TSARIN HAKIMAI DA AIKINSU DA KIRARINSU (5)

TSARIN HAKIMAI DA AIKINSU DA KIRARINSU
.
KASHI NA BIYAR (5)
.
MAKAMAN ZAZZAU (KARAMI)
Sarautar Makama a karkashin Mulkin Habe, sarauta ce wadda ake ba jarumi mai dabaru irin na yaki, aikin Makama a wannan lokaci shi ne mai rarraba mayaka mayaka kuma shi ne ke ajiye da kayan yaki a hanunsa. Haka kuma shi ke raba kayan ganima na yaki idan an samu.
.
Sarautar Makama karkashin Daular Fulani, sarauta ce ta Hakimci kuma daya daga cikin masu zaben Sarki a tsarin a tsarin Majalisar masu zaben Sarki. Wanda ya fara wannan sarauta shi ne Malam Abdulsalam Sarkin zazzau a lokacin Malam Musa Sarkin Zazzau. Sarautar Makama na daya daga cikin manyan sarautu a duk kasashen Hausa, ba ma kasar zazzau ba kawai, kusan duk kasashen Hausa. Makama na cikin manyan 'yan Majalisar Sarki kuma yama cikin masu zaben Sarki.
.
=== KIRARIN MAKAMA ===
ABDULLAHI MAKAMA
ABDULLAHI SA GARI GUDU
SHATARITA MAKAMA
FARIN GWANI SHA GUDA
TOGAI RUMFAR SARKI
Wannan shi ne kirarin Makama Karami, shi ne kirari irin na jaruntakar yaki da kuma irin matsayinsa a wajen sarki. Misali, an ce Abdallah sa Gari guda watau, jarunta kan ci Gari da yaki haka kuma Togai rumfar Sarki watau duk yadda za a yi yana nan tsare da Sarki cikin Rundunar yaki.
.
SARKIN FADAN ZAZZAU
Wannan sarauta ta Sarkin Fada tana daya daga cikin manyan sarautu na kusa da Sarki tun a wancan lokaci na Habe. Kuma shi ne Shugaban dukkan 'yan Majalisar Sarki a lokacin Mulkin Habe. Wannan sarauta ta Sarkin Fada ta kara daukaka a lokacin mulkin Fulani. Sarava ce ta Hakimci da  ake ba mutum mahimmi a kasar zazzau.
.
Wanda ya fara wannan sarauta ta sarkin fada shi ne Muhammad (DAMAGURU) Na kofar Bai (BANZAZZAU) a lokacin mulkin malam Musa. Sarkin Fada shi ne shugacn duk wani abu da sarki zai yi sako ko za a fada wa baki ko jama'a idan sarki ba zai magana ba ko ba zai karanta ba. Sannan sarkin fada shi ke kula da dukkan tsare-tsaren aikin mulki na fada da abin da ya shafi sarki. Haka kuma shi ne Alkalin manyan fadawan sarki in an sami kuskure ko laifi a tsakanin, ko gabatar da wani yaron sarki wanda ya yi laifi ga hukuma don hukunci. Shi ya sa sarautar take da girma a ko'ina cikin masarautan kasar Hausa ba zazzau kawai ba.
.
=== KIRARIN SARKIN FADA ===
FADA BABBA
DAGA RENO AKAN SAN DA KARO
DAGA TOZO AKAN SAN BAJIMI
TUKURA GIGITA MAZA
SARKIN FADAN SARKI
Wannan shi ne kirarin Sarkin fada inda aka bayyana irin karfin mulkinsa cikin Kirari
.
FAGACIN ZAZZAU
Wannan sarauta ta Fagaci, ita ma sarauta ce da ta samo asali daga Habe, kuma sunan wani daki ne hade da shigifa da ake kira Fagaci. Nan sarki ke zama da la'asar. Matsayin sarautar Fagaci shi ne Wakili ko Manzon sarki zuwa ga galadima da Dan galadima a kan aikin da ya shafi tsakaninsu da Sarki. Sarautar Fagaci, karkashin Kuma tana na daya daga cikin sarautun Majalisar Sarki kuma cikin masu zaben Sarki a yanzu a wannan masarauta ta zazzau. Wanda ya fara wannan sarava ta Fagaci a daular fulani shi ne Fagaci Ibrahim na gidan Barebari, a zamanin Sarkin zazzau Hanada dan yamusa.
.
�=== KIRARIN FAGACI ===
BINA BABBAN DAKIN SARKI,
BINA BABBAN DAKIN DODO,
DAKIN KASA DA KASA INDA GOBARA TA YI KUNYA,
FAGACIN UBAN GABASAWA.
Wannan sarauta tana da ma'anoni masu kama da juna. Fagaci dai wani wuri inda sarki ke zama ana kafin a kai wurin akwai wani Dutse, nan ake tsayawa kafin mai iso ya kai ka. Duk wanda ya isa wannan wuri sai a ce ya kai ga gaci, don daga nan sai wajen sarki. Shi ya sa ake cewa ya kai gaci. Bina Babban Dakin sarki, dakin kasa da kasa inda gobara tai kunya.
.
Wannan shi ne kirarin fagaci da irin matsayinsa a wajen sarki, ma'anar Bina sunan daki ne na alfarma a cikin gidan Sarki a karkashin wata shigifa da ake kira fagaci. Wannan daki ba mai zuwa sai wanda ya isa a wajen sarki.
.
MAKAMAN ZAZZAU BABBA
Sarautar Makama Babba ita ma kamar Makama karami ce sai dai aikinsu ne ba daya ba ana duk sarautu ne da suka samo asali a lokacin Mulkin Habe a zazzau. Wanda aka fara nadawa wannan sarauta shi ne Mal. Sharubutu a zamanin sarkin zazzau Malam Musa.
Aikin makama babba shi ne mai kula da al'amuran cikin gida kuma manzo na musamman a tsakanin Sarki da shuwagabannin addini kamar limamin Juma'a da manyan malaman Gari.
.
=== KIRARIN MAKAMA BABBA ===
ABDALLA SA GARI GUDU,
SHATARITA MAKAMA
MAKAMA BABBA
TOGAI RUMFAR SARKI
FARIN GWANI SHA GUDA
.
Wannan shi ne kirarin Makama Babba kusan duk kirarinsu daya ne da Makama Karami, duk dai sarauta ce ta Jarumai makusantan Sarki.
.
KUYAMBANAN ZAZZAU
Wannan sarava ta kuyambbana ita ma sarauta ce da ta kafu tun daga lokacin Habe, kuma sarava ce da ake ba bawan Sarki kowane muhimmin mutum a wancan lokacin kuma aikin wannan sarava shi ne babban mataimaki ga Madawaki, duk wani cu da madawaki ba yai sami daman gabatarwa ba to, Kuyambana shi ne ke gabatarwa a madadin Madaki. Yanzu cikin Mulkin Fulani wannan sarauta ta kuyambana ta sami daukaka tana daga cikin manyan Hakimai masu kasa. Wannan sarava tun bayan mulkin Habe ba a kara yin ta ba har sai lokacin Sarkin zazzau  Abdulkarimu. Wanda aka ba wannan sarauta shi ne kuyambana mai roron aiki. Kuma har yanzu da shi ake yi ma sarautar kirari.
.
=== KIRARIN KUYAMBANA ===
NAMIJIN FADA DA DAMISA
MASU GARI SU SHA WUTA AIKI YA KARE
KUYAMBA NA MAI RORON AIKI
.
Wannan shi ne kirarin Kuyambana, irin yadda ake nuna matsayinsa da jaruntakarsa, cikin kirari, kamar yadda aka ce namijin fada da Damisa. Ma'ana, mai yaki da abin da ake jin tsoro ( damisa) wannan kwarzantawa ce da kirari ko jaruntaka.
.
KARIN BAYANI
1. Sarutar kuyambana a wani kaulin na tarihi an ce tasamo asalita ne daga kalmar da yake kira na masu aiki a lokacin Habe idan zai kira sbabbin ma'aikatanshi sai ya ce, " KU 'YAN BA NA" daga nan aka sami kalmar Kuyambana.
.
2. Idan an ce sarauta ta cyi ana nufin a wancan lokacin na Mulkin Habe, amma ba ana nufin cewa wanda ke rike da sarautar bawa ne ba. Kuma an samu canje-canje inda wasu saravu suka tashi a saravar Bayi suka k6a saratar 'ya'yan Sarki a sakamakon  Karbar Mulki na fulani su ka yi a Hannun Habe. �

Post a Comment

0 Comments