SARKIN ZAZZAU AMINU ( 1959-1975)

SARKIN ZAZZAU MUHAMMADU AMINU  ( 1959-1975)
.
HOTO: Wannan hoton Marigayi Sarkin Zazzau Alhaji Muhammadu Aminu ne, Allah ya jikansa da rahama.
.
Sarkin zazzau Malam Muhammadu Aminu ya fito ta tsatson Malam Abukakar kwasau dan Iyan zazzau Malam Usman Dan Sarkin zazzau Abdulkarimu. Sarkin zazzau Malam Muhammadu Aminu ya yi ayyuka a wajaje da dama kafin ya zama sarki.
.
Ya rike mukamin  Health officer, Health Superinteendent of Health Depertment under zariya Natite authority. Ya zama sarkin sabon Gari sannan daga karke ya zama Iyan zazzau Hakimin sabon Gari tare da Jushi, Gwanda, Zabi, Basawa, samaru Bomo.
.
Alhaji Muhammadu Aminu ya samu cigaba da dama kafin ya zama sarki, shi ya gina Kasuwan Saban Gari, wajen wasanni na sabon gari, 'yan katako sabangari, ta dalilin sa sabon gari ta bunkasa haka ta samu shuwagabannin kungiya da danda suke kula da doka da oda. Lokacin sa ne kuma aka kafa jakara motor park, haka titin da ya ya taso daga Gwargwaje zuwa kasuwan zariya. Haka kuma lokacin sa ne aka kara gyara da fadada masallacin jumaa na kofar fada, kuma shi ya ne sarkin zazzau na farko da ya fara zuwa kasa me tsarki don aikin Hajj.  Alokacin sane ya fara gina gidan saukan baki na sarakuna , daga cikin su akwai na Tukur Tukur, Fambeguwa, da wasu a garin Makarfi. Gidan saukan baki na makarfi an gina shine dan sarakunan kano idan sun taso zuwa zariya su tsaya a nan su yi sallah su huta kafin su kariko.
.
Shi ne sarkin zazzau da ya fara ziyartan kasashen waje, daga cikin kasashen da yaje akwai Britain ,USA, Sudan, Beirut da istambul
.
Muhammadu Aminu ya zama sarkin zazzau bayan Rasuwar Sarki Ja'afaru wanda ya yi sarauta a 1937-1937. Sarkin zazzau Muhammadu Aminu ya yi mulki a 1959-1975.
.
Ya Rasu ya bar 'ya'ya wadanda suka hada da Madakin Zazzau Alhaji Garba Aminu, Wamban zazzau Alhaji Abdulkarim Aminu, Iyan zazzau Dr. Bashir Aminu, Marigayi Malam Ibrahim Aminu da kuma Marigayi Kogunan Zayzau Alhaji Nura Aminu.
.
Ya Rasu a watan Afirilun 1975 , yayi mulkin masarautan zazzau na tsawon Shekaru goma sha shida.
.
KIRARIN SARKIN ZAZZAU MALAM MUHAMMADU AMINU
.
"Fakara kora uban suluki, Banbauren gidan iya usmanu , shakaki dan Kwasau, Na Abdu Mai kifa daya kwala, Muhammadu Gwanki kaci Maharbanka."
.
Allah ya jikan sa da rahama ya rahamshe shi.

Post a Comment

0 Comments