TSARIN SARAUTUN HABE A ZAZZAU
Karkashin sarautun habe da fulani a kasar zazzau akwai tsari uku na sarautu. Na farko, sarautar 'ya'yan Sarki. Ma'ana , a nan ita ce duk wanda ya gaji sarauta ya yi Sarki sunansa Dan sarki. Na biyu, sarautar wadanda ba 'ya'yan sarki ba, wadanda aka nada su bisa aminci ko jaruntaka. Na uku, sarautar bayin Sarki, wacce akan ba bayin sarki ne kawai. Kuma kamar yadda aka nuna a baya cewa akwai bambanci a tsakanin sarautun Habe da na Fulani a wasu wurare, kamar bangaren tsarin aiki, ko bauta da kuma wurin sunan sarauta. Kamar Madawaki da Madaki ko kuma Magajin Gari da Magajin Dangi. A tsarin Habe ana kiran Sarautar Madaki da Madawaki , a tsarin Fulani suna cewa Madaki haka kuma Habe suna kiran Saravar Magajin Gari da Magajin Dangi. Haka kuma bisa tsarin sarautar Habe Babban Dan sarki ake ba Sarautan Dangaladima, a Daular Fulani kuwa Madaki, Babban Dan Sarki ake ba. Ga tsarin sarautar Habe kamar Haka:-
.
A tsarin Mulkin Habe duk wata sarauta tana da ma'ananta kuma akwai aikin da aka rataya mata. Kuma wasu daga cikin wadannan sarautu suna karkashin kula na wasu manyan sarautu a wancan lokaci na Mulkin Habe. Misali, sarautar Kunkeli da wagu duk suna karkashin sarautar Madaki ne, kuma ko lokacin yaki suna cikin rundunan Madaki ne. Wasu kuma suna karkashin Dangaladima da irin aikin da aka dora masu. Kusan duk manyan Hakimai akwai wasu sarautu kanana da ke karkashinsu a tsarin Mulkin Habe.
.
1. Madawaki
2. Galadima
3. Wambai
4. Dallatu
5. Garkuwa Babba
6. Makama Babba
7. Kuyambana
8. Tafida
9. Wagu
10. Shenagu
11. Barwa
12. Wan'yan
13. Dan'ke'kasau
14. Sarkin Fada
15. Cincina
16. Jagaba
17. Bakon Borno
18. Gwabare
19. Magayaki
21. Jarmai
22. Ciritawa
23. Barde
24. Kingiwa
25. Barden kankana
26. Garkuwa kankane
27. Hauni
28. Turaki
29. Sarkin Ruwa
30. Fagaci
31. Dangaladima
32. Magajin Dangi
33. Sarkin zana
34. Makama karami
35. Ma'aji Babba
36. Ma'aji karami
37. Barden Maidaki
38. Kaigama
39. Baushe
40. Mai Dala
41 magajin Rafi
42. Barden yamma
43. Bijimin Arewa
44. Rubu
45. Bijimin Yamma
46. Magajin Nagaba
47. Bijimin Kudu
48. Borokan
49. Lifidi
50. Bagama
51. Kunkeli
52. Kufena
53. Tukura
54. Doka
55. Dankade
56. Falaki
57. Dan makwayo
58. Barayan yamma
59. Kware maza
60. Madaucin Arewa
61. Zanna
62. Kwarbai
63. Kacalla
64. Kilishi
65. Sarkin Rafi
66. Madugu
67. Kangiwa
68. Suluki
69. Bijimin Gabas
70. Uban Dawaki
71. Gatau
72. Dan Rimi
73. Sarkin Mai
74. Kaura
75. Madara
76. Magajin zakara
77. Iyan kurama
78. Magajin kwa
Wadannan su ne sarautun Mulkin Habe, kuma an ci gaba da amfani da su har zuwa yau lokacin Mulkin Fulani. Sai dai akwai bambancin wurin matsayin sarauta da tsare tsaren aiki a tsakanin wadannan Dauloli guda biyu kamar yadda aka ba da misali a baya. Kusan mafi yawancin sarautu da ake da su, sarautu ne na Habe, wadanda su suka kirkiro su daga baya Fulani suka ci gaba da amfani da su.
.
Mafi yawancin rarautun da fulani suka kafa su ne a sakamakon aikin addini, sai kuma lokacin Turawa suka zo suka tsara aikace aikace. Koda yake wasu daga cikin sarakunan Habe Musulmai ne, amma wasu suna bautar gunki da wasu al'adu. Amma a lura da wasu masu tsare tsare irin na musulunci kamar yadda aka ba da misali da sarkin zazzau Isiyaku Jatau, Sarki na 59 a Daular habe, wanda shi Musulmi ne.
0 Comments