KASAR ZAZZAU KAFIN ZUWAN TURAWA da. RAGE FADIN LARDIN ZAZZAU.
.
KAFIN ZUWAN TURAWA
Lardin zazzau shi ne mafi girman a duk lardunan kasashen hausa, yana kuma daya daga cikin lardunan masu tsohon tarihi. Zazzau ta samu girman lardi saboda yake-yaken da Amina Sarauniyar Zazzau ta yi. Wannan yasa sarkin musulmi Muhammadu Bello ya ce a cikin littafin nan ''imfakul maisuri'', ya ce "Abubuwan mamaki sun faru a cikin tarihin kasashen Hausa bakwai, amma mafi al'ajabi shine mallakar kasa mai girma da Allah ya baiwa Amina sarauniyan zazzau. Ta ci duk kasashen hausa da yaki, saboda haka kanawa da katsinawa na kai mata haraji. Ta yaki bauci da sauran kasashen da suke kudu da yamma, sai da mulkinta ya danganta da bakin teku.
.
Sarauniya Amina ita ce babbar 'yar sarkin zazzau Bakwa Turunku. Yake-yaken da ta yi ta ciwo ma zazzau manya manyan kasashe. Ta mallaki mutane kwararrafa (Jukuns) da nufawa. Sarakunan nufawa ma kawo mata goro kwarya dari da fidiyayyun bayi arba'in kowace shekara. Alokacin ta Ne aka fara cinikayya a tsakanin mutanen kudancin wanman kasa. Amina ta yi shekara wajen 34 tana mulki. Ta rasu a garin Idah a bakin kogin Neja.
.
RAGE FADIN LARDIN ZAZZAU
Wannan fakadeden lardin an rage fadinsa jim kadan bayan turawa Arewa. Lokacin da turawa suka bullo, sarkin zazzau Kwasau ke mulki. A 1902 sun rage fadin lardin zazzau don su ladabtar da sarkin zazzau domin kashe wani bature mai suna Kyaftin Moleney da wani jarumin sarki kwasau ya yi a garin Keffi. Wannan jarumin mai suna Magaji Dan Yamusa an ce ya yaki turawa bullar su keffi ba tare da izinin sarkin zazzau kwasau ba.
.
Magaji Dan Yamusa Jarumi ne na inna-naha, an yi yake-yake da shi da yawa tun kafin bullowar turawa, yana daya daga cikin manyan dakarun zazzau a wannan lokacin. Kodayake baya iya sarrafa hannayensa sosai saboda sun sami nakasa, sai yaknma yana yaki da kafafun sa kuma yana amfani da likafar doki a matsayin makamin sa. A fagen fama magaji dan yamusa da likkafan dokinsa yake baiwa kura nama.
.
Turawa sun shigo garin keffi karkashin kyaftin Moloney tare da mai musu tafinta, Audu Tun-Tun. Jarumi magaji sai ya gwabza da turawa. Ance wai da bindiga ya harbe kyaftin moloney sai ga bature rica! Kwance cikin jini. Tafinta Audu nan ya bar shi kolo na shan jininsa, da likkafar dokinsa ya kashe shi.
.
Dabarar yaki irin ta magaji dan yamusa daban take, domin idan ya zabura bisa doki kai tsammani zai kawo sara da takobi ko suka da mashi ne, amma ina! Kafin ka yi aune sai ka ji likkafa mai kaifi a cikinka domin kuwa kafa zai miko maka daga dokinsa.
.
Kashe kyaftin Moloney ya tayar wa da turawa hankali sosai dan sun nemi magaji dan yamusa ruwa ajallo saboda wannan ta'annati da ya aikata. Ko da yake sarki kwasau bashi da hannu a kashe wamnan bature, bai kuma goyi bayan wanda ya yi kisan ba, sai turawa suka rage masa fadin kasarsa. Sun yanke lardin Binuwai daga cikin zazzau, kogin Gurara sai ya zama sabon iyakar lardin zazzau.
.
Lardin zazzau ya zama mai fadin 22,000sq. mil. Ya mika yamma har wajen kogin gulbi (wanda ya iyakance shi da lardin kwantagora) ya kuma kunshi garuruwan Dungurun da wushishi.
.
Acikin shekarar 1908 an sake yanke wa lardin zazzau fadin kasa. An yanke mata kasa mai fadin 10,000sq mls da ke yammacin zaria. Wannan kasar ta kunshi kabilar Gbagyi da sauran kabilun wajen, an maida su zuwa lardin Neja. Da garuruwan Minna da Bida da Abuja da sauran garuruwan da suke kusa da su. Duk suna cikin lardin zazzau ne....
.
Zamu ci gaba inshaallahu.

0 Comments