MULKIN FULANI A KASAR ZAZZAU

MULKIN FULANI A KASAR ZAZZAU(1804-2017)
.
Tarihi yanuna cewa kasar zazzau takafu sama da shekaru dubu. Da jihadin  shehu usmanu dan Fodiyo Fulani suka kifar da mulkin Habe. Fulani sun amshi mulki a bayan sakarunan habe shida.. Farkon sarkin Habe a kasar zazzau shine Gunguma , na karken su kuma shine Makau. Fulani sun amshi sarautar kasar zazzau a 1804. Farkon wanda yafara mulki a fulani shine sarkin Zazzau Musa da wazirin sa Yamusa, sai Malam Abdulkarim da Abdulsalam. Tin 1804 har zuwa yanzu 2016, fulani goma sha takwas sukayi sarautar kasar zazzau. Yau kimanin shekaru dari biyu da sha daya kenan. Akwai gidaje guda hudu da suke sarautar zazzau , sune kamar haka: Mallawa, Barebari, Katsinawa, Sullubawa.. Mallawa suna da sarakuna Hudu a kasar zazzau, Barebari Tara, Katsinawa Hudu , sullubawa kuma Daya, idan an hada jimilla sarakuna sha takwas kenan.
.
SUNAYEN SARAKUNA DA GA GIDAN MALLAWA
.
1. Sarkin zazzau Malam Musa
2. Sarkin zazzau Malam Sidi Abdulkadir
3. Sarkin zazzau Abubakar dan Musa
4. Sarkin zazzau Malam Aliyu dan Sidi.
.
SARAKUNA DAGA GIDAN BAREBARI
.
1. Sarkin Zazzau Malam Yamusa
2. Sarkin Zazzau Malam  Hammada
3. Sarkin Zazzau Malam  Muhammadu sani
4. Sarkin Zazzau Malam Abdullahi
5. Sarkin Zazzau Malam Yero
6. Sarkin Zazzau Malam Kwasau
7. Sarkin Zazzau Malam Dalhatu
8. Sarkin Zazzau Malam Ibrahim
9. Sarkin Zazzau Malam Jafaru.
.
SARAKUNAN ZAZZAU DAGA GIDAN KATSINAWA
.
1. Sarkin Zazzau Malam Abdulkarimu
2. Sarkin Zazzau Malam Sambo
3. Sarkin Zazzau Alhaji Muhammadu Aminu
4. Sarkin Zazzau Alhaji Dr. Shehu Idris
.
SARAKUNA DAGA GIDAN SULLUBAWA
.
1. Sarkin Zazzau Malam Abdulsalam.
.
Wadannan sune sunayen da gidajen sarakunan zazzau guda goma sha takwas tin daga lokacin da fulani suka amshi mulki zuwa yau.
.
ZAMU CI GABA INSHAALLAHU  ,

Post a Comment

0 Comments