ZABEN ALHAJI SHEHU SARKIN ZAZZAU

ZABEN ALHAJI SHEHU SARKIN ZAZZAU
.
HOTO: wannan hoto an daukeshi ne a 8/2/1975,  Yayin da Maimartaba ke jawabi bayan gama rantsar da shi a matsayin sarkin zazzau. A gefensa tshohon gwamnan jahar kaduna ne na mulkin soja Birgediya Abba kyari
.
A cikin shekarar 1975 Allah ya yi ma sarkin zazzau Alh. Muhammadu Aminu rasuwa a ingila. Bayan an gama juyayin mutuwarsa, sai aka umurci masu zaben sarki da su gaggauta yin zabe don fito da sabon sarkin zazzau. A cikin mutane masu neman sarautar, an sami mutane daga kowane gidan sarauta wadanda suke neman wannan matsayi. A hakika, sarki shehu idris, shi ne mutum na karshe da sunansa ya fito a cikin masu neman sarautar zazzau kuma shi ne ma fi kankantar shekaru a cikin 'yan takarar wadanda hakan ya jawo jayayya a tsakanin masu zaben sarki dangane da shekarunsa. A wancan lokacin an sanya Malam Muhammadu Jumare a matsayin wakilin Gwamnati don gudanar da wannan zabe a zarhya, kuma ya zo da ka'idodi da gwamnati ta tsara a kan masu zaben sarki kuma su masu zaben sarki su biyar ne kamar haka:-
.
1. Wazirin zazzau- Nuhu Yahaya
2. Fagacin zazzau- Muhammadu
3. Makaman zazzau- Haliru
4. Limamin juma'a- Muhammadu
5. Limamin kona- Balarabe.
.
Wadannan su ne masu zaben sarki, kuma kowanne daga cikinsu an karanta masa ka'idodin da gwamnati ta shirya a kan zaben sarki. Wadannan ka'idodi kuwa su ne:-
.
1. Na farko shi ne duk wanda za a zaba sarki, sai ya kasance bai taba yin wani laifi wanda Hukuma ta hukunta shi ba.
.
2. Na biyu kuma, ya kasance ya taba rike , ko yana rike da matsayi na sarauta ko hakimta.
.
3. Na uku ya kasance na da cikakken ilimin zamani.
.
4. Na hudu ya kasance ba mai yawan shekaru ba ne , wato tsoho.
.
5. Na biyar kuma a tabbatar da ya na cikin daya daga cikin gidajen sarautar zazzau.
.
Bayan kowa ya gamsu da wadannan ka'idodin sai aka ci gaba da tattaunawa a kan maganar zabe, inda kowa ke kawo nasa. Kowa ya fadi nasa sai a ba shi dama ya yi bayani a kansa game da irin ayyukan da ya yi kuma da irin iliminsa da kuma halayya na rashin saba doka.
.
Haka kuma a kan ba da dama ga wani ya soki ra'ayin wani dangane da wani abu na aibi dake tare da wannan mutum da ya zaba.
.
Haka dai akai ta yi har aka kawo kan Alh. Shehu. Wani daga cikin masu zaben , ya tashi ya fadi irin abubuwan da ya yi wanda ya kunshi tun daga kan iliminsa har zuwa mukaman da ya rike ba tare da wani laifi ba, kuma shekarunsa sun kai yadda ake bukata, kuma ga shi ya goge a kan sha'anin mulkin jama'a. Daga nan sai wakilin gwamnati ya tambaya cewa ko akwai jayayya a kan wannan bayani da wannan mutum ya yi?. An sami yar jayayya kadan wadda ba ta yi tasiri ba.
.
A cikin wurin zabe sai aka sami wani ya ce ya goyi bayan mutum na farko a kan bayanin da ya yi a kan maimartaba sarkin zazzau shehu. Daga nan fa ai shi kenan sai aka sake samun goyon bayan wani, har ma dai saura kuma suka yadda a kan hakan.
.
Bayan gama zabe, sai wakilin gwamnati ya shaida wa masu zaben sarki cewa an tanadi horo na musamma ga duk wani mai zaben sarki  da ya azarba bin fadin abinda aka tattauna game da zaben ko ya fada wa wanda aka zaba har sai gwamnati ta fadi wa jama'a sunan sabon sarkin da aka zaba.
.
� Har ila yau akwai Majalisar sarakuna wadda ta ke karkashin gwamnatin Arewa ta tsakiya Inda (MAIGIRMA SARKIN KATSINA) Ke rike da mukamin shugaba a wannan lokaci. Ita wannan Majalisa ta kunshi sarakunan Katsina , daura, zazzau, jama'a, kagoro, jaba, marwa da kwai. Kukansu sun ba da goyon baya a kan zaben da aka gudanar a masarautar zazzau, kuma sun yi na'am da zaben da aka yi na Alh. Shehu Idris Ya zama saskin zazzau.
.
Daga nan sai wajen gwamna wanda a lokacin Brigadier Abba Kyari shi ne Gwamnan Jihar Arewa ta Tsakiya shhi kuma tare da ma shawartar majalisarsa suka amince ya zartar da haka ba tare da bata lokaci ba.
.
An ba da sanarwa cewa Alh. Shehu Idris ne Allah ya zaba ya zama sarkin zazzau a Ranar 8 Ga watan fabrairun 1975 kuma Gwamnan Jihar arewa Ta Tsakiya wato Brigediya Abba Kyari ne ya fada da bakinsa. Daga nan aka fara shirya yi a ranar. Gwamna Abba Kyari ya zo ya mika masa sanda a gaban sarakuna na Arewa. Sarki Mai Daraja ta daya. Kuma an yi wannan biki ne a filin sukuwa dake hanyar samaru a sabon Garin zaria.
.
Bisa al'adar nadin sarki a kasar zazzau, Madaucin . Cikin gida ne ke sa wa sabon Sarki alkyabba da rawani, kuma masu busa farai kuma su busa, wanda ke nuna cewa ya tabbata sarki. Bayan da gwamna ya mika masa sanda da sauran kayan aiki na sarautar gargajiya sai aka umurci liman da ya rantsar da shi kamar yadda ya ke a tsarin sarakunan musulunci. Daga nan sai manyan 'yan Majalisar sarki da Hakimai suka zo gabansa suka yi mubaya'a a bisa jagorancin wazirin zazzau.
.
Daga nan sarki ya dawo gida mutane daga kasashe daban daban suna ta zuwa don yi masa murna a jan wannan daraja ta sarauta da Allah ya ba shi. Aka ci gaba da shan shagali mawaka da maroka daban daban daga kasashe suka zo don taya murnar wannan sarauta.
.
Ran sarki ya dade, dubu bisa dubu dan idirisu autan sambo Allah ya karama lafiya.
.
A MADADIN DAUKACIN  KUNGIYAR  KASAR ZAZZAU A JIYA DA YAU , MUNA MIKA SAKON TAYA SARKI MURNAR CIKA SHEKARU 42 AKAN KARAGAR SARAUTAR ZAZZAU.
.
MUNA FATA ALLAH YA KARAMA ADALIN SARKI LAFIYA, ALLAH YA JA KWANA, DUBU BISA DUBU

Post a Comment

0 Comments