Marigayi Alhaji Usman Mairiga (OFR) haifaffen Anguwan Liman. Shine ɗan ƙasa na biyu da ya zamo Editan Jaridar Gaskiya tafi Kwabo. Shi ya karɓi Alhaji Abubakar Imam. Ya yi aiki a matakan gwabnati da dama tunda gwabnatin lardi har zuwa ta Tarayya. Kana ya yi Director a Hukumar Alhazai ta ƙasa. Marigayin mutum ne mai sauƙin kai da sada zumunci. Baban ɗansa shi ne Alhaji Adamu Usman Mairiga wanda maaikaci ne a ofisin lardin Zazzau. Allah Yakyautata makwancinsa Ameeeeeen
0 Comments