FILIN JIRGIN SAMA NA FARKO A GARIN KADUNA
.
PHOTO: Wannan hoton kan jirgin kasa ne na farko a Arewa. Ya fara zirga zirga tsakanin Dungurun zuwa Wushishi a shekarar 1901. Kuma da itace "kwakwalagi" yana amfani kafin samuwar Kwal.
.
Filin jirgin sama na farko a garin Kaduna shi ne babban filin sukuwa da yanzu ake kira da Dandalin Murtala ko "MURTALA SQUARE". A wannan fili ne jiragen sama suka fara sauka.
.
Jirgin sama na "imperial Airways" ya fara sauka a garin kaduna a cikin shekarar 1925. Kananan jirage uku ake amfani da su a wannan lokaci. Sarkin zazzau ibrahim shi ne ya eara kawo ziyara a wannan filin jirgin sama, har ya shiga aka yi shawagi da shi. Jiragen ba'a amfani da su da daddare, da zarar yamma ta yi sun daina zirga-zirga ke nan saboda rashin fitilun lantarki irin na yanzu. Da rana lokacin da jiragen suke amfani sai a turnika hayaki a wurare dabam dabam a wannan fili saboda matukin jirgi ya gane wajen sauka daga sama. Wannan hayaki idan ya yi sama zai nuna wa matukin jirgin filin sauka.
.
A haka aka rinka amfani da wadannan jirage kafin samuwar filin jirgin sama irin na zamani a garin kaduna. Ameani da jirgin sama ya saukaka zirga zirga cikin hanzari a wannan zamani.
0 Comments