GUNDUMOMIN MULKI DAKE DA HAKIMAI A MASARAUTAR ZAZZAU
.
Gundumomin Mulki guda Tamanin da biyar (85) dake Masarautar zazzau suna karkashin kananan hukumomi Goma sha daya (11) na Masarautar zazzau.
.
KARAMAR HUKUMAR ZARIYA
1. Gundumar zariya da kewaye
2. Gundumar Tukur-Tukur
3. Gundumar waje T/wada zariya
4. Gundumar Dutsen abba
6. Gundumar wucicciri
.
KARAMAR HUKUMAR SABON GARI
1. Gundumar Sabon gari
2. Gundumar Hanwa
3. Gundumar Muciya
4. Gundumar samaru
5. Gundumar basawa
6. Gundumar Bomo
.
KARAMAR HUKUMAR SOBA
1. Gundumar Soba
2. Gundumar Maigana
3. Gundumar yakasai
4. Gundumar Turawa
5. Gundumar Ricifa
6. Gundumar Rahama
7. Gundumar Kusallo
.
KARAMAR HUKUMAR MAKARFI
1. Gundumar Makarfi
2. Gundumar Meyere
3. Gundumar Nasarawa
4. Gundumar Gubuci
5. Gundumar Ruma
6. Gundumar Gimi
7. Gundumar Gazara
.
KARAMAR HUKUMAR KUBAU
1. Gundumar kubau
2. Gundumar Anchau taka lafiya
3. Gundumar Gadas
4. Gundumar dutsen-wai
5. Gundumar pambeguwa
6. Gundumar kargi
7. Gundumar zuntu
.
KARAMAR HUKUMAR KADUNA TA KUDU
1. Gundumar kakuri
2. Gundumar sabon garin kaduna
3. Gundumar Badikko/kurmin mashi
4. Gundumar Unguwar mu'azu
5. Gundumar Tudun wadan kaduna
6. Gundumar Makera
7. Gundumar Barnawa
.
KARAMAR HUKUMAR KADUNA TA AREWA
1. Gundumar Doka
2. Gundumar Gabasawa
3. Gundumar Kawo
4. Gundumar unguwan shanu
5. Gundumar Malali
6. Gundumar Kabala
.
KARAMAR HUKUMAR KUDAN
1. Gundumar Hunkuyi
2. Gundumar Kudan
3. Gundumar Likoro
4. Gundumar kauran wali
5. Gundumar Doka
6. Gundumar Haskiya
.
KARAMAR HUKUMAR IGABI
1. Gundumar Rigasa
2. Gundumar Zangon Aya
3. Gundumar Turunku
4. Gundumar igabi
5. Gundumar Rigacikun
6. Gundumar farakwai
7. Gundumar gwaraji
8. Gundumar Sabon Birnin daji
9. Gundumar Kwarau
10. Gundumar fanshunu
11. Gundumar kerawa
12. Gundumar jaji
13. Gundumar afaka
14. Gundumar Gwada
.
KARAMAR HUKUMAR IKARA
1. Gundumar ikara
2. Gundumar Pala
3. Gundumar Furana
4. Gundumar Anchau
5. Gundumar saulawa
6. Gundumar Kurmin Kogo
7. Gundumar paki
.
KARAMAR HUKUMAR GIWA
1. Gundumar Shika
2. Gundumar Tsibiri
3. Gundumar Giwa
4. Gundumar Fatika
5. Gundumar yakawada
6. Gundumar dan mahawayi
7. Gundumar Kakangi
8. Gundumar Gangara
9. Gundumar kaya
10. Gundumar Karaukarau
11. Gundumar Kidandan
.
Wadannan su ne Hakiman kasar zazzau na asali da wadanda aka daukaka su suka zama Hakimai da sarauta da aka aro daga wasu kasashe aka nada su a wannan masarauta ta zazzau daga ciki akwai sarautar 'yan sarki da wadanda ba sarautar 'yan Sarki ba.
Haka kuma cikin wadannan sarautu akwai masu rike da kasa watau, Hakimai masu rike da kasa da kuma Hakiman Karaga wadanda ba su rike da kasa, sai dai rawani kawai.
.
Wadannan Gundumomi da kuma ambata a baya su ne garurwan Hakimai masu Kasa wadanda suke rike da Hakimcin wadannan garuruwa. An sami karin wadansu Gundumomi ne sakamakon karin masarautu da aka yi a jahar Kaduna a lokacin Gwamnar Jahar kaduna Ahmad Muhammad Makarfi lokacin da aka yanke wasu garuruwa na kudanci kasar zazzau ba a yi karin gundumomi ba har sai a lokacin mulkinsa.
.
Wadannan garuruwa duk suna karkashin masarauar zazzau ne a cikin kananan Hukumomi goma sha Daya (11) na Lardin zazzau, kuma kowace gunduma tana da Hakiminta da ke Mulkinta. Wadannan Hakimai suna gabatar da aikinsu a karkashin masarautar zazzau da karamar Hukuma. Akwai ayyuka da suka shafi masarautar watau, cibiyar masarautar zazzau (zazzau emirate council) a kan wata fadakarwa ko sako daga gwamnatin Jaha ko Tarayya to, za a nemi dukkan Hakimai su kuma su nemi Dagatansu don Gudanar da aiki ko sako. Haka kuma akwai ayyuka na musamman da Hakimai ke gabatarwa a karkashin Hukuma kamar abin da ya shafi harkas tsaro da lafiya da ilimi, da kare Hakkin dan Adam. Wadannan na cikin kadan daga ayyukan Hakimai.
.
Haka kuma akwai ayyuka da suka shafi raya al'adu da Addinai da kyautata zamantakewa tsakanin manoma da Fulani wanda a kullum masarauta da karamar Hukuma ke yi ma Hakimai tambihi a kai don a sami ci gaba da zaman lafiya a koina cikin zazzau.
0 Comments