TSARIN HAKIMAI DA AIKINSU DA KIRARINSU (1)

TSARIN HAKIMAI DA AIKINSU DA KIRARINSU
.
KASHI NA FARKO (1)
.
A tsarin mulki irin na Habe kowane Hakimi cikin manyan Hakimai yana da sarava kuma da ma'anarta da kuma irin kirarin da ake yin ma wannan sarava sannan da irin aikin da ya rataya a wuyar wannan sarauta. Haka kuma akwai sarautun wasu daga cikin Hakimai wadanda suke karkashin wadannan manyan Hakimai kamar yadda za a gani a tsarin ayyukan Hakiman.
.
Amma yanzu a tsarin Mulkin Fulani, wadannan Hakimai da ke karkashin manyan Hakimai a yanzu, duk Hakimai ne masu cin gashin kansu scoda canje canje da aka samu lokacin mulkin Fulani. Bari mu kawo kirarc da tsarin sarautu da ma'anonin su kamar haka;
.
Kirarai wani abu ne ko wasu kalmomi ne da ake fada ma mutum ko kuma akan alakanta shi da su don daukkakansa, ko don halayensa ko jarumta ko don asalinsa. Watau , wasu zababbun Kalmomi ne da ake furtawa domin zuga ko kambamawa.
.
Akan kuma yi ma mutum kirari da surarsa, kamar tsawo ko fadi ko gajarta, ko kuma a yi masa kirari da sana'arsa da ya gwanance a kai. Mafi yawancin kirarin da ake yi wa masu sarauta ana yi ne a dalilin jarunta ko wajen yaki, ko kusantaka da matsayi a wajen sarki ko kuma domin kwarjini da kasaita ko kuma asali.
.
Wadannan kirari na Hakimai kusan duk daya ne ake yin su a kasashen Hausa, amma wasu sun sha bambam. Misali, duk inda ka je za ka ji kirarin waziri iri guda ne, kamar haka, "waziri babba Gwadabe" ko kuma Madaki za ka ji ana ce masa: "Goje gaban gayya". Kirari kuma na iya shafar wasu ko wani mutum da ya rike wata sarauta, kuma kirarin na nan har yau. Misali sarautar cigari, ta samo asali ne daga Sarkin Kano Yusuf na Dabo Cigari. Daga nan aka sami Kirari ga kowane Sarki.
.
Yanzu kuma bari mu kawo tsarin sarautu tare da kirarinsu kamar haka:-
.
MADAKIN ZAZZAU
Sarautar Madaki a zazzau ta samo Asali ne daga Mulkin Habe, amma su Habe suna kiranta Madawaki kuma ita ce sarauta mafi girma cikin sarautun Hakimai, 'Ya'yan sarki, kuma shi ne shugaban rundunar mayaka. Ba'a nada Sarki ko cire shi sai da yardar Madaki. Kuma shi ne jagoran Hakimai a kowane irin taro kamar gaisuwar fada ko gaisuwar Shekara. Amma a mulkin daular fulani an sami bambanci inda sarautar Madaki sai Babban dan Sarki kurum ake ba wannan sarauta. Wanda ya fara wannan sarauta A Mulkin daular Fulani shi ne Malam Yamusa, Sarkin zazzau, a zamanin Malam Musa, Sarkin zazzau kuma daga kansa ne Madaki ya fara sarki kuma darajar wannan sarauta ta daukaka ta zama muhimmiya a wannan masarauta ta zazzau. Bisa tsarin Mulkin Fulani, Madaki shi ne Babba cikin 'ya'yan Sarki, kuma shi ne shugaban 'ya'yan Sarki duka. Sarkin zazzau Malam Yamusa, shi ne ya gaji Madaki ma kaye na Habe, a zamanin Sarkin zazzau Malam Musa.
.
KIRARIN MADAKI
" KACI KACALA,
GOJE UBAN FADAWA,
ABUBBUGARI SANDAN FADAN SARKI,
KODA MASO ZUBAN JINI
KODA MASU SHASSHAWA
KARI KIKI BABBAR LAYA
WANDAWA DA KAI AKA GAYYA
DAN UBAN GABASAWA."
Wadannan kalmomi na kirarin Madaki, duka kalmomi ne na jaruntaka a kan yaki saboda saravar asalinta ta mayaka ce.
.
�WAZIRAN DA AKA NADA A ZAZZAU TUN DAGA 1804-DATE
.
1. Wazirin Zazzau Cifudu.
2. Wazirin Zazzau Muhammadu Bello dan Alkali
3. Wazirin Zazzau Malam Bako
4. Wazirin Zazzau Malam Ahmadu
5. Wazirin Zazzau Malam Yusuf
6. Wazirin Zazzau Malam Lawal
7. Wazirin Zazzau Malam Muhammadu Sunusi
8. Wazirin Zazzau Malam Nuhu Yahaya
9. Wazirin Zazzau Alh. Abdurrahaman Jumare Yahaya
10. Wazirin Zazzau Alh. Ibrahim Aminu
.
WAZIRIN ZAZZAU
Waziri a masarautar zazzau, shi ne mataimaki na Sarki kuma wazirin Sarki a kan wani abu da sarki bai sami yi ko halarta ba. Kuma yana cikin manyan 'yan Majalisar Sarki, kuma shi ake turawa a kan wata hidima wadda ta shafi sarki da sarkin wata kasa. Amma bisa tsarin mulki irin na Fulani waziri a kasar zazzau shi ne babba a duka gaba dayan Hakimai, 'ya'yan sarki da wadanda ba 'ya'yan Sarki ba, duk suna karkashinsa. Kuma shi ne babban dan Majalisar Sarki, kuma daya daga cikin masu zaben sarki kuma shi ne ke rike Gari idan Sarki ya yi tafiya mai nisa. Wanda ya fara wannan sarauta ta waziri a daular Mulkin Fulani shi ne waziri Cifudu a zamanin Malam Musa sarkin zazzau. Amma wannan sarauta ta waziri, ba ta da karfi sosai a wancan lokaci na mulkin Habe.
.
KIRARIN WAZIRI

"WAZIRI BABBAN GWADABE
WAZIRIN SHEKASA TAFE
WAZIRI LAWALI ABIN BIYA
JIRGI UBAN FADAWA
LAWALI MAI SARKI
A BI HANYA A DAINA RATSE"

Wannan shi ne kirarin waziri, ana nuna matsayinsa da girman sarautar cikin kirarinsa. Misali, waziri Babban Gwadabe, na nufin waziri Babbar Hanya, ta zuwa ga Sarki. Gwadabe na nufin hanya a Sakkwatanci. Haka kuma waziri shekara tafe, ana nufin wazirin sarki, soboda Sarki ne ake ma kirari da "shekara tafe" da ke dauke da ma'anar, idan ya fara yaki, sai ya kai inda ya yi niyyi.
.
A karkashin rarautar waziri akwai sarautar dan Galadiman waziri, wanda yake Hakimi ne a karkashin waziri. Kuma sarauta ce wacce ake nada ta a gaban Sarki ga wanda waziri ya amince da shi ya ba shi sarautar amma ba waziri zai nada shi ba, Sarki ke nadawa kamar yadda ake nada kowane Hakimi.  Wannan ya saba wa na sauran Hakimai da za su nada Hakimansu a gabansu, ba tare da an zo da su gaban Sarki ba.
.
MAGAJIN GARIN ZAZZAU
Sarautar Magajin Gari ta kafu ne a lokacin Mulkin daular Fulani amma a lokacin Mulkin Habe ana kiran ta Magajin Dangi kuma tana daya daga cikin sarautu masu mahimmanci cikin saravar 'ya'yan sarki. Wannan sarauta ta sami canji a lokacin Fulani inda suka daukaka ta suka mayar da ita sarautar 'ya'yan Sarki a kasar zazzau. Kuma aka kira ta Magajin Gari. Wanda ya fara wannan sarauta ta Magajin gari Shi ne magajin Gari malam zakari dan Malam Musa Sarkin zazzau a zamanin sarkin zazzau Malam Musa, na gidan Mallawa.
.
KIRARIN MAGAJIN GARI
" JIRGI MAI ATAGWANNI,
MAGAJI ABOKIN SARKI,
MAGAJI ABOKIN DODO,
DANO BABBA MAGAJI,
BA A MAGAJI DA YARO,
DAN UBAN GABASAWA."
Wannan shi ne kirarin Magajin Gari kuma ana fadin irin matsayinsa da daukakarsa cikin kirarinsa kamar haka, Magaji abokin Sarki, Magaji abokin Dodo. Ma'ana, ya kusanta da sarki. Sai jirgin mai atagwanne.� ma'ana, mai rishi da takama kuma tun kafin ya zo akan ji amonsa (sautu).

Post a Comment

0 Comments