WASANNIN MOTSA JIKIN DA SARKIN ZAZZAU SHEHU KE SHA'AWA

WASANNIN MOTSA JIKIN DA SARKIN ZAZZAU SHEHU KE SHA'AWA
.
Game da sha'anin wasannin motsa jiki, Maimartaba sarki Shehu yana sha'awar wasannin motsa jiki na zamani kamar kwallon gora (HOCKEY) da kwallon bango (FIVES) a fadarsa, wanda yanzu haka wurin na nan kebe da sauran wurare irin wadannan don wasanni.
.
Haka kuma Maimartaba kan tafi gonarsa don ya hau doki ya motsa jiki. A kan kwashi dawakai a kai gona inda ya kan hau ya zagaya a fili wadatacce da ke gonar.
.
Wani karin abin sha'awa shine a duk lokacin da sarki zai yi wannan wasanni ya kan gaiyaci wasu daga cikin abokansa don suyi wasan. Kamar Alh. Hussaini Alhassan, Alh. Danjuma Bawa, Alh. Bello Aliyu, haka kuma ko da ba sarki a wurin sukan shiga don motsa jini yanzu haka a kwai sabon filin wasa na jefa kwallon raga da aka gina kuma ana yin wasa a cikin sa.
.
Wannan wasanni sarki yana nuna irin mahimmancin da suke da shi musamman ga mutun wanda yayi nauyi da yawa to zai taimaka masa wurin samun kuzari da rashin nauyin jiki. Shi yasa sarki yake ba irin wadannan wasanni mahimmanci kuma ya gina irin wadannan wuraren wasanni a fadarsa.
.
ALLAH YA KARAMA SARKI LAFIYA DA KWANCIYAR HANKALI

Post a Comment

0 Comments