,Wannan hoton Malam Attahiru ne wanda ake yi wa kirari da " Tinjimin Malami Uban Tijjani, Kan da sarauta, cikin da karatu, hannun da rubutu, kafar da takama, zuciyar da kyauta, bakin da hadisai".
.
Malam Attahiru ya taho daga fadar sarkin kano a wajen shekarar 1927, inda ya koo da zama a garin kaduna. Zaman wannan Malami a wannan gari na Sabuwar Doka ya taimaka kwarai wajen bunkasarsa da tafiyar mulkin Turawa ta fannin shugabanci. Yana daya daga cikin kusoshin Gwamnatin wannan lokaci a matsayinsa na Shugaban Malamai da Mai ba da shawarwari ga shugabannin mulki.
.
Wajen jama'ar gari kuwa, Malam Attahiru ya yi taimako wajen koyar da jama'a domin ya yi nisa ga fannoni da dama. Shi mutum ne Malami mataffannoni wanda Allah ya Albarkata da dimbin sanin hadisan Annabi Muhammadu (s.a.w) da tarihi da hisabi da dai sauran fannoni . Allah ya yi wa Malamin Muhibba da kwarjini da iya tafiyar da Mulki. Shi mutum ne karimi ga son jama'a don duk inda ka ga babban Malami ka ga Malamai na biye da shi. Allah ya jikansa da Rahama.,
0 Comments