KOTUN SHARI'A A CIKIN SABON GARIN DOKA da kafa MIXED COURT
.
PHOTO: wannan hoton kotun daukaka kara ne na Arewa a Turawan Mulki suka gina a shekarar 1920 a garin kaduna.
.
Saboda ayyukan station Magistrate sun yi yawan gaske, saboda haka sai aka kada akin shari'a a cikin sabon Gari. Ita wannan kotun sai ta shiga aikin jin kararrakin jama'ar gari, su kuma suka daina zuwa kangiwa domin shari'a . Ana hukunta masu laieuka sannan kuma wannan kotu na taimakawa wajen samun kudi, watau "REVENUE" .
.
Tun kafin kada wannan kotun Shari'a aikin Station Magistratd hukunta duk wani mai laifi a kaduna ko kuma sauran garuruwa. Ita wannan Magistrate tana matsayin Babbar kotu ke nan domin kuwa ana jin kowane irin kararrakin jama'a . Misali idan zalunci wani mutum a wata kasa kuma ya kawo kara a kotun station Magistrate dake kaduna. Sai ma'aikatan wannan kotu su shiga neman bayani a gare shi, ita wannan Magistrate Court ta tanadi dakunan saukar baki masu kara da abinci domin masu tahowa daga nisan duniya, domin sukan zo a jigace wani zibi ma ba a cikin hayyacinsu ba. Da isowar mai kara sai ya shiga kada kararrawa yana cewa na kawo kara na kawo kara wadansunsu ma har birgima sukan yi domin Baturen mai shari'a ya tausaya musu. To wanda ya zo a jigace sai a bashi abinci ya ci sannan a kai shi masauki, kashe gari in ya dawo cikin hayyacinsa sai ma'aikatan shari'a su shiga neman bayani. Liman Malam Jafaru wanda shi ne Magatakardan Gwamna shi ke rubuta bayanin mai kara da ajami, sannan ya bayyana wa station Magistrate. Nan da nan sai mai shari'a ya aika da yan bincike domin su tafi garin da ake bukacesu , su kuma binciki yadda ainihin al'amarin yake kafin su taho da wanda ake kara din, kaein nan da kwana uku an gama binciken, an kuma zartar da hukumci, kowane nd aka samu da laifi sai a hukumta shi kamar yadda shari'a ta bukata.
.
Kafa kotun shari'a a sabon garin doka a cikin shekarar 1920, yara wa station Magistrate aikace-aikacen Shari'a da yawa. In har shari'a ta zo gare shi to tafi karfin Alkali ke nan , sai kotun koli wanda takd karkashin station Magistrate.
.
Alkalan farko wadanda suka fara shari'a cikin sabon kotun Garin Doka sune Alkali M. Sa'idu sai Alkali Malam Lukumanu. Bayan wadannan alkalai sauran da suka yi alkalanci su ne; Alkali Malam sani daga shi sai Alkali Malam Sh'aibu Banufe.
.
KOTUN MIXED COURT
Ita wannan kotu ta samo asali ne tun cikin shekarar 1930 ya zuwa wannan lokaci, garin kaduna cike yake da jama'a kabilu iri-iri masu addinai daban daban. Da darko dai jama'ar gari na karkashin Dokar "SUPRDME COURT" Wanda ita ma tana karkashin Satation Magistrate amma saboda kabilu dabam dabam wadanda galibinsu mutanen kudgncin najeriya dake zaune a sabon garin Doka, sai aka ga hukuncin alkalai bai dace da su ba saboda bambancin al'adu. Yadda al'adu kan bambanta kuwa wuri uku ne: 1. Aure 2. Gado 3. Jayayyar 'ya'ya. Amma sauran laieuka kamar sata, eada da bashi duk daya nd. An kafa mixed court a shekarar 1932 a matsayin "Grate C" ita wannan kotun da aka Kafa a kaduna, tana jin kararraki tsakanin musulmi da wanda ba musulmi ba. Wadanda suke zaune a kaduna. Su musulmi sai a yi masu hukunci bisa shari'ar alkali ya zartar, su kuma wadanda ba musulmi sai a hukunta su a al'adunsu. Mutanen da ke kawo kararraki sun kunshi mutanen igabi cikin Tudun wada da sabon garin Doka.
.
Alkalin wannan kotu yana da muftai har guda uku wadanda suke shugabannin yarabawa da ibo, su wadannan su ke ba da fatawa wajen shari'ar mutanensu bisa al'adunsu. Su wadannan muftai masana ne bisa shari'a da al'adu. Na ukun shi ne Malam Bahaushe Masanin shari'a. Duk wadannan masu shari'ar , suna karkashin "President" watau shugaban kotun baki daya. Da farko dai President din Mixed court shi ne Hakimin (DISTRICT HEAD) Igabi. Ita wannan kotu ta taimaka sosai wajen taeiyar da shari'a, kawo zaman lafiya da lumana a cikin Sabon Garin Doka da kewaye.
0 Comments