TSARIN AIKACE - AIKACEN MAI MARTABA AL. DR SHEHU IDRISU
.
A 1957 Malam Shehu idris ya kammala karatun sa a katsina Training College, daganan sai ya fara koyarwa, bayan dan zaman da ya yi na koyarwa a hunkuyi sai aka yi masa canji zuwa Makarantar firamare ta zangon Aya nan hanyar kaduna. Kuma a nan ne ya samu daukaka aka bashi matsayi shugaban makarantar firamare ta Paki cikin karamar hukumar Ikara. Likkafa ta ci gaba inda aka dawo da shi zariya inda ya bude makarantar kaura , wato L. E. A Primary school Kaura.
.
Bayan 'yan shdkaru sai ya canza aiki zuwa aikin akawun kudi ( Accountancy ) a ma'aikatan ayyuka dakd karkashin N. A . Daga nan ne aka tura shi makarantan koyon aikin mulki bangaren koyon aikin Akawun kudi (institute of administration kongo) a shekara ta 1962. Daga nan ne ya zama sakataren sarkin zazzau Alh. Muhammadu Aminu. Ya kuma zama sakatare a masarautar zazzau a shekarar 1967.
.
An nada shi sarautar wakilin ofis kuma sakatare na karamar hukumar zaria a shekarar 1968, an yi masa hakinci bayan dawowarsa daga karatu tare da mukamin daya ke rike da shi na sakataren karamar hukuma. Daga nan ya zama hakimin Birni da kewaye kuma Danmadamin zazzau a shekarar 1973.
.
Haka kuma wani karin abin farinciki shi ne a lokacin da aka ce yana daya daga cikin wadanda za'a tura karatu a kasar waje daga gwamnatin najeriya ta arewa, a lokacin yana rike da mukamin sakataren karamar hukumar zariya, a kwai abubuwa da dama na farinciki da baya yiyuwa sarki ya manta dasu shi ne tun daga lokacin da ya fara aiki a cikin shekarar 1958. Kusan dukkan aikace aikacen da ya yi har zuwa zaman sa sarki. Ba'a taba samun shi da wani laifi na rashin gaskiya ba ko laifin wanda ya saba dokokin aiki. Tun daga shekarar 1964 har zuwa 1968 sarki yana cikin aikin Gwamnati da tafiya yin kwasa kwasai a gida da wajen najeriya. .
.
Ranar takwas ga watan fabrairu 1975 ( 8/2/1975) ne ranar da aka zastar da cewa Malam Shehu Idris shi nf Allah yaba sarautar zazzau. Ita ce kuma ranar da ya hau wannan matsayi da yake kai har yanzu. ALLAH YA JA ZAMANIN SARKI.
.
Bayan wasu 'yan shekaru an yi ta samun canje chanjen wasu daga cikin aiyukan ofishin sarki suka koma zuwa ofishin karamar hukuma to amma sabo da tsare taren aiki da akayi tun farko yasa dole dai wasu daga cikin aiyukan sai an yi hadin guiwa wurin aiwatar dasu.
.
A yanzu an dauke nauyin abiyan hakimai da ma'aikata daga ofishin sarki zuwa kananan hukumomi, to amma duk da haka tsare tsaren aikin suna nan a karkashin masarauta. Haka kullum sarki ke samun koke koken jama'a daban daban daga gundumomin masarautar sabo da haka a kullum aiki karuwa ya ke yi ba raguwa.
.
Zamu ci gaba

0 Comments