ZIYAR CUNLIFF DA KYAFTIN MANU DA BARKEWAR YAKIN DUNIYA NA BIYU (WORLD WAR II)
Kyaftin Manu Zariya, mutumin zariya ne, shi ne bajintar da ya nuna ta bashi mukamin kyaftin a yakin duniya na Farko. Labarin wannan dakare akwai mamaki domin an ce wai shi mutum ne wanda baya jin harbi a fagen fama, saboda haka duk inda ya ratsa sai ya bar gawarwakin Jamusawa rududu a kwance sun sha dalma. Awani lokaci kuma an ce ya bar jamaar Hitler su gama harbe harben da aka hore su da yi, kafin ya nuna masu idan wajen kwashewa ne to ai ya yi musu nisa.
.
An ce Damarun da wannan Dantaliki ya yi amfani da su lokacin yakin duniya suna nan a gidan ajiye kayan tarihi na sojoji na kaduna.
.
Saboda irin wannan halayyar tasa da kuma yawan jamusawan da kyaftin Manu zariya ya kashe, sai Turawan Ingila na shakkarsa suna yi masa kirari da " KING GEORGE" watau Sarkin Ingila. Jamusawa ba su da takabus indai na Manu yakd. Halayyar irin yakinsa daban take da sauran sojoji da kuma irin abin al'ajabin da wannan dan tahaliki ke nunawa, sai ana yi masa rade radin cewa wai aljana yake da ita , don haka ne ba ya jin harbi. Wannan ya sa har kirari ake masa da " NA MANU MAI UWADDAMA" . Saboda yawan jini da ya zubar shi kansa sai da ya dan tabu, da ya komo kaduna ya zauna da mai Damusa har karshen rayuwarsa. Shi Mai damusa jarumi ne kuma kwararren sojan Igwa a wannan zamani, shi ma ya yi bajinta kwarai da gaske.
.
JANAR CUNLIFF YA KAWO ZIYARA
.
Domin tabbatar da godiyar Ingila bisa yadda shugabannin Arewa da jama'arsu suka mara mata baya a lokacin yakin Duniya na farko, sai shugaban Rundunar sojojin WAFF ya kawo masu ziyarar ban girma.
.
A watan Maris na shekarar 1919, Janar Cunliff da jama'arsa sun kai wa Sarkin Zazzau Aliyu Dan Sidi ziyarar ban girma. Janar din ya nuna godiyarsu bisa yadda aka taimakesu da Dakarun yaki. Wannan ziyara ta faranta wa sarkin da jama'ar sa rai ta kuma kara dankon zumunci tsakaninsu. Koda yake Turawan Ingila suna mulkin Mallaka a wannan lokaci, amma saboda muhimmanci abubuwan da 'yan Arewa suka yi masa game da isasshen goyon baya da suka nuna sun kara masu kwarjini da daraja a idanun Turawan ingilishi. Abin da Nigeriya ko kuma Arewa ta yi wa ingila, tarihi ba zai mainta da shi ba. Kamar yadda muka yi bayani idan bautn aikin soja ne Turawa 'yan Arewa suka sani suke kuma kauna ba domin komai ba sai don karewarsu tare da rashin tsoron su in dai batu na yaki ne.
.
BARKEWAR YAKIN DUNIYA NA BIYU
.
An gama yakin duniya na farko a cikin shekarar 1918, wannan ya sa an sallami sojoji da yawa. Amma barkewar yakin Duniyar na biyu a cikin shekarar 1939, ya dawo da kwasar sababbin sojoji domin a horar da su. Idan batu na yaki ne, to 'yan Ardwa ne aka sani, kuma su aka fi bukata ba don komai ba sai don kwardwarsu waje baiwa kura nama.
.
Sojojin da suka yi yakin duniya na farko sun fito da Arewa da Nijeriya baki daya ga idanun Duniya. Kasashen Duniya sun farga sun kuma waye wajen da cewa ba albarkar kasa nijerya kawai ke da shi ba, a'a har ma da na jama'a kuma jarumai. Abin da sojojin farko suka yi wa Arewacin wannan kasa , har zanzu mutanen wannan sashe su na cin moriyarsa. Da ba mu da jarumai ai da ba mu samu bataliyoyi da makarantun sojoji ba. Da yakin duniya na biyu ya barke sai aka dawo gidan jiya , aka kuma shiga kwasar sojoji. Sojojin yakin Duniya na biyu sun kara nuna wa duniya bajintarsu. Saboda wannan da sojojin yakin duniya na biyu sun kara nuna wa duniya bajintansu. Saboda wannan abin da sojojinmu suka yi sai ya kara mana mutumci a idanun Turawa. Idan ka duba ko a yanzu akwai manya manyan makarantu da bataliyoyin sojoji a Arewacin wannan kasa.
.
Kwarewar wannan yaki shi ma ya kawo bunkasar garin kaduna, sojojin da aka kwasa daga sassa dabam dabam bayan da aka sallame su sai suka koma da zama a wannan gari. Bayan da yakin ya kare sai Kaduna ta cika makil da tsofaffin sojoji. Ba ma karin jama'ar garin ya samu ba kawai, har ma da na gine gine da makarantu. Acikin shekarar 1944 aka gina babban Asibitin soja da ke Badiko don kula da sojojin da suka tagayyara a wajen yaki. An kare yakin Duniya na biyu cikin shekarar 1945.
.
Saboda matsayin Kaduna na hedkwatar Arewacin Nijeriya da kuma matsayinta na wajen horar da sojoji, sai garin ya samu babban barikin sojoji. A wannan gari ne aka samu sashen Rundunar soja BIRGED , ta farko wadda ake tafiyar da shugabancin sojojin Arewacin lardunan Arewa, ita ce kuma babaar tashar da ke da kayayyakin yaki na Nijeriya baki daya, a wannan lokaci. A ita wannan kungiyar masu gani ta soja GARRISON din akwai battaliya Ta Uku "3rd Battalion", 1 Frield Battery da 'yan Atilare (sojojin Igwa masu farmaki daga nesa). Sannan kuma ga injiniyoyin sojojin Nijeriya duk a wannan Birged dake Garin kaduna., ,
0 Comments