SABON LARDIN ZAZZAU, BABBAN KOGIN DA KE LARDIN ZAZZAU da KAFUWAR GARURUWA KUSA DA KOGIN KADDUNA
.
Idan baku mantaba satin da yagabata mun kawo muku tariin lardin zazzau tin kafin zuwan turawa dakuma dalilin da yasa turawa suka rake fadin lardin zazzau, inda mukace sunyi hakane dan su hukunta Sarki Kwasau bisa ga laifin da sadaukin sa me suna Magaji Dan Yamusa yayi na kashe Kyaftin Moloney. Zamu ci gaba
.
Lardin zazzau dake da makeken girma sai gashi an tauye shi zuwa mai fadin 13,320q mls. Wannan sabon lardin yana iyaka da lardin kano daga Arewa, daga Gabas kuma yana iyaka da lardunan Bauci da Kano daga yamma kuma yana iyaka da lardunan Sakkwato da Neja, sannan daga Kudu Yana iyaka da lardin Nasarawa.
.
Allah ya azurta wannan lardi da kabilu iri-iri , kasa mai albarka,manya manyan itatuwa, tsibirai da manya-manyan koguna da rafuka. Acikin wannan lardin akwai manyan koguna guda biyu. KOGIN KADUNA DA KOGIN GURARA.
.
KOGIN KADDUNA
Babban kogin lardin zazzau shine kogin kaduna. Shi wannan kogi ya faro daga traunukan Ganawari da ke lardin Bauci, sannan ya shigo cikin lardin zazzau ta kudu Maso Gabas, yana kadawa Arewa zuwa Yamma har cikin lardin Neja a inda ya hade da kogin Neja.
.
Allah ya albarkaci wannan makeken kogi da abubuwa masu dinbin yawa, ana masa lakani da Kogin Kadduna (RIVER CROCODILES), Yana da wannan lakani shekaru aru aru kafin zuwan Turawa.
.
A zamanin da idan yan fataushin sanu za su haye kogin sai sukan yi wata al'ada wadda za ta rufe bakin kadduna ruf. Dayin wannan al'ada sai su zuba a kogin, sannan fataken su sa shanunsu ciki su yi iyo su haye. Koda kada ya kawo bara ga saniya lokacin da take iyo, ba zai iya bude bakin sa ba. Idan fataken suka haye kogin tare da shanunsu, sai su sake yin wata al'ada su zuba a cikin kogin wadda za ta bude bakin Kaddunan. Da yin haka sai ka ga bakin Kaddunan ya Bude.
.
KAFUWAR GARURUWA KUSA DA KOGIN KADDUNA
.
Makeken kogin nan na Kadduna na da Isasshen ruwan rani da damina, sa'annan kuma cike yake da manya-manyan kifaye da inda mazauna gabar kogin suke yin sana'ar su. Albarkar kasa da yanayi mai kyau, yasa kabilu daban daban barin garuruwa masu yawa da ke kusa da wannan kogi amma zamu kawo muku kadan daga Cikin su, wadan kuma ke da makwabtaka da dajin Doka, dajin da Turawa suka kafa wani sabon gari mai suna " KADUNA "
.
A cikin wannan garuruwa, akwai masu nisan zamani wadanda suka kafa biranensu, suke sha'anin mulki, kasuwanci da yake-yake shekaru aru-aru kafin bullowar Nasara. Kafuwar wadannan garuruwa bunkasar su da dangantakar su da juna zai wayar da kan jamaa matuka wajen zaman ka-zo-na-zo da Gwarawa , Fulani, Hausawa da Bare - Bari suka yi a wannan wuri mai albarka kafin zuwan Turawa. Yin haka zai fahimtar da jama'a inda aka kafa garin kaduna, 'yan garuruwan da suke makwabtaka da dajin da aka kafa garin. Wannan ya zama jazaman a wannan lokaci da jama'a ke zaton wai an tashi garin wata kabila ce don kafa garin KADUNA.
.
HOTO: hoton kofan doka ne tacikin ganuwa wanda aka dauka a 1980.
.
Allah ya kara daukaka kasar zazzau
0 Comments