HANYAR MOTA ZUWA ZARIYA

HANYAR MOTA ZUWA ZARIYA
.
Tun kafuwar garin Kaduna jama'a ke zirga zirga bisa jakuna, dawaki, basukuri da Motoci saboda hanyoyin mota a cikin gari sun gyaru sosai. Zirga zirga tsakanin kaduna zuwa zariya bisa mota ba ta samu ba sai a karshen shekarar 1919..
.
Hukumar Local Authority ta zariya, sun dauko aikin hanya daga zariya ta kwaba da sabon Birni. Ita wannan hanya ta hade ta Firdaburdi wanda ta tashi daga Kaduna Zuwa Rigacikun. An faro wannan aikin hanya nd da ranin watan satumba, an kammala ta kafin karshen shekarar 1919..
.
Budewar wannan hanya ta kara sanya jama'ar garin kaduna sun mallaki Basukuri da Motoci, don a tsakanin 1/1/20 - 31/3/21, an yi rajistar Basukuri guda 167 da kuma motoci 6.
.
Budewar wannan Hanya babban mataki ne na kara bunkasar garuruwa. Duk wani mai hali in baya bukatar bin jirgi to sai ya bi mota don hanyar ta bude.

Post a Comment

0 Comments