MEYAKAWO TURAWA AREWA?

ME YA KAWO TURAWA AREWA?
*** KASHI NA DAYA ***
.
Kayayyakin goda  iri-iri sun yi kasuwa a nigeria, kuma Nigeriya tayi alfahari da su. Koda yake yanzu arzikin gona bashi da kasuwa kamar da saboda samun kayan ma'adinai kamar Man fetir da Tama da Karafa da saura. Amma duk da haka dole tarihi ya kawo amfanin da suka yi wa wannan kasa tun fil'azal, wato tin kafin a fara tinkaho da kayan ma'adinai.
.
Zamu faro tinkafin a haifi wannan kasa mai suna Nigeriya, watau tun ana kiran wannan wuri da yankin Neja watau (NIGER AREA).
.
Rahoton samun auduga da aka ce akwai ta jingim a garin Abeokuta da ke yammacin Nahiyar Afrika da ke yankin Neja, ya jawo hankulan manyan kasashen duniya, Ingila da Amirka zuwa ga wannan gari. Daga Ingila labarin Auduga ya tayar wa da kamfanonin sarrafa auduga wato " Cotton Manufacturing Company" hankali sosai don haka sai wadannan kamfanoni suka tara kudi dala 600 suka turama malamin makarantan nan mutumin Jamaik, da ya zo yankin Neja ya nemo musu Auduga. Sunan mutumin Mista Robert Campbell. Shi Mister campbell sai yataho Abeokuta.
.
A Amirka kuwa akwai dubban 'yantattun bayi wadanda cinikin dan adam ya kai su can, akwai kuma mutane masu fafutukan sama musu 'yanci, wato 'yanci da zai mai dasu dai-dai da farar fatan Amirka. Daga cikin wadannan mutane akwai Bakar fata dan Gwagarmayar neman 'yan ci mai suna Dr. Martin Robinson Delany, shi ma yaz yankin Neja don nema wa yan uwansa bakaker fatar Amirka wato " Afro Americans" wajen zama . Mr Delany ya zo Abeokuta karkashin kungiyar Wayar da kan Afirka watau " African Civilization Society" .
.
Garin Abeokuta ya samu manyan baki a ranar 5 ga Nuwamber , 1850, Dr. Martin Delany da Mister Robert Campbell sun Hadu a wannan gari, Mister samuel Ajayi Crowther shi ne ya ba su masauki. Saukarsu ke da wuya sai Mister Campbell ya shiga tattaunawa da 'yan fataucin auduga ya tsara su sosai ya kuma jawo hankalinsu.
.
Garin Abeokuta ya kayatar da Dr Martin sosai , don ya tattauna da shugabannin Yarbawa da Alake, watau Sarkin Abeokuta bisa gagarumin abin da ya kawo su da neman yarjejeniya da su bisa neman kasa don kwaso dubban Bakar Fatar Amirka zuwa garin Abeokuta. Likitan ya yi wa shuwagabannin Yarbaawa bayanin cewa akwai daruruwan Amirkawa da ke son komawa kasar haihuwar su Afirka dan zaman su A amirka yana gallazama rayuwar su sosai. Ya jaddada wa shugabannin cewa zuwan Amirkawa kasarsu yai Kawo masu ci gaba ta fannin karin ilimi da sana'a da bunkasar noma da kuma ma'aikatu.
.
Jin wannan kalami na Dr. Martin sai shi Alake na Egba Land tare da jama'arsa suka bada goyon bayan su da amincewa da zasu karbi amirkawa da hannu biyu-biyu. Ranar 27 ga Disamba, 1859 sai Alaken tare da yan Majalisarsa suka sanya hannu karbaar " Afro Americans" da kuma ba su muhalli a garin Abeokuta. Dr. Martin da Mista Robert suka sa hannu a wannan yarjejeniya a matsayin wakilan Bakar Fatar Amirka.  Wannan taro kowa na farin ciki turawa Amirkawa za su zo kasarsu zasu sami cigaba hakama Likita na murna yan uwansa sun sami  Wajen zama. A fannin auduga kuwa ko wannen su na cike da murna domin Ingila da Amirka sun samu kasuwar auduga.
.
Dr Martin ya samu watanni biyar a garin Abeokuta yana tattaunawa da shugabannin Abeokuta da 'yan fataucin auduga, kafin ya koma gida sai da yayi 'yan bincike-bincike game da ciwuka iri daban-daban da suke addabar mazauna wannan wuri, ya kuma bayar da shawarwarin xadda zaa bi a shawo kan wannan matsala. Manyan bakin sun bar yankin Neja suna cike da farin ciki dowannen su ya samu abubuwan da ya zo nema.
.
SHIN AN KWASO AFRO AMERICAN ZUWA KASAR NEJA KUWA? Shin MISTA CAMPBELL YA DAWO DOMIN CIGABA DA KASUWAN CIN AUDUGA KO A'A?
.
Dan samun amsoshin wannan tambayar ku kasance da mu gobe idan Allah ya kaimu.

Post a Comment

0 Comments