SARKIN ZAZZAU SHEHU IDRIS A MAKARANTAR MIDIL TA ZARIYA
.
Bayan kammala karatunsa na Elemetare, sai ya sami daukaka zuwa Makarantar Midil ta zariya ( Middle school ) a shekarar 1952. Ita wannan makaranta ta Middle dake zariya tana daya daga cikin makarantar farko da aka samu a Arewa, domin an kafa ta ne a shekarar 1912, a lokcin wani Baturd mai suna Mr. G. Power a matsayin Babban Jami'i mai kula da makaranta karkashin lardi. A lokacin ana kiranta makarantar lardi wato ( zariya provincial school ). A shekarar 1912, shugaban makarantar wato Headmaster , wani bawan Allah ne da ake kira Malam Muhammadu Sambo, shi ke rike da ita a matsayin Headmasta a wancan shekara ta 1912.
.
Ana nan ana samun canje canje a makarantar inda ta koma zariya middle school, a shekarar 1930 har ya zuwa 1955. Daga baya aka mai da ta ( zariya provincial secondary school ) a shekarar 1955 zuwa 1961 jim kadan sai ta koma (Goverment secondary school zariya) , wadda a yanzu ta koma "ALHUDA-HUDA COLLEGE" Zariya tun daga shekarar 1981 zuwa yau. Ita ce kuma za ka gani da ka shigo kofar Doka a hannun dama in za ka cikin zariya.
.
Sarkin zazzau ya sìga wannan makaranta a lokacin sunanta Zariya Middle School a shekarar 1952 kamar yadda na fadi a baya kuma a wancan lokacin wani jami'in kula da ilimi mai suna Mr. M. O. Water Field shi ne ke kula da makaranta, kuma wani Babban Malami mai suna Malam Abdul Rahman Mora ke rike da ita a matsayin Hedmaster, duk wadannan jami'an ilimi ne na lardin zazzau a makarantar.
.
Sannan kuma akwai wasu shugabannin makarantar a wancan lokacin da suka koyar da Maimartaba sarki kamar haka:-
.
1. Mal. Abdulrhaman Mora 1950-1954
2. Mal. Nuhu N. Bayero 1954-1958
.
Wadannan su ne Heimastoci a wannan lokacin da sarki yake karatunsa na Middle School. Akwai manyan mutane wadanda suka koyar a makarantar kamar tsohon shugaban kasa Alh. Shehu Usman Aliyu Shagari, da Dan masanin Kano Alh. Yusuf Maitama Sule da Alh. Abba Habib.
.
Sarkin zazzau shehu ya sami shekaru biyar kafin ya gama karatunsa na Middle school. Bayan gamawarshi sai ya wuce katsina "Training College" dake garin katsina.
.
Zamu ci gaba

0 Comments