WASANNIN SHAKATAWA, KUNGIYOYIN FARKO A GARIN KADUNA, UNGUWAR LEBURA HADE DA SHIRYE-SHIRYEN KAFA TUDUN WADA KADUNA
.
Duk inda Turawa suke yana daga cikin halayyarsu idan lokacin aiki ya yi sai a tsaya a dukufa wajen aiki. Haka kuma idan ka gansu suna hutawa sai ka ce ban da hutu ba abin da suka iya.
.
Turawan mulkin tun a wajen shekarar 1920 sun hada kulob a kaduna domin wasanni iri iri. Kowane dan kulob ya na biyan 5s a kowane wata. Ana wasan kwallon Tennis da Golf da na Cricket.
.
Akwai kuma wasan Polo. 'yan kulob din polo suna wasanninsu da yammar ranakun Litini da Laraba da Kuma Juma'a tun cikin shekarar 1920.
.
KUNGIYOYIN FARKO A GARIN KADUNA
Jama'ar Garin Kaduna suna zaune ba tare da nuna bambancin Addini ko na kabila ba. An kafa kungiyoyi masu yawa don samun habaka a lokaci dabam dabam . Kungiyar farko ita ce kungiyar Al'ummar kaduna wadda aka kafa tun wajen shekarar 1920, shugabannin wannan kungiya ta " KADUNA COMMUNITY LEAGUE" Sune : Malam Mai Buruji da kororo dan Malam da Mista ladipo da Mista D. I. Imoudo da Babbar Riga da Malam Ra3a da Namarashe da Malam M. A. Inuwa da Mista Nwanko. Sauran kungiyoyin da aka kafa a wannan lokaci har da kungiyar masu Gidaje da 'yan haya wamda za ta tabbatar da zaman lafiya tsakanin mai Gida da 'yan hayarsa.
.
Daga baya an samu kungiyoyi masu dama da suka bullo kamar: kungiyar 'yan mata shugabannin kungiyar sune: Hajiya Katiti da Hajiya Ramatun Buda da kari da Gwado da Hajiya Tinka. Wajen masu wasan kwaikwayo kuwa akwai Mamuda Gwamna da Alhaji Bala Keffi da Alhaji Bala I. G. P da Alhaji yaro Tela da Nadada Tela. Duk wadannan kungiyoyi da sauran irinsu sun bada na su taimako wajen kawo zaman lafiya da annashuwa a cikin Garin Kaduna.
.
UNGUWAR LEBURA
.
Saboda yawan leburorin da ake samu a kullum a cikin sabon Gari, sai aka kafa masu unguwa a yamma da kasuwa (wajen kasuwar Fanteka a yanzu). Ita wannan unguwar aka sa mata suna unguwar Leburori kafin karshen shekarar 1920. Akwai daruruwan leburori a wannan unguwa jingim.
.
Unguwar lebura ba ta karkashin hukuncin STATION MAGISTRATE saboda tana cikin kasar Zariya ne, dalilin haka aka tattauna da Rasdan na Zariya bisa su mazauna wannan unguwar hukuma ta san da zamansu.
.
Saboda wannan dalili sai Iyan Gari Iya Abdullahi ya nada shugaba, wato mai unguwa wanda zai kula da shugabancin wadannan jama'a . Wanda aka nada shi ne Jakadan Sarkin Kawo Abdullahi mai suna Kwasau.
.
A hankali wannan unguwar sai cika take yi da jama'a kuma sarkin unguwar Leburori Kwasau yana tafiyar da shugabancin sosai don tabbatar da zaman lafiya da lumana. Abin ka da garin leburori da gari ya waye in rana ta fito sai ka ji garin tsit ba ka jin duriyar kowa daga yara sai mata, amma da zarar yamma ta yi leburori sun dawo wajen aiki sai unguwar ta cika makil da jama'a.
.
SHIRYE SHIRYEN KAFA TUDUN WADA
.
Gwamnjn wannan Lokaci Mista H. Clifford ya tada kananan sarakunan Garuruwan wannan wuri sai Gwamna ya ce da su za'a tashi jama'ar unguwar leburori daga inda suke, kuma za a kafa gari mai suna Tudun wada saboda za'a yi gidan Gwamna a Badiko ba a kuma son hayaniyar jama'a ta dame shi.
.
Gwamna Clifford ya tara wadannan sarakuna ne a wannan daji kudu da Buzaye watau inda za a kafa Tudun wada. Su wadanda aka yi taron da su kuwa su ne: iya Abdullahi da Sarkin kawo Abdullahi, ya ce da su a wannan wajen za'a yi safiyon fulotai, mutanen kangiwa (inda alkali yake), za'a tayar da su a basu fulotai a wannan wuri, haka kuma za'a gina babban dakin sharia da gidan alkali, mutanen unguwar lebura su ma za'a dawo da su nan a basu fuloti.
.
Gwamna Clifford ya ce da Iyan Gari Abdullahi, "Mun karama maka girma don haka za ka koma gidan MAGAJI SAMBO dake Makera shi kuma Magaji Sambo ya koma Cukun. Babban baturen ya bayyana cewa " mun yi wat wanya dake kujama ritaya, kujama dake karkashinsa mun kara wa Magaji sambo da ita." . An kuma yi wa Magaji sambo Tabari karin girma a wannan lokacin da ake shirye shiryen kafa Tudun wada.
.
HOTO: WANNAN HOTON MARIGAYI SARKIN ZAZZAU IBRAHIM KWASAU NE . A Lokacinsa ya taimaka sosai wajen bunkasa garin Kaduna. A zamaninsa ne aka kafa Tudun wadan Kaduna. Allah ya ji kansa ya rahamsheshi Ameen.,
.
0 Comments