MULKIN MAIMARTABA SARKIN ZAZZAU ALHAJI DR. SHEHU IDRISU A ZAZZAU
.
Babu mamaki in har aka samu wanda ya gaje ka a kan halaye masu kyau da ban sha'awa , domin wannan wani abu ne da Allah Madaukaki ya kan yi nufi da hakan. Idan aka dubi halayen da masana tarihi suka fadi a kan Mal. Abdulkarimu (sarkin zazzau) , sai a ga ya yi daidai da irin rayuwar wannan jika nasa wato Maimartaba sarkin zazzau Alh. Shehu. Kusan ma wasu masana sun yi nuni da cewa shi sarkin shehu ya tasamma daran musu ta wasu wurare saboda yanayin zamani da albarkansu da yake tare da shi. .
Babu mamaki in har aka samu wanda ya gaje ka a kan halaye masu kyau da ban sha'awa , domin wannan wani abu ne da Allah Madaukaki ya kan yi nufi da hakan. Idan aka dubi halayen da masana tarihi suka fadi a kan Mal. Abdulkarimu (sarkin zazzau) , sai a ga ya yi daidai da irin rayuwar wannan jika nasa wato Maimartaba sarkin zazzau Alh. Shehu. Kusan ma wasu masana sun yi nuni da cewa shi sarkin shehu ya tasamma daran musu ta wasu wurare saboda yanayin zamani da albarkansu da yake tare da shi. .
Rayuwar sarkin zazzau shehu ya sanya ta ne a kan jam'a ba wai shi kansa kawai ba, ta inda yake nufin ya ga an zauna lafiya da jama'a tare da tsare mutuncinsu da hakuri da abin da Allah ya ba shi, sannan da irin wannan halaye ne ya ke kokari ya ga cewa ya kyautata wa jama'arsa . Ba ya fushi don an bata masa rai kuma ba ya raya muguwar hanya irin ta zalunci. Ba ya rama mugunta saboda hakurin da Allah ya yi masa, babu fariya a rayuwar sarkin zazzau shehu, ta irin haka ne ma ya sa wasu mutane suke sha'awar mulki a kasar zazzau. A duk lokacin da ka zo don bukatar ganin sarki , za ka gan shi cikin sauki ba tare da bata lokaci ba, haka kuma zai saurare ka ya share maka hawaye idan da akwai wata damuwa. Anyi wasu lokuta da wadansu abubuwa kan faru bai san hawa ba bai san sauka ba sai kaji kasa ta dauka cewa ai sarki ne ya sa, ko kuma da hannun sarki hakan kuma ba gaskiya bane. To da zarar sarki ya ji irin wannan sai ya yi shiru har maganar ta wuce. Gaskiya ta bayyana jama'a su yanke wa kansu hukunci, dama haka ake san mai mulki da hakuri. .
Maimartaba ya sha kwaranniya iri iri, amma saboda hakuri da adalci in ma ya ji wanda ya aikata abin sai ya yi masa alheri, ba ya bukatar labarin halin da wani ya shiga na barna, ba ya son a ba shi labarin mai zaginsa don bashi da mugun kulli a zuciyarsa sai dai tattalin zaman lafiya tsakanin jama'a. Sarki ba ya rikon mutane a rai don da yana rikon mutane a ransa da yanzu babu kowa a tare da shi. Haka aka san mai mulki da rikon mutumin kiriki da na banza, malami da jahili, mai hankali da mahaukaci, manya da yara, maza da mata duk kayan sarki ne Allah ya mallaka masa su.
.
Sabo da haka rayuwarsa ta kammala ne wuri guda watau tsare gaskiya ta kowane hali wajen warware matsalolinsa da zuciyarsa kuma ba ya sa baki a kan abinda aka umurce shi da kada ya shiga ciki don neman zaman lafiya kamar siyasa ko kungiyoyin addini, wannan su ne kadan daga cikin rayuwar sarkin zazzau a tsakaninsa da jama'arsa. .
Duk da irin wannan matsayi da Allah ya kai shi bai sa shi ya nisanta da abokansa da suka tashi tare ba. Yana da wani lokaci na masanan da sukan yi hira, har ma in hira ta yi hira sukan manta da cewa su na tare da sarki ne don jin dadi. Sarkin zazzau Alh. Shehu ya sadaukar da rayuwarsa wurin Allah a kowane lokaci game da dukkan bala'e ko fitina da za ta samu wannan kasa. Ya kan taimaka wajen sa malamai, almajirai har ma da shi kansa ta hanyar rokon Allah.
Sau da yawa yan kan ziyarci makabartu a wani lokaci na musamman. Wannan kadan ke nan daga cikin rayuwar sarkin zazzau Shehu Idris. .
Allah ya karama sarki Lafiya da san jama'a Ameen
0 Comments