TAKAITACCEN TARIN SARAKUNAN ZAZZAU DAGA GIDAN SARAUTAR KATSINAWA


GIDAN SARAUTAR KATSINAWA DA SARAKUNAN SU
.
Gidan sarautar Katsinawa a zazzau sun kafu ne a karkashin wani bawan Allah wanda ake kira Malam Muhammadu mutumin Bagdada. Lokacin da ya bar Kasar ya shigo Kasar Hausa ya fara zama ne a Daura da Gwarzo ta kasar Kano. A zamaninsa ne kuma ya haifi dansa da ake kira Nuruddin.. Daga baya ya koma Katsina inda ya zauna a wani gari da ake kira Jarkuki a inda ya sake samun haihuwa da namiji, aka sa masa suna Abbas. Malam Abbas shi ne ya haifi malam Abdulkarim jagoran gidan sarautar Katsinawa a zazzau, kuma Sarki na uku a jerin Sarakunan Fulanin Zazzau.
.
Wannan Gida na sarautar Katsinawan zazzau shi ne gida na uku a cikin jerin gidajen sarautun Fulani na zazzau. Sun yi Sarakuna guda hudu zuwa yanzu.
.
1. SARKIN ZAZZAU MALAM ABDULKARIM
Sarkin zazzau Abdulkarim shi ne sarki na farko a gidan sarautar Katsinawa, kuma shi ne ya kafa gidan. Ya yi sarautar Sa'in zazzau a lokacin Mulkin Malam Musa Sarkin zazzau. Ya yi Sarki bayan Rasuwar Malam Yamusa Sarkin zazzau daga shekarar 1834-1846. Yana da 'ya'ya kuma cikinsu wanda ya yi sarki shi ne, Sarkin zazzau Sambo dan Abdulkarim.
.
2. SARKIN ZAZZAU MALAM SAMBO
Sarkin zazzau Sambo dan Abdulkarim yana daya daga cikin 'ya'yan Malam Abdulkarim Sarkin zazzau. Ya yi sarautar Wambai Kafin ya zama Sarkin Zazzau. Ya samu sarautar Zazzau bayan rasuwar Sarkin zazzau Abubakar na  gidan sarautar Mallawa daga Shekarar 1879-1888. Yanzu haka jikansa ne ke sarautar zazzau.
.
3. SARKIN ZAZZAU MALAM MUHAMMADU AMINU
.
Sarkin zazzau Malam Muhammadu Aminu shi dan Abubakar Kwasau ne. Shi kuma Abubakar Kwasau dan Iyan zazzau Usman dan Sarkin zazzau Abdulkarimu ne. An fara nada shi sarautar sarkin Tsabta kafin iyan zazzau a zamanin Sarkin Zazzau Ja'afaru. Shi ne sarki na goma sha bakwai cikin jerin sarakunan Fulani a zazzau. Ya yi mulki daga shekarar 1959-1975.
.
4. SARKIN ZAZZAU SHEHU IDRIS
Sarkin Zazzau Shehu Idris, shi jika ne wurin sarkin zazzau Sambo. An fara nada shi sarautar Wakilin Ofis kafin sarautar dan Madamin zazzau. Ya hau gadon sarautar zazzau a shekarar 1975 har zuwa yanzu. Shi ne Sarki na goma sha takwas, kuma shi ne sarkin da ya fi kowane sarki dadewa a Mulkin zazzau, a yanzu. Allah ya karama sarki lafiya
.
Ku kasance da KASAR ZAZZAU A JIYA DA YAU dan samun tarihin sauran Gidan dama wasu tarihin masarautar zazzau.�
.
Wannan shine dan takaitaccen tarihin Sarakunan zazzau daga gidan Katsinawa. ku kasance damu domin kawo muku na sauran gidajen
.
Daga: KASAR ZAZZAU AJIYA DA YAU (Facebook)

ko kuma zaku iya ziyartan shafin mu na yanar gizo-gizo ta www.kasarzazzau.tk

Post a Comment

0 Comments