ZAMAN SARKIN ZAZZAU SHEHU A GIDAN ALHAJI AMINU SALIHU

ZAMAN SARKIN ZAZZAU SHEHU A GIDAN ALHAJI AMINU SALIHU
.
HOTO: wannan shine Marigayi Alh. Aminu Salihu
.
Bayan Rasuwar Mai Anguwa Idrisu Auta, sai wani daga cikin masoyansa ya dauki sarkin zazzau shehu ya zauna tare da shi. Wannan mutum kuma shi ne Alhaji Aminu Salihu. Kuma ya ri ki sarki kamar dan da ya haifa na cikinsa. Sannan ya samu karin tarbiya bisa ga wadda ya samu a hannun mahaifinsa.
.
Alh. Aminu  mutum ne mai hakuri kuma mai neman abin kansa ga addini da gaskiya da rikon amana saboda haka babu wani abin mamaki idan sarki  shehu ya samu irin wadannan halaye a tare da shi.
.
Sarkin zazzau ya zauna da Malam Aminu salihu bisa amana, bai taba yin masa wani abu da ya yi fushi da shi ba. Haka shima Alh. Aminu ya rike shi kaman dan da ya haifa na cikin sa , ya bashi kula da tarbiya kamar yanda yake baiwa 'ya'yan cikin sa.
.
Hakama matan Alh. Aminu , hajiya safiya Dammo ta nunama sarki tsananin soyayya, saboda wannan tsantsan soyayya da ta nuna masa ya kasance bata son taga wani abu da zai taba shi ko ya tayar masa da hankali, haka kuma a koda yaushe ta kan ja ra'ayin sarki shehu da ya yi karatu, kada ya sa wasa a duk al'amuran da ya sa gaba. Haka kuma a wancan lokacin Maimartaba Sarki ba shi da wasa da ya wuce wasan dan bywaro da langa. Shi ke nan kusan wasan da yake yi tare da yara 'yan uwansa.
.
Game da tarbiya , sarkin zazzau shehu ya sami karin tarbiya a zamansa hannun Alh. Aminu Salihu watau dai karin wanda ya samu a wurin mahaifinsa. Sarki ya yi karatu mai yawa a hannun mahaifinsa Malam Idrisu Auta kafin ya wuce zuwa makarantan Malam Bawa da M. Abubakar kofar kuyanbana inda ya yi karatun allo har ya sauke Alkur'ani.
.
Maimartaba yana da manyan abokansa kamar M. Abdulsalamu Ahmad wanda tare suka tashi da sarki a gidan Alhaji Aminu salihu kuma kullum tare suke , sai sauran abokansa kamar su Alh. Danjuma Bawa, Alh. Bello Aliyu, Alh. Dadaye Aliyu, Mal. Garba Iguda da Mal. Ahmad Dan Bala. Kusan wadannan mutane a koda yaushe tare za ka gansu da sarki, babu wani abu na sabani da ya taba shiga a tsakaninsu, saboda irin tarbiyar da suka samu a hannun iyayensu da malamansu. A koda yaushe za ka ga sun taru suna hira a gida a cikin dakin Haj. Safiya Dammo ita kuma a lokacin tana masu tatsunniya suna jin dadi da walwala a tsakaninsu.
.
Irin wannan rayuwa da sarki ya yi da wadannan abokansa da suka tashi tare, shi ne ya kawo su har zuwa yanzu. Kuma kowa da yadda yake a wurin shi, sabo da sanin juna tun suna kanana har ya zuwa yau babu yadda za'a yi sarki su kwana uku ba su hadu ba da Alh. Danjuma Bawa ba sai dai ko bisa lallura ta rashin lafiya, kuma ko da da rashin lafiya sai sun yi hira ta waya.
.
Haka kuma suke da Alh. Bello Aliyu wanda yanzu yake  a kano a duk lokacin da ya zo zariya zai kamo hanya ya zo fada su yi hira irin ta abokai, saboda irin yadda aka san shakuwarsu har ma idan aka ce Bello yana tare da sarki, to rabuwarsu sai hali. Hakama Marigayi Hussaini Alhassan ( Mabudin Zazzau ) a duk ranar duniya sai sun hadu da Maimartaba sarkin sai dai idan tafiya ce ta kama wani daga cikin su.� Hajiya Safiya Dammo ta ce sarkin zazzau shehu ya kasance mutum me kula da addini da san jama'a da hakuri. Takara da cewa " haka kuma ba ni manta wani abu da ya ke faruwa a kullum idan Mai martaba ya zo wurina ina aikin taba tunkura tare da yara masu rufe mini bakin tunkura, idan na dura su kuma sai su toshe bakin, to idan za su tafi sai in kawo tunkura in ba su a matsayin ladan aikinsu, su kuma sai su je su sayar kobo uku ko hudu da sisi. To a kullum suka zo sai mai martaba ya ji irin yadda suke magana sai shi ma ya ce zai yi a lokacin..
.
Idan muka yi laka'ari da wannan batu zamu ga ce wa shi maimartaba tinyana karami mutum ne mai tausayi da hakuri da san mutane masu neman nakan su, wanda wannan halin ya biyo shi har izuwa girman sa.
.
Muna fata Allah ya karama sarki lafiya.
.
Ku biyomu a nan gaba dan jin tarihin Mulkin Sarkin zazzau Alh. Shehu idrisu.

Post a Comment

0 Comments