TARIHIN ABBAS MUHAMMAD FAGACHI (SARKIN AYYUKAN ZAZZAU)- Daga kasar zazzau a jiya da yau
.
Malam Abbas Fagachi, ya fito ne daga cikin zuri'ar Katukan zazzau Malam Usman Tsoho (SABULU), Wanda shi ne katuka na farko a zazzau, tun daga lokacin da Fulani suka karbi mulki a hannun Habe a shekarar 1804. Zuriar Usman Tshoho sun yi katuka har guda shida, tun daga zamanin Malam Musa Sarkin Zazzau Har Izuwa Zamanin Sarkin Zazzau Alu Dan Sidi, su ke rike da wannan sarauta ta Katukan zazzau.
.
Katuka Usman Tsoho shi ne kakan Marigayi Fagacin Zazzau Alh. Muhammadu, wanda aka fara nadawa sarautar Sarkin Ayyukan Zazzau a zamanin mulkin Sarkin zazzau Ibrahim Dan Kwasau a shekarar 1935.
An nada shi Fagacin zazzau Hakimin kasar giwa a shekarar 1941, kuma ya yi Hakimin Kasar Ikara a tsakanin 1959 zuwa 1960. An koma da shi Makarfi daga shekarar 1961 zuwa 1978. Yana cikin manyan 'yan majalisar sarkin zazzau kuma mai zaben sarki, ya rasu a ranar 22 ga Afirilu, 1984. Zuri'ar Fagaci Muhammadu suke rike da sarautar fagaci har zuwa yau, kuma daga cikin wannan zuru'a ne aka haifi Abbas muhammad Fagaci.
.
An haifi ABBAS MUHAMMAD FAGACHI a kofar Fada, cikin Garin Makarfi, a karamar hukumar Makarfi a cikin shekarar 1966. Ya fara karatunsa na addini a Makarantar Malam Abdu Mahaddaci da ke garin Makarfi. Bayan ya yi nisa da karatun nasa ne na addini sai aka sa shi a makarantar Firamare ta Makarfi a shekarar 1973. A cikin shekarar 1978 aka dawo da shi Zariya inda ya karasa karatun Firamare, a Makarantar Firamare ta Unguwar kaho a shekara ta 1978. Bayan ya kammala karatun Firamare, ya sami shiga Makarantar Sakandare ta Dutsin-Ma a cikin shekara ta 1979, daga baya ya sami canji zuwa Makarantar Sakandare ta Alhudahuda dake zariya daga 1979-1984. Bayan ya kammala karatun sakandare ya sami shiga Jami'ar Ahmadu Bello, inda ya yi karatun Difloma a Makarantar Koyan Aikin Mulki da ke Kongo daga Shekarar 1984 zuwa 1986. Ya sake komawa Jami'ar Ahmadu Bello inda yayi karatu na Difloma a kan aikin Shari'a a Tsangayar Koyar da Shari'ar Musulunci daga 2004 zuwa 2006. Ya sake komawa Jami'ar Ahmadu Bello , a Tsangayar koyon Aikin Lauya daga 2007-2011. Ya tafi Makarantar Horon Lauyoyi da ke Kano a shekara ta 2011 zuwa 2012, ya halarci kwas din babbar Difloma a harkar ilimi a Makarantan horas da Malamai ta Gwamnatin Tarayya da ke zariya. Ya sami shaidar Karatun Digiri na biyu kan karatun Lauya a jami'ar Ahmadu Bello da ke zariya.
.
Ya kuma halarci kwasa-kwasai da dama a kan koyon Harshen Larabci kamar haka: FCE Zaria 2001-2002; Sheik Abubakar Mahmud Gumi College (Higher Islam) 2004-2005.
.
A bangaren aikin Gwamnati, ya yi aiki da kamfanin sai da kayan Gona na Jihar Kaduna (FASCOM) a shekarar 1986-1991.
Ya koma yayi aiki da kotun Daukaka Kara ta Tarayya (Federal Court of Appeal, Kaduna) 1991-1996 daga nan ya ajiye aiki don kansa. Yanzu Abbas Malami ne a Makarantar Kimiya da Fasaha ta Nuhu Bamalli da ke zariya, yana da 'ya'ya ashirin da bakwai da mata hudu.�
.
Abubuwan sha'awan Malam Abbas Muhammad Fagaci sun hada da rubuce-rubuce da kuma yawaita karatu. Kuma ya wallafa littafai da dama kamar haka:
1. Tarihin Mai Martaba Sarkin Zazzau Alh. Dr Shehu Idris
2. The Intellectual Tradition in Northern Emirates.
3. Sarautu da Al'adun na Masarautar Zazzau.
4. Tarihin Rayuwar Malam Yusuf Aboki ( Makama Babba)
5. The 40th Anniversary of a Distinguished ruler.
6. The Traditiona
Title Holders of Katsinawa Dynasty in zazzau Emirate
7. Historical Perspective of a Teacher
8. Rayuwar ilimi
9. Historical Origin of Traditional Titles and Cultures of Zazzau Emirate.
Muna fata Allah ya ma rayuwarsa Albarka ya kara ma masarautar zazzau mutane masu hazaka da basira irin sa. Allah ya kara masa lafiya da kwanciyar hankali Ameen�
Daga: Kasar zazzau Ajiya da yau (Facebook)
Wepsite: www.kasarzazzau.tk
0 Comments