Marigayi Sarkin Zazzau, Jaafaru Dan Isiyaku (1937-1959) yana daya daga cikin wanda Marigayi Sarkin Zazzau Malam Alu Dansidi (1902-1920) ya turasu makarantar Dan Hausa a Kano a (1910) Tarihi yanuna cewa shi Malam Jaafaru Dansiyaku Mai BIYAYYANE ga duk nagaba dashi, kuma ga kwazo da Hazaqa wajen Karatu da aiki.
Haka kuma Tarihi yanuna cewa akwai abuta da aminci tsakanin Sarkin Zazzau Alu Dansidi da Mahaifin Malam Jaafaru, wato Malam Isiyaku Dan Sarkin Zazzau, Malam Abdullahi wanda Tarihi yanuna cewa yayi Sarautar Zazzau sau biyu Wato (1857-1871 & 1874-1879). Bayan dawowarsa daga makarantar Dan Hausa sai aka turashi yayi aiki a matsayin akawun Sarkin Zazzau Alu, domin Biyayya da Hazaqarsa Sarkin Zazzau Alu yayi masa Hakinta wato ya nadashi Katukan Zazzau, kuma Hakimin Zangon Katab a (1917).
Yayi kwazo kwarai kuma Ya Qasaita domin Tarihi yanuna cewa anace masa Sarki A kudu. Yana zangon Katab Har bayan Mulkin Sarkin Zazzau Alu a (1920) Dalhatu ya Hau (1920-1924) daga nan Sarkin Zazzau Ibrahim Ya hau ( 1924-1936).
Sarkin Zazzau Malam Jaafaru ya Kafa Tarihi kuma yabar Tarihi Babba a Masarautar Zazzau. Musamman daga gidan sarautar Barebari.
Allah ya karbeshi a (August 1959). Allah yayi masa rahama, ya yafe laifukansa yasa yana Aljannatul Firdaus!!!
0 Comments