ZAZZAU CIKIN KASASHEN HAUSA BAKWAI

ZAZZAU CIKIN KASASHEN HAUSA BAKWAI
.
Tarihin kasashen Hausa ya nuna cewa sun karu ne a karkashin wani mutum da ake kira Abu Yazidu wanda ake yi ma lakabi da suna Bayajidda Dan Abdullahi Sarkin Bagadaza wanda ya yi Hijira daga kasar Bagadaza ya shigo kasar Hausa tare da wasu daga cikin mayakansa inda ya shiga kasar Borno. Kuma anan ya auri diyar Mai Borno na wannan lokaci wadda ake kira MAGIRA. Bayan ya jima a Borno sai mai Borno ya fahimci cewa karfinsa zai yi yawa saboda haka ya yi yunkurin kashe shi amma bai sami nasara ba. Sai Bayajidda ya gudu zuwa Garun Gabas daga nan ya wuce zuwa Garin Gaya kuma ya bar matarsa a Garun Gabas kuma a wancan lokaci tana dauke da ciki a nan ta haifi da namiji Mai suna BIRAM. Wannan yaro shi ne ya girma har ya zama Sarkin Garun Gabas, inda ake cewa Biram ta Gabas daya daga cikin kasashen Hausa Bakwai.
.
Lokacin da Bayajidda ya isa kasar Gaya ya sami makeran karfe suka kera masa takobi daga nan ya wuce zuwa kasar Daura inda ya kashe Macijiyar Daura. A wannan jaruntaka da ya nuna wajen kashe wannan mashahuriyar Macijiya.
.
Sarauniya Daurama ta haifi Bawo Gara kuma shi ne ya haifi 'ya'ya shida wadanda su ne asalin Garuruwan Hausa guda shida. Gazaura wanda ta mulki Daura, sai Gunguma wadanda suke su tagwaye ne, daya ya yi Mulkin katsina daya kuma ya yi mulkin zazzau. Haka kuma Bagauda da Zamagari su ma tagwaye ne dukan su sun yi mulki. Bagauda a kano, Zamagari a Rano. Sai Duma wanda ya yi Mulki a Gobir.
.
Wannan wani bangare kenan na tarihin kafuwar kasar Hausa. Amma an sami dan bambancin bayani a kan wannan tarihi inda wasu marubuta suka yi dogaro da rubutaccen bayanin da wasu mashahurin Malami ya yi tare da dogaro da wani mashahurin Malami. Wadannan malamai su ne Sultan Muhammadu Bello da Sheikh Abdulkadir Almustapha. Wadanda suka yi zamani da shi cikin karni na goma sha tara (19).
.
Wannan bayani da suka rubuta cikin shekara ta 1820 ya nuna cewa dukkan wadannan kasashe suna karkashin Mulkin Shehun Borno ne. Kuma shi Bawo bawa ne na shehun Borno wanda yake ba'a san ko  daga ina ya fito ba, sai dai kawai Shehun Borno ya ba shi karfi na mulki na kula da wadannan kasashe a lokacin yana da 'ya'ya bakwai kuma da ya ga tsufa da ciwo sun tsam masa, sai ya dauki wadannan 'ya'yana shi ya ba su sarautun wadannan kasashe. Wannan shi ne bayanin wani bangare na Tarihin kasar Hausa.
.
Zazzau na daya daga cikin wannan zuri'a ta Abu yazid (BAYAJIDDA), kuma su ne suka kafa masarautar Habe a zazzau shi ne dalilinda ya sa zariya ta kasance cikin garuruwan da ake kira Hausa Bakwai, duk da samuwan tarihi daban-daban daga masana tarihi da malaman tarihi. Zariya dai ta kafu ne a karkashin Mulkin Habe sun kuma yi sarakuna har guda sittin (60),  a wannan kasa ta zazzau, kafin Fulani su karbi Mulkin kasar karkashin jihadin shehu Usman ibn Fodiyo. An kiyasta samin sanin shekarun Muhammadu Habu, wanda ya yi mulki daga 1505-1530 daga kansa ne aka fara lissafin shekarun sarakunan Habe na zazzau ban da sarakuna guda goma sha bakwai (17) da suka    Yi kafin shi. Watau, daga zamanin Gunguma zuwa zamanin Sarki Sukwana..
.
Daga: KASAR ZAZZAU AJIYA DA YAU (Facebook)
ko kuma zaku iya ziyartan shafin mu na yanar gizo-gizo ta www.kasarzazzau.tk

Post a Comment

0 Comments