TSARIN SARAUTAN FULANI A ZAZZAU

TSARIN SARAUTAN FULANI A ZAZZAU
.
Sarautar Fulani ta kafu ne a dalilin cin Habe da yaki karkashin jihadin Shehu Usman dan Fodiyo. Bayan cin nasarar kwace kasar Zazzau sai Fulani suka ci gaba da tafiyar da Mulkin kasar tare da ci gaba da wasu daga cikin al'adun Habe. A zamanin Habe, ana ba macf ce sarautar Iya da Mardanni inda a zamanin Fulani, sarki na farko watau, Malam Musa Sarkin zazzau ya mai da wannan sarautana Habe akan 'ya'yansa mata Iya Atu da Mardanni A'i 'ya'yan Malam Musa sarkin zazzau. Daga baya bayan rasuwar sa sai Malam Yamusa ya gaje shi kuma ya karbi wannan sarauta Ta Iya da Mardanni ya ba 'yan uwansa maza. Daga wannan lokaci ba a kara ba wata Mace sarauta ba. Ma'ana aka share wannan al'ada ta Habe da mulani suka dauka. Daular Fulani tana da tsarin sarautu natana asali haka kuma akwai sarautu da aka aro daga wasu kasashe wanda ita ba ta da wadannan sarautu a tsarin sarautunta. Ga tsarin sarautun.
1. Madaki
2. Galadima
3. Wambai
4. Dallatu
5. Iya
6. Mardanni
7. Dan galadima
8. Magajin gari
9. Dan madami
10. Turaki karami
11. Salanke
12. Sarkin ruwa
13. Katuka
14. Wali
15. Sa'i
16. Jisambo
17. Makama babba
18. Wan'ya
19. Kuyambana
20. Rubu
21. Fagaci
22. Ma'aji
23. Turaki babba
24. Sarkin Fada
25. Barde
26. Madauci
27. Sarkin yaki
28. Waziri
29. Sarkin zana
30. Shantali
31. Tafida
32. Barden kudu
33. Barden gabas
34. Barden arewa
35. Barden yamma
36. Turakin Dawaki
37. Garkuwa
38. Kuyambana
39. Danmori
40. Sarkin Mai
41. Sarkin shanu
42. Karfen dawaki
43. Galadiman dawaki
44. Sarkin yara
45. Makama karami
46. Fagacin dawaki
47. Tafarki
48. Makaman doka
wadannan  su ne sarautun Fulani na asali wanda suka kirkira da wanda suka gada wajen Habe suka hada. Haka kuma akwai sarautu wanda ake ba 'ya'yan sarki da sauran wasu mutane amma an aro su ne daga wasu garuruwa suka zama cikin sarautun Fulani na zazzau. Wadannan sarautu, an aro su ne , wasu a zamanin sakin zazzau Jafaru  da sarkin zazzau Aminu, wasu kuma a lokacin Sarkin zazzau Shehu Idris. Amma mafi yawan sarautun da aka aro, su ne a zamanin sarkin zazzau shehu Idris.
1. Ciroma
2. Tafida
3. Sarkin Fulani
4. Dan iya
5. Dan masani
6. Dan buran
7. Marafa
8. Yarima
9. Dan isa
10. Dan Maje
11. Sarkin kudu
12. Talba
13. Barade
14. Koguna
15. Santuraki
16. Sarkin dawakin Tsakargida
17. Bunu
18. Dan kade
19. Uban doma
20. Dan lawal
21. Sarkin Baura
22. Dan darman
23. Sarkin sudan
24. Durbi
25. Dan amar
26. Dan makwayo
27. 'Yan doto
28. Gado da masu
29. Shatima
30. Maina
31. Garkuwan soro
32. 'yan daka
33. Mayana
34. Zanna
35. Sarkin bai
36. Magajin Rafi
37. Sarkin Gabas
38. Sarkin Arewa
39. Cika Soro
40. Daneji
41. Maradi
42. Sarkin baura
43. Dan ruwata
44. Dan adala
45. Sardauna
46. Majikira
47. Uban Gari
48. Makama gado da masu
49. Dan barhim
50. Bebeji
51. Barde kerarriya
52. Uban dawaki
wadannan su ne sarautun da aka aro su daga wasu kasashen na Mulkin daular Fulani kamar sakkwato da kano da Katsina da Bauchi da Adamawa. Irin wannan aron sarauta ana yi a tsakanin kasa da kasa domin su�  Ma sauran kasashen za ka ga sun nada sarautun da ba nasu ba a matsayin aro daga wata kasar.
.
Haka kuma akwai sarautu wadanda aka yi su a matsayin aiki kamar sarautu masu lakabin sarakuna ko  wakilai. Wadannan sarautu sun kafu ne a sakamakon aikin En'e (N.A) Turawa, inda aka raba ma'aikatu kamar bangarorin sharia da kurkuku da tsabta da ma'aikatan gona da ilimi da sana'a da ayyuka. Duk wadannan suna da sarautu akan shuwagabanninsu kamar haka:
1. Wakilin Raya Kasa
2. Wakilin Biya
3. Wakilin Birni
4. Wakilin Sana'a
5. Wakilin Asibiti
6. Wakilin Tsabta
7. Wakilin Magani
8. Wakilin Gona
9. Wakilin waje
10. Wakilin Gabas
11. Wakilin kudu
12. Wakilin arewa
13. Wakilin Fulani
14. Wakilin yaki da jahilci
15. Wakilin yamma
16. Wakilin Makaranta
17. Wakilin watsa Labarai
18. Wakilin doka
19. Wakilin ofis
20. Wakilin daji
21. Wakilin kahu
22. Wakilin Ruwa
23. Wakilin Bai
24. Wakilin Masallaci
25. Wakilin Falaki
26. Wakilin Malamai
Cikin wadannan sarautu na wakilai , sarautun da suka fi dadewa su ne sarautun wakilin Gabas da Yamma da Kudu da Arewa. Saboda su wakilai ne da sarki ke tura su wasu bangarori na kasa domin gabatar da ayyuka na musamman. To amma baya zuwan Turawa sai aka dora ma wakilan Raya kasa wadannan ayyuka duka kusanshi ne shugaban wakilan duka. Kowa zai zo da bayanin aiki zuwa gare shi, shi kuma ya gabatar zuwa ga sarki don aiwatarwa ko gyare-gyare.
.
Haka kuma sarauta irin ta wakilin doka ita ma ta sami asali ne da daukaka daga lokacin Mulkin Turawa. A wancan lokaci ne aka ba sarakunan Arewa shawara da su rika nada 'ya'yansu sarautar wakilcin doka, watau wakilci mai kula da sha'anin tsaro na wannan masarauta. Shi ne ya kawo dalilin da sarakunan Arewa suka fara nada 'ya'yansu irin wannan mukami da zarar sun kamala karatunsu. Kamar misali a Sakkwato an nada Muhammadu Maccido dan Sarkin Musulmi Abubakar, Sarkin Kano Abdullahi bayero ya nada. Ado Bayero a matsayin Wakilin dokan Kano, haka kuma a Katsina Sarkin Katsina Dikko ya nada Usman Nagogo, a matsayin Wakilin Dokan Katsina, haka kuma a Adamawa aka ba Lamidan Adamawa Alh. Aliyu Mustapha sarautar Wakilin Dokan Adamawa. A zariya Malam Ibrahim Sarkin Zazzau ya nada Alhaji Lawal Doka a matsayin wakilin Doka.
.
Wadannan su ne wakilan Sarki a kan harkar tsaro tare da yin bayani a kan cin da ya shafi tsaro na kasa tsakanin Sarkin da Turawan mulki  a wancan lokaci.
.
Sauran sarautu kuma kamar sarautar Sarkin Gandu da sarkin kofa da sarautar yari dama akwai su tun lokacin da sarkin kofa da sarautar Yari dama akwai su tun lokacin Mulkin Habe, amma an ba su matsayi na shugabancin kula da wasu bangarori a lokacin aikin En'e (Native Authority).
.
Wadannan su ne sarautun da ake kira wakilan ma'aikatu kuma a wasu lokutan baya ana ba wanda ke shugabancin ma'aikata ne sarautar wakilinta, amma yanzu akwai bambanci. Ana iya ba kowa wannan sarauta ta wakilci ko (Sarki). Wadannan wakilai ko sarakuna su ne wakilan sarki a wancan lokaci akan duk abin da aka ba ka wakilci kuma wajibi ne a gabatar ma da sarki bayani a kan wannan ma'aikata da ake shugabanta. Wannan shi ne matsayin wadannan sarautu na wakilai.
.
Madaki da wambai da dan Galadima da Dallatu da Magajin Gari da Iya da Wali da Sa'i da Sarkin Ruwa da Turaki Karami wadannan kusan duk sarautu ne da ake ba 'yan Sarki. Amma an sami wasu zamuna na wasu sarakuna da aka ba da wasu daga cikin irin wadannan sarautu kamar Turaki da Sarkin Ruwa da Sa'i da Salanke da Galadima da Dallatu, ga wadanda ba 'ya'yan Sarki ba , a lokutan wasu sarakuna.
.
An sami karin sarautu wadanda aka aro daga wasu kasashe aka ba 'ya'yan Sarki a yanzu. Wadannan sun hada da sarautar Talba da yarima da Sarkin Kudu, Sarkin dawakin Tsakar Gida, Koguna da Dan isah da Dan Darman da Sarkin Baura da Bunu da dan Maje da Uban Doma da Dan Lawan da Barade da Barden kudu da 'yandoto da Durbi da Dan Ruwata da Majikira da Ubangari da Dan barhim da Barde Kerarriya da dan Adala Cikasoro.
.
Wadannan sarautu duk 'ya'yan Sarki ke rike da su a yanzu kuma sabbin sarautu ne da aka aro na 'ya'yan sarki daga wasu masarautu a na kuma iya ba da su ga mutanen da ba 'ya'yan Sarki ba.
Wadannan sarautu sunsaga cikin tsarin sarautu na 'ya'yan Sarki a zazzau, banda sarautar Madaki kusan kowace sarauta ta 'ya'yan Sarki akan daukakata ta zama babbar sarauta, ta zama ita ce ta biyu, wannan yana faruwa ne idan akwai wata alaka ta musamman tsakanin Sarki da Hakimi.

Post a Comment

0 Comments