HARKAR RAYUWAR MUTANEN KADUNA
.
PHOTO: Wannan hoton Gwamna lugga kenan Governor-General na Nijeriya (1914–1919).
.
Garin Kaduna, gari ne wanda Turawa, Leburori da Sojoji suka kafa karkashin shugabancin Gwamna Lugga. Shi wannan Gwamna ya samu babban yabo saboda gano wannan waje da kuma daukar dawainiyar kafa wannan gari da ya yi da hannuwa biyu.
.
Kamar yadda muka sani duk inda sojoji ko leburori suke. To dole ne su kunshi kabilu iri iri wadanda addinansu da al'adun su suka bambanta da juna. Irin wannan zama ba zai yiyu ba in dai babu shugaba nagartacce wanda zai tabbatar da babu wata kabilar da aka danne kuma wani addini da aka hana binsa. Tara leburori da sojoji karkashin shugabancin turawa sai ya zama kamar tsintsiya ce da madaurinta daya, matukar babu wannan madauri to duk tsintsiyar sai ta watse a hankali. Haka yake a kaduna, inda babu Turawar Mulki da wannan zaman gari bai yiyu ba, don kowace kabila ba zata jure wa ganin al'adu ko addinin wata kabilar ba.
.
Dokokin da Turawa suka kafa wa wannan gari sun taimaka kwarai da gaske wajen maida wannan abu zama tabbatacce. Sabili da haka, kaduna sai ta taso da zaman lafiya, tsabta tare da habaka cikin dan karamin lokaci, a wannan gari babu wanda zai bugi kirji ya yi abin da ransa yake so, in har wannan abin zai karya dokar Gari. Zuwan Turawa kasar nan abin da suka yi kokari su yi hani da yinsa shi ne "MULKIN IFRIKIYYA"
.
A cikin mulkin Ifirikiyya ko kuma mulkin kama karya, shugaba yana iya sanya jama'a su yi wa mutum wasoso a gidan sa babu dalili, muddin dai wannan shugaba ya bukaci haka. Irin wannan shugabanci da Turawa suka tarar ana yi a kasar nan sai suka yi Tir da shi cewa ai shugabanci bai yarda da zalunci ba, in ana so a hukunta jama'a bisa shari'a sai akafa masu dokoki, duk wanda ya kuskura ya karya wadannan dokokin, to sai a hukunta shi yadda shari'a ta zayyana.
.
Idan jama'a kabilu iri-iri suka zauna tare karkashin hukuma daya, saboda babbancin addinai da al'adu ,dole ne su dauki matakan da za su bi don su zauna cikin lumana. Dole ne su rungumi kaddara su bar kyamar junansu wannan czai yi wu in sun fahimci juna sosai. Tun da wannan gari ya kunashi kabilu iri-iri kabilar wannan gari to ta dan bambanta da yan uwarta da ke sauran kasashe, misali Bahaushen garin kaduna ya bambanta da na kano da zariya da sakkwato da daura da kuma katsina ta fuskar halayya. Su hausawan wadannan garuruwa sun sami damar tafiyar da al'adunsu kamar yadda suke so, 'ya'yansu kabilu da suka bambanta da ta su, duk wani abu wanda yake baya cikin tasu al'adar to wannan abu fa abin kyama ne.
.
Shi Bahaushen garin Kaduna kuwa, kaddara ta sa ya taso karkashin shugabancin da dolensa ne kuma ya rungumi kaddara kabilu don zaman tare wajibi ne kuma yana ji, yana kuma gani, ya kyale sauran kabilu da al'adunsu a wannan gari ne zaka ga kowa ya kama harkar gabansa , Musulmi da wanda ba Musulmi su ce "a'a wane , zaka tafi masallaci, to sai ka dawo". Haka kuma shi ma idan makwabtan nashi kiristoci ne, kuma za su tafi Majami'ar su, shi ma sai ya rama, "aa Mista wane zaka tafi Majami'a ,to sai ka dawo". Ba kuma abin mamaki bane ka ga wannan gidan Musulmi ne na gaba da shi gidan wanda Ba Musulmi ba ne, mai yiwu wa ma wannan gidan ana sayar giya a cikinsa. Shi wannan Musulmin ba shi da damar hana sayar da ko shan giya a gidan makwabcinsa, muddin ba a shigo wajen mulkin sa ba.
.
'Ya'yan mutanen Kaduna kuma, sai suka wayi gari suka ga ai yawancin yan ajinsu a makaranta Yarabawa ne ko Ibo, sannan saboda rayuwar yau da kullum sai ka ga 'yan kabilu iri iri sun yi rukuni rukuni in sun taso makaranta ko kuma in za su tafi.
.
Saboda cudanya da kabilu kala kala Kalmar turanci ta gurbata Hausar mutanen Kaduna. A lokuta da yawa Hausawan wannan gari sukan sami kabilar da ba ta jin Hausa sai Turanci, turancin ma Burokin. Wannan abu ya tilasta wa jama'ar wannan gari samun kalmar turanci ko da Burokin ce.
.
Fahimtar wannan abu zai rage kyama da wulakancin da su Hausawan Kaduna ke gani. Misali an dauki rayuwa in ba irin ta sauran kasashen Hausa ba, rayuwar banza ko wannan rayuwar na bisa ka'idar Addinin Musulunci.
.
Mazauna wannan gari sun bai wa zuriarsu abubuwa guda biyu da za su fada wa duniya. Na farko dai leburori ne suka hade ko kuma suka dinke Nijeriya daya a lokacin tana kasasashen kasashe, sun dinke wannan babbar kasar tasu Nijeriya da aka yi a cikin shekarar 1914. Gumin wadannan bayin Allah ya taimaka kwarai da gaske wajen habaka Arzikin Arewacin Nijeriya da sauran bangaren Nijeriya baki daya.
.
Abu na biyu kuma shi ne, sojojin da suka yi yakunan duniya sun fitar da kasar Nijeriya a idanun duniya baki daya, sun yi bajintar da ba za'a manta da ita ba cikin tarihin yakunan duniya. Galibin wadannan sojoji 'yan Arewa ne. Bajintar wadannan bayin Allah ba za a manta da ita ba don har yanzu Arewa na cin albarkacin wadannan bayin Allah.
.
DAGA KARSHE KUMA SU WADANNAN BAYIN ALLAH SOJOJI DA LEBURORI TARE DA NASARA SUN KAFA GARIN KADUNA, SUN KUMA TAIMAKA WAJEN HABAKARTA.
0 Comments