ME YA KAWO TURAWA AREWA?
=== KASHI NA BIYU ===
.
Komawar Dr. Martin Amirka ke da wuya sai ya ba da rahoton tafiyars Afirka, ya kuma tashi haikan wajen ganin wasu rukuni na Amirkawa sun fara tasowa daga Amirka zuwa Abeokuta. Amm abin takaici sai wannan gagarumin shiri ya ci tura, saboda wasu dalilii, idan da ba haka ta faru ba da yanzu akwai zuri'ar Amirkawa zaune a Jihar Ogun.
.
Dalilan da suka kawo rashin nasaran wannan tafiyan suna da yawa. Alokacin da Dr. Martin ke fafutukar kwasar Amirkawa Bakaken Fata zuwa Garin Abeokuta sai yakin basasa ya barke a kasar Amirka. Wannan ya tilastawa bakaken fata shiga aikin soja, shima madugun tafiyar sai ya shiga aikin soja. Saboda kwazon Dr. Martin shine Bakar fatan farko da ya kai mukamin Manjo a cikin rundunan sojan Amirka watau "UNION ARMY" . A wannan lokaci har ya samu yabo daga shugaban Amirka, Mista Abraham Lincoln. Yakin basasa ya kawo cikas kwarai da gaske wajen ci gaba da shirin kwaso Amirkawa zuwa gida afrika.
.
Shugaban yarbawan Abeokuta, ko da yake sun yarda da shirin amma ya kauce wa al'adarsu , don al'adarsu aa ta yarje wa wani bare ya zo ya mallaki kasa a kasarsu ba. Yake yaken da kasashen yarabawa ke fada da shi tsakaninsu a wannan lokaci bai ba da damar samun sukunin ci gaba da shirin ba. Manyan mishan wadanda za su fadi aji, sai rikici ke barkewa tsakaninsu saboda kasuwancin auduga da suka yi dumu dumu a ciki, suna bakaken tare da handama. Saboda haka babu wani mai fada a ji cikinsu aallantana a yi amfani da shi wajen cim ma nasara.
Babban abinda ya hana cigaba da shirin komawar bakar fatar Amirka zuwa Abeokuta shi ne rashin kudi . Yakin basasar Amirka shi ya kawo wannan wahalar kudin.
ME YA SA INGILA DA AMIRKA SUKA KALLAFA WA RANSU WAJEN NEMAN AUDUGA IDANUWA A RUFE?
.
Bullowar masana'antu watau "INDUSTRIAL REVELUTION" tare da samun injunan sake sake sun tilasta su neman kayyaki fiye da bayi. Yakin basasar Amirka ya tsananta kasashen Amirka da Ingila na neman auduga.
.
Babban kamfanin da ke saka da auduga wanda ake kira "LANCASHIRE'S COTTON MILLS" da ke Ingila ya shiga wani hali na kaka ni kayi a farkon karni na ashirin. Wannan kamfani wanda shi ne masana'anta mafi girma wanda kuma yake tashe tun cikin karshen shekarar 1700, sai ya shiga matsalar karancin auduga. Kamfanin yana da ma'aikata wajen miliyan uku kuma yana saka kayyakin iri iri da auduga. A wannan lokaci kayayyaki da ingila ke sayarwa ana kuma samun fam miliyan dari a shekara. Amma a cikin shekarar 1901-1902 sai kamfanin ya shiga matsalar samun auduga.
Tunkafin wannan lokaci kuwa turawan ingila ke ta fafutukar neman auduga saboda bala'in annobar ciwo watau "plaque" ta kashe manonan auduga da yawa a kasar amirka inda kamfanin ke samun auduga.
Shigan turawa Arewa sai ska dukufa wajen neman auduga da matakan da za su bi su wawashe ta.
.
Binciken da suka yi a shekarar 1904 ya nuna akwai fiye da kowane wuri a duniya baki daya, kuma wadannan wuraren za su samar da audugar da za ta ishi kamfanin auduga da ke "LANCASHIRE". Dalar Auduga ta zo , saboda haka sai fataucinta ya tashi haikan. Ko da yake samun audugar da ake a garin Abeokuta daga Arewacin wannan yanki ake yin fataucinta. An jima ana fataucinta kafin a farga da gane inda take jingim, watau Arewacin wannan kasa
ME YA TILASTAMA TURAWA SHIGOWA AREWA?
.
Idan mutum ya amsa wannan tambaya da cewa Turawa su shigo Arewa ko su tafi tsirara baza'a karyata shiba. Don kuwa sun dade suna Allah Allah su shigo Arewa, da shigowarsu ba abin da suka yi shirin yi sai aikin shimfida hanyar jirgi (Daga Baro zuwa Kano) ba abin da suka rika diba ido rufe kamar auduga. Auduga suka fi sani , ita kuma ta fi komai daraja a wannan lokaci. Turawa sun shigo Arewa domin kwasar arzikinta baki daya.
Bullowar Turawa 'yan kasuwa Arewa ya sa darajar kayyakin goda fitowa, awancan lokacin kasuwar manja ke tase. Binciken da turawa Sukayi a shekarar 1910 ya fito da dimbin kayyaki masu daraja wadanda suke jibge a Arewa, kuma sun da tsadar gaske a birnin London.
Lardin sakkoto da yola da Borno suna da danko watau "GUM" Mai daraja ta daya da irin dankon da ake samu a kasashen sudan da senegal. Akwai rama "FIBRE" , Mai karfi da daraja, farashin ton guda fam 16-17. Akwai Alkama mai kyau da daraja a sassa dabam dabam a Arewacin wannan kasa farashin kwata guda a birnin London sulai 36s :6d ( sulai talatin da shida da sisi) dawa "GUINEA CORN" Ta ci kasuwa a london ana sayar da kwata guda sulai ashirin da uku. Kudin kokon kwara kuwa, 40s . A kan kowace laba 384. Kanwa "POTASH" ce dai yadda ta je London haka ta dawo domin ba su gano amfaninta ba. Sauran kayyakin da suka yi kasuwa su ne Fatu da gyada da kuza da sauransu. A takaice dai arzikin Nigeria ta Arewa a wannan lokaci, don haka shigowar Turawa Arewa idanu rufe ba zai bayar da mamaki ba.
.
Wani abin mamaki shi ne Turawa sun dade suna hanknron shigowa Arewa, to wadannan dalilai ne suka hana su shigowa sai cikin shekara 1900? Dalilan jinkirin shigowar su suna da yawa, amma ana iya takaita cewa Hikimar Allah ce ta yi wa Daular Usumaniyya shinge. Tofaffi na fadin cewa Mulkin Fulani shekara dari ne kurum zai yi. Yakokin jaddada addini na Mujaddadi Shehu Usmanu dan Hodiyo, an fara su nea a 1803. Babu wanda ya yi mamaki da ya ga karewar mulkin nan bayan shekara dari ta cika, domin a ranar 15 ga watan Maris, 1903 sojojin Turawan Ingilishi suka isa birnin Sakkwato daga kano, wadanda ke shugabantar su kuwa su ne Janar Kembal da Kanar Morland. Wannan ya dasa aya ga daular Usumaniyya...
.
Za mu cigaba inshaallahu a inda zamu kawo mu ku ZUWAN TURAWA AREWA
0 Comments