Tarihin Sarkin zazzau shehu idris

,TARIHIN SARKIN ZAZZAU ALHAJI DR. SHEHU IDRISU LLD CFR
.
ISHARA GAME DA HAIHUWAR ALHAJI SHEHU IDRIS A SHEKARAR 1936
.
A shekarar da aka haifi Mai Martaba Sarkin zazzau Alhaji shehu babu shakka an ga abin mamaki, wannan abin mamakin kuwa shi ne, bayan haifuwarsa da kwana bakwai, Mai Anguwa Idrisu Auta ya aika da goro ga 'yan uwa da masoya domin radin sunan Mai Martaba, sai kurum zuma ta taso wanda yake ba a san ko daga ina take ba sabo da babu wani gida kusa inda zuma ta yi sansaninta.
.
Daga nan sai mutanf kowa yana kau da jiki gudun kar ta harbe shi to, amma kuma ba ta harbi kowa ba a cikin jama'ar da suka zo sunan. Haka dai aka tsaya har zuwa wani dogon lokaci sannan aka yi sunan, kuma duk irin wannan tsawon lokaci wannan zuma bata harbi kowa ba. Bayan gama rada suna sai ta samu wuri jikin itace ta yi sansani har sai da ranar da akayi sunan ta zagayo sannan a wannan rana ta tashi da daddare amma ba a san inda ta yi ba. Ganin haka sai Mai Anguwa Idrisu ya kira wani daga cikin yaran gidansu wanda ake kira Majidadi Alu, ya ce masa ya shirya ya tafi ya samu wani Malami da ake kira Malam Lawal, shi Malamin masanin gaske ne kwarai kuma bawan Allah ne, yana zaune a garin da ake kira Gungurfa cikin yankin shika a kasar Giwa.
.
Majidadi Alu ya tafi  ya sami Malam Lawal yana karatu Tare da dalibai, sai dai Mai Anguwa Idrisu ne ya aiko shi da ya shaida masa cewa an yi suna to amma wannan rana zuma ta hana mutane sukuni , ya dai kwashe duk abinda ya faru ya fadama malam. Daga nan Malam Lawal ya ce wa Majidadi ya koma ya shaida wa Mai Anguwa cewa babu wanph abu bisa yardar Allah sai dai Alheri a kan wannan kyauta da Allah ya yi masa, saboda haka ya ci gaba da rokon Allah shiriya abisa kyautan da ya bashi. To irin wadannan su ne isharori da Allah ya boye a kan kome ne Alhaji shehu Idris zai zama a gaba, sai da Allah ya kawo shi wannan matsayi sa'an nan ake kafimtar haka. Domin babu mai ilimin gaibi face Allah don haka Malam Lawal Gungurfa ya ce ma Malam Idrisu kada ya yarda a camfe shi da wani abu. Sai dai fatan alheri, kuma shi Mai Anguwa Idrisu ya yarda da wannan bayani da Majidadi Alu ya fada masa, domin ya yarda da cewa dukkan wani al'amari yana hannun Allah ne.
.
RAYUWAR SARKIN ZAZZAU ALH. DR. SHEHU IDRIS LL.D Cfr
.
Mai martaba sarkin zazzau, kuma sarki na goma sha takwas a  mulkin daular fulani a lardin zazzau, an haife shi a zariya a cikin shekara ta 1936 kuma shi Dan Malam idrisu auta ne, daya daga cikin 'ya'yan sarkin zazzau Malam Sambo, wanda ya yi mulki daga shekara ta 1879-1888, ya fito ne daga jinsin gidan sarautar Katsinawa wadda Malam Abdulkarimu sarkin zazzau ya fara a cikin shekara ta 18è4-1846.
.
Mai martaba  ya yi karatunsa a na elementare a Makarantan Elementare na farko da ke kofan Kuyambana cikin Birnin zaria (TOWN SCHOOL 1 ) A shekarar 1947 zuwa 1950. Bayan kammala karatunsa na elementare sai ya shiga Middle school da ke zariya a cikin shekarar 1950 har zuwa 1955. Bayan kammala Middle school a shekarar 1955 sai ya sami ci gaba zuwa, Babbar makarantar koyan aikin malinta ( katsina training collage)  a cikin shekarar 1956 zuwa 1957. Bayan gama karatunsa a katsina Training Collage ya samu kyakkyawan sakamako inda ya fito da takardar shaida ta kwarewa a kan aikin malanta. Daga nan ne ya samu koyarwa a karkashin hukumar ilimi da ke karkashin En'en zaria ( Native Authority ) ya karantar a wurare da dama, kamar Hunkuyi, zariya, Paki, Zangon Aya.
.
Daga nan Maimartaba ya halarci Kos din da ake yi na sanin yadda ake tafiyar da harkar kudade na ( N.A) A makarantan koyan Aikin mulki dake karkashin Jami'ar Ahmadu Bello zariya (Institute of Administration, kongo A. B. U zaria a cikin shekarar 1961. Bayan ya kammala wannan kos kuma ya sami takardar shaida mai kyau, sai ya fara aiki a karkashin ofishin Marigayi sarkin zazzau Alh. Muhammadu Aminu, a matsayin sakataren sarki ( Private Secretary ). Alh. Shehu Idris ya sake komawa ma'aikata a shekarar 1963 , da gamawarsa ne sai ya shiga aikin gwamnatin Jahar Arewa.
.
Maimartaba sarkin zazzau Alh. Shehu Idrisu ya kara himmatuwa kan neman ilimi ya tafi kasar Australia don yin kos a kan koyon aikin mulki 1967. Bayan dawowarsa daga wannan kos sai aka bashi Hakimin Birnin Zariya da kewaye kuma aka nada shi sarautar Dan Madamin Zazzau a cikin shekarar 1973.
.
Yana nan a wannan matsayi na Hakimin Birni Allah ya yi wa Alh. Muhammadu Aminu Rasuwa. Daga nan aka zabi Alh shehu Idrisu ya zama sarki a ranar 8 ga Febrairu, 1975, ya zama sarki na 18 a zazzau na hudu a gidan sarautar Katsinawa. Ya hau gadon sarautar zazzau yana da shekara talatin da tara a duniya yanzu kuma shekaransa 42 a kan gadon sarautar zazzau. Ya hau gadon sarautar zazzau yana da matan Aure guda uku 'ya 'ya biyar. Daga baya ya auri diyar sarkin Musulmi Abubakar III a lokacin da ya hau mulki.
.
JERIN SUNAYEN MATAN SA
1. Hajiya Habiba
2. Hajiya Fatima
3. Hajiya Binta
4. Hajiya Mariya
.
Marigayi Alh. Aliyu Shehu , Madakin zazzau , da Marigayi Ahmad Shehu. Mata kuwa su ne Hajiya salaha, Hajiya Aminatu da Hajiya Mairo. Wanda aka fara haifuwarsa a kan gadon sarauta shine Muhammadu Kabiru yanzu haka dai Maimartaba yana da 'ya'ya Talatin da biyar maza da mata banda wadanda suka rasu.
.
Kamar yadda aka fada a baya cewa madakin zazzau Aliyu shi ne babban Dan sarkin zazzau Shehu , bayan rasuwar madaki nd aka nada Malam kabiru shehu sarautar madaki.. Wanda ya fara rasuwa a maza shine Malam Ahmadu, sai mu'azu sai Madaki Aliyu sai Kabiru, haka  kuma a cikin 'ya 'yan Sarki mata wadda ta fara rasuwa ita ce Haj zaliha, matar Alh Ja'afaru. Muna fata Allah ya jikan wadanda suka rigamu gidan gaskiya, yasa muma idan namu ya zo mu cika da imani Ameen.
.
Za mu ci gaba inshaallahu
DAGA: kasar zazzau A jiya da yau

Post a Comment

0 Comments