TAKAITACCEN TARIN SARKIN ZAZZAU DAGA GIDAN SARAUTAR SULLUBAWA

TAKAITACCEN TARIN SARKIN ZAZZAU DAGA GIDAN SARAUTAR SULLUBAWA
.
Gidan sarautar Sullubawa su ne ake ma lakabi da Fulanin Iba da kuma ake kiran su Sullubawa. Wannan gidan sarauta ya kafu ne a karkashin Malam Abdulsalam Sarkin zazzau. Kuma shi ne Sarki na bakwai a Daular Fulani daga kansa ba a kara sarauta ta Sarki a gidan ba.
.
SARKIN ZAZZAU MALAM ABDULSALAM
Sarkin zazzau Malam Abdulsalam shi ne ya kafa sarautar gidan Sullubawa, kuma shi ne ya fara yin sarautar Makaman zazzau a lokacin Mulkin Fulani. Ya yi sarautar zazzau bayan an fitar da Sarkin zazzau Sidi Abdulkadir a sarauta. Ya yi mulki daga shekarar 1853-1857. Yanzu haka zuri'arsa na nan a Unguwar Bishar , cikin Birnin zariya.
.

Wannan shine dan takaitaccen tarihin Sarkin zazzau daga gidan Sullubawa. ku kasance damu .
,
Daga: KASAR ZAZZAU AJIYA DA YAU (Facebook)

ko kuma zaku iya ziyartan shafin mu na yanar gizo-gizo ta www.kasarzazzau.tk

Post a Comment

0 Comments