ZUWAN TURAWA AREWA
.
A ranar litini, daya ga watan Janairu na shekarar 1900, Turawan Mulkin Mallaka ( British Crown), karkashin Kyaftin Lugga suka karbi Mulkin Nigeria ta Arewa daga hannun Turawan kamfani. Shi kyaftin Lugga sai ya zama Gwamnan farko na sashen Arewa a wannan kasa. A wannan ranar ce kuma ya kwantar da tutar Turawan kamfani ya tayar da tutar Turawan Mulkin da sanyin safiyar wannan Ranar a Lakwaja.
.
Lakwaja ce hedkwatar farko, donin tana da babar tashar jirgin ruwa, a nan ne kogunan kwara da na Binuwai suka hade. Karbar wannan mulki da turawan ingila suka yi sai ya sa Turawa zuwa Nigeria domin kasuwanci da tafiyar da mulkin mallaka. Sabboda haka za zama tilas a neman musu wajen zama, kogunan kwara da na binuwai suna saukaka zirga zirga amma abin takaici mazauna wajen na yawan yin najasa a cikinsu.
.
Wannan dalili ya sa ruwan koguna ya gurbace harma ruwan sha ya kan gagari jama'a, duwatsun dake cikin wadannan kogunan kuma suna yawan lalata jiragen ruwan turawa. Idan kogin kwara ya ciga jirage basa yawo, lakwaja ta cika da karuwai birjik abin kyama.
.
Hankalin Turawa mazauna lakwaja ya tashi haikan saboda wannan matsaloli. Rahoton Gwamna Lugga na farkon shekarar 1900-1901, ya ce "Na yi imani cewa barin wannan hedkwata da kuma matsayinta na mazaunin turawa, ya zama dole, don haka sai a tashi neman waje mafi dacewa, inda najasa ba za ta gurbata ruwan shaba, kuma duwatsu ba za su lalata jiragen ruwammu ba".
.
Hakan ya sa aka kafa kungiyoyi suka bazama ne man wajen da ya fi dacewa. Manjo Morland, watau Baturen sojan da ake wa lakabi da Mai Madubi da kungiyarsa sai aka umurcesu da subi kogin Kadduna. Latana Monk Manson da tawagarsa su bi Tsawon kogin Gurara, shi kuma Laftana Lowry Cole da tawagarsa subi Kogin Okwa da ke kan kogin Binuwai, kuma aka umurce su da kada su sake suyi fada da jama'a, sannan anyi da su za'a hadu a Garin Girku. Nan danan kowa ya bazama kogin da aka turashi dan binciko inda zaa kafa sabuwar hedkwata.
.
.
A cikin farkon watan Fabrairu na shekarar 1901, Manjo Morland wanda ya bi kogin Kadduna da Laftanu Lowry Cole daga kogin Okwa suka iso zariya a lokacin sarkin zazzau kwasau. Su wadannan 'yan bincike sun hadu ne a Girku daga nan suka Runtumo zuwa birnin Zariya.
.
Duk 'yan kungiyoyin binciko inda za'a kafa ita wannan sabuwar hedkwata sun yi kyakkyawar aiki amma babu wani rahoto wanda ya yi nuni da wajen da ya dace a zauna. Hakan ya kara tayar da hankalin turawa sosai, turawa sun tashi haikan wajen neman wajen da zasu zauna, amma abin ya ci tura.
.
To wata kila garin wishsh zai dace don kuwa ana iya bi ta kogin kadduna a kai gareta kuma akan yi watanni hudu jirage na kai komo. Wannan dalili yasa turawa kwaso kayayyakin su ta ruwa zuwa ga wannan gari.
.
Kash, zirga zirgar jiragen ruwa tsakanin Lakwaja zuwa wushishi akwai hadarin gaske, saboda 'yan fashi da sunji motsin jirgi suke fitowa su wazge dukiyoyin matafiya. Su wadannan 'yan fashi da ke kwantagora da Bida, sun hana jama'a sakat. Ganin irin wannan mummunan aikin nasu sai yasa baa karfafa maida garin wishishi hedkwata ba, muddin ba a samu shiryawa da su ba.
.
Tunda ga shi an riga an kwaso kayyyaki masu yawa daga lakwaja, sai ya tilasta neman wajen da za'a zauna, koda a gwaggwafe ne. Wannan ya sa Gwamna Lugga da Dr. Langley Da Mista Eaglesome ( shugaban firdaburdi) da Mista W. Evan Scott ( Baturen safiyo) da kyaftin Abadie ( Mai jimina) suka taso da kansu zuwa garin wishishi domin su gane wa idanuwansu yadda garin yake da kuma hanyoyin da za su bi don su tabbatar da an sami wurin zama. Sun taso a ranar 19 ga watan Janairun 1901.
.
Da wadannan manyan Turawa suka iso wushishi, sai Mista Eaglesome da Mista Scott suka yanki daji suka nufo garin don su duba wajajen da kyau. Daga baya sai suka dawo suka saida wa Gwamna cewa , a bayan gari za'a iya shimfida hanyar jirgi mai nisan kilomita ashirin da biyar, amma saboda wajen bai cika kyau ba, ruwa zai yi ta barna a kowace shekara, sa'annan aikin wannan hanya zai dauki tsawon misalin watanni goma sha biyu.
.
Jin wannan labari sai Gwamna ya ce tun da yake wannan sabon wurin da suka dubo bai da ce ba a cigaba a kan kogin kadduna su gani ko zasuyi gamo da katar.. Da turawa suka cigaba sai suka jimma wani waje mai ni'ima wanda yake kusan kilomita daya daga kogin kadduna, kuma kilomita biyar Arewa da garin wishishi. Sunan wannan waje " ZUNGURU" Ko "DUNGURUM".
.
KAFA DUNGURUN HEDKWATAR AREWA
.
Duk da kin garurwan da ke kusa da koguna da Gwamna Lugga yake yi, wannan sabon guri ya kayatar da shi fiya da sauran gurare. Wannan wajen yana da koramu masu ni'ima idan kuma kogin kadduna ta kawo tana daukar jiragen ruwa har nisan kilomita 10. A cikin watan Fabrairu na shekarar 1901 Gwamna ya zabi Dungurum ta zama hedkwatar Nigeriya ta Arewa.
.
Samun hedkwatar ke da wuya sai nan da nan Baturen Safiyo Mista W. Scott Evan da Mista Eaglesome suka tashi aiki haikan. Jim kan har an gina wa Gamna gida da dakunan ma'aikata ashirin da asibita da kuma ofisoshin ma'aikata. Kafin maris, al'amarin ginin hedkwatar sai aka shimfida hanyar jirgi da ta hade wushisi ( Gwari juko) da Dungurun. Jirgi ya fara bin hanyar a shekarar 1901. Turawan mulki sun tare a Dungurun a cikin watan Satunba na shekarar 1902.
.
SHIN ZAMA A DUNGURUN ZAI YI YU MA TURAWA KUWA? Idan ba zai yi yu ba WASU IRIN MATSALOLI SUKE FUSKANTA KUMA INA ZASU KO MA YA ZAMA HEDKWATAR SU? Ku kasance damu nan gaba dan jin wadannan amsoshin.
0 Comments