da sadau soja da mai Buruji da Musa kirinki da Malam Rafa da Audu na sarkin kano da Garba Tasawa da korau dillali da Mista Johson da samanja Gaji da Usman uban Ndabado da hauwa Tarwada Baki kamuwa koda haki da bagobiri dan Janhol da Mijin Aya da Liman Malam Musa da Malam Baffa Gwambe.
.
LAYIN GWANDU
Wadanda suka kafa wannan layin su ne:- Sarkin Alaro bagobiri baban Baito da belu makerin sarki da Musa dan Audu wanzami da Dan sakkwato Mai Turare da usman Makeri da sarkin Mutane Malam Hussaini.
.
LAYIN IBADAN
Wanda suka kafa wannan layin su ne:- Adamu Mijin shatu mai karfin Doki da Dan Duniya Direban Gwamna da titi mai kudin kotu da Malam Musa Bussa da inuwa Magini da Dan Gambara da sarkin yarabawa oga Dada da shatu Gindingyare da Malam Ali mai Yanka da Madam kwantagora.
.
LAYIN KABBA
Wadanda suka kafa wannan layi su ne Muhammadu dan kosassa da ibrahim dankaza da Buraimoh Tafinta da Yakubu tela da Malam garba mai kaji.
.
SAURAN DUNGURAWAN DA SUKA KAFA LAYUKA DA DAMA SU NE:-
mamman zinda Odilan, Gwamna da sarkin zango malam dodo da liman malam jiya da budu da Gambo jaki da nakauru da Babaraba da Mista Okonkwo da Usman Dogo mai Kwado da Linzami da Sambo Algazaru.
.
Dukkan wadannan layukan da aka lisafta , za'a samu mutum guda ya zauna a layuka fiye da biyu saboda wadatar fili da saukin samunsa, don haka zai yi wuya a tabbatar da tahakikanin wadanda suka fara kafa layi tun da ba abu ne a rubucf aka tarar ba. An yi wannan Ab nd don a dan nuna wa jama'a yadda layuka suka fara kafuwa, akwai Dungurawa da Tsofaffin sojoji masu yawa wanda wannan littafi bai kawo su ba.
.
PHOTO : Wannan hoton layin kwantagora ne a cikin shekarar 1936 , ga gidan sarkin fawa Muhammadu Makasau Kurdn Gwamna Lugga a gefen dama
0 Comments