TAKAITACCEN TARIHIN SARAKUNAN ZAZZAU DAGA GIDAN MALLAWA
.
Kamar yadda kuka sani yazo a tarihi an samu sarakuna guda hudu daga gidan sarautan mallawa, ga dan takaitaccen tarihin nasu kamar haka:-
.
1. SARKIN ZAZZAU MALAM MUSA
Malam Musa wanda ya yi yawon neman ilimi a wurare da dama ya kasance a kasar zazzau inda ya zauna a garin zariya don neman ilimi kafin bayyanar Shehu Usman Dan Fodiyo. Malam Musa ya yi karatu a babbar Makarantar nan mai Tarihi ta gidan Limamin Kona da ke zariya a karkashin shugabancin Malam Hamidu Limamin Kona na wancan lokaci. Ya yi karatun Littattafai da dama a makarantar kuma ya kasance daya daga cikin wadanda Liman ke turawa dan yin wa'azin Juma'a kasashen zazzau.
.
Bayan bayyanar Shehu Usman Dan Fodiyo daga nan Malam Musa ya tafi kasar Gobir inda ya sadu da Shehu Usman Dan Fodiyo don taimaka masa wurin tabbatar da Jihadin Musulunci. A sakamakon haka Shehu Usman ya turo su kasar zazzau don jaddada addinin Musulunci inda suka kori Habe daga mulki suka kafa daular Fulani ta zazzau, kuma suka dawo da tsare-tsaren Musulunci a Mulkin Fulani ya kawar da al'adun Habe marasa kyau kuma ya tabbatar da masu kyau. Ya hau gadon sarauta a shekarar 18 04. Ya rasu a shekara ta 1821. Daga nan Malam Yamusa Sarkin Zazzau, ya hau gadon sarauta, ya ci gaba da nasa tsarin daga gidan Barebari.
.
2. SARKIN ZAZZAU MALAM SIDI ABDULKADIR
Malam Sidi Abdulkadir shi ne babban Dan Malam Musa Sarkin Zazzau. An nada shi sarautar Dan Galadiman zazzau a zamanin da mahaifinsa Sarkin zazzau Malam Musa ke Sarkin zazzau. Haka kuma an fitar da shi a zamanin Sarkin zazzau Abdulkarim na gidan sarautar katsinawa, kuma shi ne ya fara yin wannan sarauta ta dan Galadima. Ya yi sarauta bayan rasuwar Sarkin zazzau Mamman sani na gidan sarautar Barebari bisa zabe da ake yi daga masu zaben sarki kuma an tabbatar masa da sarautar zazzau a zamanin Sarkin Musulmi Aliyu Babba a shekarar ya rasu. A cikin 'ya'yansa akwai Alu Dan Sidi wanda shima ya yi Sarkin zazzau.
.
3. SARKIN ZAZZAU ABUBAKAR DAN MALAM MUSA SARKIN ZAZZAU
.
Sarkin zazzau Abubakar yana daya daga cikin 'ya'yan Malam Musa Sarkin zazzau. An fara nada shi sarautar Madaki a lokacin Malam Abdulkarimu Sarkin zazzau, har zuwa lokacin Sarkin Zazzau Hammada wanda shi ya tube shi a madaki. Daga baya da Sidi dan Sarkin zazzau Musa ya yi Sarki , sai ya nada shi sarautar Wambai. Wani kauli kuma an ce, ya yi sarautar Iyan Kurama a zamanin Mulkin Mahaifinsa Malam Musa Sarkin Zazzau. Yana kan Sarautar Wambai, Allah ya yi masa Sarautar Zazzau, bayan Rasuwar Sarkin Zazzau Abdullahi dan Hammada. Ya yi Sarauta na tsawon shekaru uku da watanni 1871-1974 A. D
.
4. SARKIN ZAZZAU MALAM ALIYU DAN SIDI
.
Sarkin zazzau Malam Aliyu Dan Sidi yana cikin 'ya'yan Sarkin zazzau Sidi, kuma jika wurin Mal. Musa sarkin zazzau. An fara nada shi sarautar wambai yana kan wannan sarauta ne Allah ya yi masa sarki. Ya gaji sarkin zazzau Kwasau, dan sarkin zazzau Yero na gidan sarautar Barebari, a shekarar 1903 zuwa 1920 lokacin da aka tube shi daga sarauta aka tafi da shi garin Lokoja inda turawa suka tsare shi kuma a can Allah ya masa Rasuwa. Yanzu haka kabarinsa na nan a garin Lokoja.
.
Wannan shi ne takaitaccen tarihin Sarakunan gidan Sarautar Mallawa wadanda suka yi Sarki a zazzau, kuma su ne ke zaune a mafi yawancinsu a Unguwar Kwarbai cikin birnin zariya kuma su ne ke da tsaga guda biyu a bangaren dama da hagu na kumatunsu. Wannan Tsaga shi ake kira da Mallanci.
.
Ku kasance damu domin kawo muku takaitaccen tarihin sauran gidajen.
.
DAGA: KASAR ZAZZAU AJIYA DA YAU (Facebook)
ko kuma zaku iya ziyartan shafin mu na yanar gizo-gizo ta www.kasarzazzau.tk
0 Comments