FARKON ZUWAN JIRGI KASA BIRNIN ZARIYA
.
Jirgin kasa ya fara zuwa Birnin Zazzau a ranar 20 gawatan Janairu na shekarar 1911. An bude hanyar jirgin cikin watan Fabrairu na wannan shekara. Wanda ya bude muhimmiyar hanyar shi ne Mukaddashin Gwamna, Mista C. L. Temple.
.
A wannan lokacin zage zagi sun nuna farinciki da gaske, farin cikin samun nasarar aikin hanyar jirgin, kuma suna murna da zuwan jirgin kasa birnin su. Domin su nuna farin cikin su, sai aka yi babban biki zuwan jirgin. Cikin karamin lokaci sai Sarki da manyan shuwagabanni suka shiga shirye shiryen bikin DABA, An gayyato baki daga ko'ina cikin kasashen Hausa. A wannan biki ne kcilun da ke kudancin zariya suka fara shiga Birnin Zazzau. Domin su ma an gayyato su zuwa wannan biki.
.
An yi wannan bikin Daba a ranar 22 ga watan yuni na shekarar 1911. Lokacin wannan biki, an kawo jiragen kasa na musamman guda ashirin. Manyan baki da shugabanni sun hallara. Ga 'yan sanda, ga sojoji masu fareti da sojojin doki dauke da bindigogi duk sun hadu , ga 'yan bigilanti ga makada da mawaka da sauran jama'ar gari da manyan baki, kowa sai murna ya ke yi. Wanda ya bude bikin dabar shine Mukaddashin Gamna Mista C. L temple.
.
Taragunan jiragen sun cika makin da 'yan biki, sun bar zariya da safe misalin karfe 7:00 na ranar 2 ga watan Yuli na shekarar 1911. Jirgi ya taho da su , ya biyo ta Kaduna sai Minna zuwa Dungurun zuwa Baro. Basu isa Lakwaja ba sai ranar 3 ga watan Yuli na shekarar 1911, watau kashegari. An yi wannan muhimmiyar tafiyar tarihi cikin sa'o'i talatin dhawan bangirma na musamman.
.
A cikin wadannan sa'o'i (30hrs) 'yan bikin Dabar na cike da farin ciki da murna da jin dadi.
.
JIRGIN KASA NA FARKO DA ITACE ( KWAKWALAGI) YAKE YIN AIKI KAFIN BULLOWAR GAWAYIN KWAL, KUMA TARAGUNAN JIRGIN ABU DE SUKE BASU DA RUFI.
0 Comments