TSARIN HAKIMAI DA AIKINSU DA KIRARINSU
.
KASHI NA UKU (3)
.
DALLATUN ZAZZAU
Wannan sarauta ta Dallatun zazzau, ita ma sarauta ce da ta samo salali daga Habe. Kuma aikin Dallatun a wancan lokaci yana da matsayi biyu ne. Na farko, shi ne kula da wurarbn da aka tsara don ajiye rundunar mayaka. Na biyu shi mataimaki ne na musamman na Galadima a kan harkokin cikin gida da rikon Gari. Sarautar Dallatu a karkashi Daular fulani, sarauta ce wadda ake ba dan Sarki ko kowane muhimmin mutum sai dai an fi ya ba da ita ga 'ya'yan Sarki. Ita ma wannan sarauta ta Hakimci ce. Akan kai wada ke rike da ita Hakimcin wata kasa. Wanda ya fara wannan sarauta ta Dallatu shi ne Malam Abdullahi kanen katukan zazzau Usman Tsoho (SABULU), A lokacin Malam Musa, Sarkin zazzau.
.
=== KIRARIN DALLATU ===
DALLATUN SARKI
GAZUMZUMIN RINJAWA,
WANDA YA HANA FADANCIN DARE,
MAJINA GISHIRN YARO, KOWA YA YI KURICIYA YA SHA TA.
DAN UBAN GABASAWA
.
Wannan shi ne kirarin Dallatu. Shi ma ana yi masa kirari da irin tasa kasaitar da matsayinsa da kuma jaruntakarsa.
.
Wadannan sarautu na Wambai da Dallatu ba su da wani muhimmanci a da kamar yadda suke a yanzu lokacin daular fulani. A wancan lokaci muhimmancin wadannan Hakimai shi ne yaki ba shugabanci ba. Kowa na kokari ne ya gwada irin tasa jaruntakar.
.
KATUKAN ZAZZAU
Sarautar Kavka ita ma sarauta ce ta Habe kuma tana daya daga cikin manyan sarautu na Hakimci. Wannan sarauta tana da matsayi na wakilcin Sarki a kasashen da aka fidar da sarki ko ya rasu. Katuka yakan tafi domin rikon wannan kasa. A yanzu wannan sarauta ta katuka ta sami daukaka ta koma saravar 'ya'yan Sarki a karkashin Daular Mulkin Fulani kuma sarauta ce da ake ba da ita hade da hakimcin kasa. Wanda ya fara wannan sarauta ta katuka shi ne Malam Usman Tsoho Sabulu, a zamanin Sarkin zazzau Malam Musa Bamalle. Amma daga baya ta koma sarautar 'yan sarki wanda ya fara wannan sarauta a 'ya'yan sarki shi ne Sarkin zazzau Malam Ja'afaru dan Isiyaku.
.
=== KIRARIN KATUKA ===
KA WUCE KACIRO KA GA ZUWAN MASU GARI,
KATUKA KAI NE BABBA,
DUMAN DUTSE GAGARA YARO FAFA,
JIRAYI NA SARKI
DAN UBAN GABASAWA.
Wannan Shi ne kirarin Katuka, kuma ana nuna irin matsayinsa da jaruntakarsa wajen yaki inda ake cewa Duman Dutse gagara yaro fafa, wuce kaciro ka ga zuwan masu gari. Ma'ana, shi ya wuce tsayawa daga wajen in ya iso Fada, ciki yake shiga.
.
Kusan duk wadannan sarautu da ake fada sun sami canjin matsayi da aiki ba kamar yadda suke a wancan lokaci na Habe ba. Sun daukaka a wannan zamani na Fulani kuma ba sa yin irin ayyukan da suke yi a da, cikin wannan zamani.
.
SARKIN RUWAN ZAZZAU
Sarautar Sarkin Ruwa ita ma wannan sarauta ta Habe ce kuma aikin wannan sarauta a wancan lokaci shi ne Manzo ko wakili a tsakanin Sarki da masunta da duk abin da ya shafi al'amuran ruwa, kamar kududdufi ko koramu da sauransu. Lokacin mulkin sarauniya Amina, shi ke kula da haka gulbi da ba ruwa.
.
Amma a yanzu sarauta ce ta 'ya'yan sarki, amma ana ba da ita ga muhimman mvane a cikin gari. Kuma a na ba mai wannan Sarautar Hakimcin kasa, cikin wannan Daula t Mulkin Fulani. Wanda ya fara wannan sarauta a Daular Fulani shi ne Malam Abdullahi na Anguwan Magajiya zariya a zamanin Sarkin zazzau Yamusa.
.
=== KIRARIN SARKIN RUWA ===
WUCE KUNYA MU JE ZUWA GIDA,
WUCE KUNYA JE ZUWA GARI,
BAMBARO NA BAKIN SARKI
DIYAM NA BAKIN NAMU.
.
Wannan shi ne kirarin Sarkin Ruwa. A na yi masa kirari da irin jaruntakarsa, kamar yadda aka ce masa wuce kunya mu je zuwa gida, wuce kunya mu je zuwa gari. Ma'ana, idan Hadarin ruwa ya taso to, yakan yi iyakan kokarinsa ya ga cewa ruwa bai taba sarki ba har ya kai gida. Haka kuma bambaro na bakin sarkh, na nufin ginshiki na kusa da sarki.
.
SA'IN ZAZZAU
Sarautar Sa'i na daya daga cikin sarautun da Daular Fulani suka kirkira. Kuma sarauta ce wadda ake ba mutum mai ilimi kamar sarautar Salanke ko wali. Aikin sarautar Sa'i shi ne karba da rabon zakka daga ko'ina cikin kasa, sannan ya gabatar da ita ga Sarki don rabo. Sannan kuma yana daya daga cikin manyan 'yan majalisar sarki ta bangaren abin da ya shafi Addini.
.
Wannan sarauta ta daukaka zuwa saravar 'ya'yan Sarki a wannan lokaci, d6in tana daya daga cikin saravar da ake ba su. Haka kuma ana ba muhimmi mai ilimi.
.
=== KIRARIN SA'I ===
SARKIN ZAZZAU NA FULANI
SARKIN ZAZZAU NA FULATAN
MAI JANGALI DA MUTANE
DIKKO SA'IN SARKKI
SA'IN MAI SA A YI DOLE
.
Wannan shi ne kirarin Sa'i, kuma ana nuna darajojin sarautar daga inda ta samo asali, wanda har yanzu da shi ake masa kirari kamar haka: Sarkin zazzau na fulatan. Ma'ana, Asalin wanda ya fara yin sarautar Sa'i shi ne, Abdulkarimu, kafin ya yi Sarkin zazzau, karkashin Daular fulani. Mai jangali da mutane, ne nufin ana yin jangali na fulani da Zakka duk suna hannunsa a wannan lokaci shi ne mai wannan ikon.
.
DANMADAMIN ZAZZAU
Sarautar Dan Madami na daya daga cikin sarautun da Habe suka kirkira kuma tana daya daga cikin sarautun cikin Gida a karkashin Galadima.
.
Wannan sarauta ta Dan Madami ta daukaka a cikin Mulkin daular Fulani. Ta koma sarautar 'ya'yan Sarki a yanzu , a kasar zazzau. Wanda ya fara yin wannan sarauta shi ne Malam Yaje Fulata, a zamanin Sarkin zazzau Malam Musa Bamalle.
.
=== KIRARIN DAN MADAMI ===
FASKARA KORA TAKON DAMISA
KISA DA MONO GOBARANKU FULANI
DA KWARI DA TUDU DUKA NAKU
.
Wannan shi ne kirarin dan Madami. Shi ma ana nuna irin daukakar mulkinsa da matsayinsa a cikin kirarinsa, kamar faskara kora takon Damisa. Ma'ana, ba ya gudun a wajen yaki. Kuma a sannu ake sa ma'anar takon Damisa, ke nan.
.
Zamu ci gaba inshaallahu
0 Comments