KAFA GARIN KADUNA

,RASHIN DACEWAR GARIN DUNGURUN DA KAFA KARIN KADUNA SABUWAR HEDKWATA
.
Ko da yakd Gwamna Lugga shi ne ya zabi Dungurun ta zama hedkwata, amma ba ta gamsar da shi ba . Zaman Dungurun ba shi da dadi ko kadan, yanayin garin ya cika zafi , da rashin armashi. Saboda wadannan dalilai, babban kwamishinan wannan lokaci Sir D. P. C Girouard (1901-1908) , ya yi Allah wadai da zaman wannan gari. Wannan matsalolin da ke gallabar mazauna Dungurun ta tsananta sai kara fitowa fili ta keyi, Bayan da Gwamna Lugga ya sami karin girma ya zama Gwamna Janar , sai ya ta da kaimi sosai na ganin cewa an bar garin Dungurun Zuwa Kaduna.
.
AN KAFA GARIN KADUNA SABUWAR HEADKWATA
.
Zirga zirgar jirgi tsakanin Baro zuwa Kano ta yi nisa, a cikin shekarar 1911-1912. Wannan ya bai wa Turawa ganin ni'imar da Allah ya yi wa jejin da ke gabas da hanyar jirgi, Arewa da gadar jirgin kogin kaduna. Wannan abu ya sa Turawa godewa Allah domin abin nema shekara da shekaru ya samu. Watau wajen da zai dace da zamansu. Wannan jeji da suka gani zai dace da kafa hedkwata, zai yi kuma kyau a muhallinsu.
.
Kafa hedkwata a wannan waje zai dace sosai saboda an shigo cikin kasar Hausa ke nan , abin da akd son yi tun shekaru da suka wuce. Idan an kafa wannan gari ba zai kusanci wani sarki ba kuma balle a sami tangarda wajen shugabanci.
.
Amma abinda ya fi kayatar da Gwamna Lugga game da wannan jejin sh ne babu wani gari a cikinsa sai manyan itatuwan doka a namun jeji. Idan har an kafa gari a cikinsa  ba zai kawo kishi tsakanin kabilu ba tun da wata kabila da aka tasa da sunan gari.
.
Lugga dai ya daidaita shawarar cewa zai yi gine gine a karkara, wurin da za'a yi gine gine kuwa shi ne kusa da gadar kogin kadduna, inda soja suka riga suka yi ofisoshinsu, watau wajen Kakuri da Makera. Amma sai aka yarda a yi su a sashen Arewacin kogin, watau Dajin Doka, saboda hangen amfanin yin hedkwata a inda baa tashi wata karkara ba.
.
Kafa garin Kaduna a inda ba'a ta da wata kabila ba na da babbar fa'ida. Ba don komai ba sai don kawar da kishin kabilu, wanda yin hakan sai ta zama kwantacciyar hedkwatocin Kanada da kuma Austuraliya da Afrika ta kudu. Ba don komai ba sai don duk wadannan hedkwatocin an kafa su a wurare da ba karkashin kowa ba watau "NEUTRAL GROUNDS".
.
Garin Kaduna ya taso da bakin jini, a farko dai tun yar tangardar da aka samu wajen kafa garin, wannan gari ya sha suka da yawa. An yi ta dauki ba dadi tsakanin gwamna lugga da sarakuna da kyar ya samo kansu, sannan suka ba shi goyon bayan kafa garin , don sun hangi kada gurin ya girma ya bunkasa ya fi garuruwan sarakunan yankin.
.
Lokacin da Gwamna Lugga ya hada Arewa da Kudu, sai ya shirya sabon garin nan watau Kaduna don ya zama hedkwatar duk Nigeriya. Amma sai Ofishin sakataren mulki dake ikko suka ce ba su yarda ba tun da yake sai anyi tafiyar kwana biyu kafin sako ya iso ta jirgi daga teku. Saboda idan suka aiko da sakonsu mai daraja zai dade kafin ya sadu da gwamna a kaduna kuma amsosin da zaa bayar ba za su iso bakin teku ba cikin lokaci,,  Har yadda za a iya sa su cikin jirgin Ruwan "BUSTA". Ko da yake dai ba safai sukan sami yin haka nan din ba.
.
Kaduna da yake tana tsakiyar wurin da babu kowa sai daji, da ita ce tafi dacewa da a yi haka nan. Akwai isasshen ruwan sha, fili da za a iya kara budawa , saannan ga fili isasshe na yin babban filin jirgin sama. Tashi sama na wurin kamar kafa 2,000 daga bakin teku, saannan kuma yanayin kasar mai kyau ne. Hasali ma dai tana da dukkan abubuwan da ikko ba ta da su, kuma da ba ta sami mummunan mugun abu ba na ikko , watau iskanci wanda yake shi ne duk mai mutunci bai jure masa.
.
Hasali ma dai a taron nan na London Mista Lyttelton ya ce " Ni a ganina, game da gardamar da ake yi cdwa tsada ita ce za ta hana a ta da hedkwata zuwa Kaduna wannan kururuwa ce fiye da kima".
.
Al'amarin baba ne gare mu domin kuwa a cikin yankin kasar nan, a ikko akwai tashar jiragen ruwa nan, Apapa dakd ketaren gabas, to tan ne kuwa du galinn kayan cinikin Nijeriya ta Arewa wanda aka sayo da wadan da ake sayar wa suke biyowa. Gaskiya ne kam a kan kawo kaya da dama fatakwal, amma dai mafi yawa sun fi bi ta Apapa wanda uk ya sami rike ikko to shi ke da Apapa kd nan don haka yana iya torhd hanyar cinikin Arewa.
.
Wannan dalili shi ya sa ake rika jin cewa hankali zai fi kwanciya idan aka bar ikko a hannun Gwamnatin Tarayya, wanda a cikin harkokinta kowa na iya tsoma baki. Idan da kogin Kadduna zai iya daukar jiragen ruwan busta da maida kaduna hedkwatar Nigeriya ya tabbata. Garin Kaduna ya samo sunan sa nea daga Kogin Kadduna, kamar yadda Nijeriya Ta samu daga sunan Kogin Neja.

Post a Comment

0 Comments