TSARIN HAKIMAI DA AIKINSU DA KIRARINSU
.
KASHI NA HUDU (4)
.
TURAKIN ZAZZAU (KARIMI)
Sarautar Turakin Zazzau, Sarauta ce wadda ta samo asali daga lokacin Mulkin Habe. Ma'anar Turaki, ita ce manzo a tsakanin Sarki da Madawaki, watau Turaki shi ke gabatar da sakonni a tsakanin Sarki da Madawaki, a bisa tsarin mulki a wancan lokaci.
.
Sarautar Turaki ta kasu kashi biyu Turaki karami da Turaki babba a lokacin Mulkin Fulanh a zazzau. Wannan sarauta ita ma ta sami Daukaka inda ta koma sarautar 'ya'yan Sarki a zazzau. Wanda ya fara wannan sarauta ta Turaki shi ne Malam Bayero dan sarkin zazzau Hammada. Ya yi sarautar Turaki Lokcin mahaifinsa ke sarkin zazzau.
.
=== KIRARIN TURAKI ===
TURAKI TURA KAN SARKI,
SURI MATATTARA KASA,
BUGAU ALKALIN YAKIN FADA,
FAGACIN MAJE DAKA ALLAH KA SO NA WAJE.
DAN UBAN GABASAWA
Kamar yadda aka yi bayani a cikin kirarin Turaki cewa fadancin Maje daka Allah ka so na waje wannan yana nuna matsayin sarautar Turaki a wurin Sarki. Ma'ana, ya zama sirrin Sarki kuma yardajje ga Sarki tun da zai ishe Sarki har cikin Turaka ya bayyana masa abin da yake so.
.
Wannan shi ne kirarin Turaki , kuma kirarinsa ya yi daidai da aikinsa. Misali wannan fadancin maje daka Allah ka so na waje, na nufin saboda Turaki ba shi da iyaka da shiga wurin sarkitduk abin da ya fada shi ake aiki da shi, domin shi ne kai-koma a wurin sarki. Kuma suri matattara kasa na nufin duk 'ya'yan Sarki, shi ne ke kai sako a tsakaninsu da sarki.
.
YARIMAN ZAZZAU
Wannan sarauta ta Yarima tana daya daga cikin sarautun da aka nada a lokacin Mulkin Fulani. Wannan sarautuna cikin saravu da aka aro a zamanin Sarkin zazzau na sha takwas (18), Shehu Idris, kuma sarauta ce ta 'ya'yan Sarki, wadda dan Sarki kawai ake bai wa Wannan sarauta. An fara nada ta a kan Alh. Murir Ja'afaru dan Sarkin zazzau Malam Ja'afaru dan Isiyaku. Wannan Sarauta ta samo asali ne daga Borno. Asalin wannan sarauta ana ba dan Sarki ne a tura shi bangare na Borno da ake kira Yeri a matsayin shugaban wajen daga. Ta haka aka sami kalmar Yarima, watau shugaban wannan wuri.
.
=== KIRARIN YARIMA ===
YARIMA DAMISAN 'YAN SARKI
YARIMA DAN MASU GARI
DAN BAKON RUWA DA CIYAWA
DAN UBAN GABASAWA
Wannan shi ne kirarin Yarima kuma ana nuna irin Gatanshi da matsayinsa a fada kamar yadda aka ce Yarima dan masu Gari, dan Bakon Ruwa da Ciyawa. Ma'ana, dan Sarki kenan. Duk idan ka ji an ce, masu Gari ko bakon ruwa da ciyawa, to Sarki ake nufi.
.
CIROMAN ZAZZAU
Wannan sarava ta Ciroma, sarauta ce ta Fulani a nan Kasar zazzau kuma sarauta ce aka fara nada ta a lokacin Mulkin Sarki na Sha shida (16) Sarkin zazzau Malam Ja'afaru na daular Fulani, kuma wanda aka fara nadawa shi ne Malam Aminu dan wali Haliru na gidan Mallahwa. Sarauta ce ta 'ya'yan Sarki a zazzau.
,
.Wannan sarauta an aro ta ne daga Borno kuma sarauta ce mai girma da daukaka. Kuma sarauta ce da ake ba dan Sarki na cikinsa kuma shi ke kula da dukkan bangarorin da 'yan uwansa suke kula da su.
.
=== KIRARIN CIROMA ===
CIROMAN SARKI
CIROMA YARIMA
GOGAYYA CIROMA
YARIMA DAMISAN 'YAN SARKI,
DAN UBAN GABASAWA.
Wannan shi ne kirarin Ciroma kuma ana nuna fifikonsa da matsayinsa a fada kamar haka Ciroma Damisan 'yan Sarki. Ma'ana, ana shakkun shi cikin 'ya'yan Sarki.
.
GALADIMAN ZAZZAU
Sarautar Galadima a zamanin Habe sarauta ce wadda ake ba amintaccen Sarki kuma shi ke rike Gidan Sarki da nauyin iyalan Sarki gaba daya idan Sarki ya fita zuwa yaki. Saboda wannan karfi da aka tara masa ya sa duk abin da ya zartar a gidan Sarki ya zauna.
Sarautar Galadima ta daukaka kuma ta sami matsayi a Mulkin daular Fulani inda ta tashi a matsayintana da lokacin Mulkin Habe. Sarauta ce wadda a Mulkin Fulani ake ba dan Sarki ko amintaccen Sarki kowane jarumi kuma yana daya daga cikin 'Yan Majalisar Sarki kuma cikin masu zaben sarki idan Sarki ya rasu, ko an fidda shi. Haka kuma ana ba shi Hakimtar kasa. Saravar galadima sarauta ce da habe suka kirkira ta daga baya Fulani suka gyarata suka daukaka ta zuwa sarautar 'Ya'yan Sarki ko kowane mazumuncin Sarki ko kowane mahimmin mutum a gari. Wanda ya fara wannan sarauta ta Galadima shi ne Galadima Dokaje na Unguwar Magajiya cikin Birnin zariya. Sarautar Galadima na daya daga cikin saravu masu asali. A duk inda ka je akwai wannan sarauta a kasar Hausa. Sarautar Galadima ta samo asali ne daga borno tun lokacin Mulkin Askiya a Kanem-Borno inda Borno ta ci da yaki sai ta ajiye Galadima a wurin a matsayin wakilin Shehun Borno. Daga nan ne aka sami wannan sarava ta yi karfi a ko ina cikin kasar Hausa.
.
=== KIRARIN GALADIMA ===
Wannan shi ne kirarin Galadima kuma cike yake da kalmomin zuga saboda kasancewarsa mai jiran gadon sarauta. Ma'ana, raba masu rana da hazo. A lokacin Habe idan aka ce Galadima to shi ne Magajin Sarki saboda haka ba sauran wani ya ce yana neman Sarki sai da kuma a yi ta neman sarautar Galadima. To, shi ne raba musu (gardama). Zuciya ta so magana, baki ya kasa fada. Ma'ana ya kosa ya hau Gadon sarauta.
0 Comments