TSARIN HAKIMAI DA AIKINSU DA KIRARINSU (6)

TSARIN HAKIMAI DA AIKINSU DA KIRARINSU
.
KASHI NA SHIDA (6)
.
SALANKEN ZAZZAU
Sarautar Salanke ita ma ta samo asali ne tun lokacin Habe kuma tana daya daga cikin manyan sarautu masu maìmmanci. Wannan sarava tana kula da harkokin Addinin Musulunci ne kuma shi ne ke gabatar da Addu'oi a lokutan sallolin Idi. Haka kuma shi ne ke jagorantar sallar Jana'iza ta duk wani Hakimi da ya rasu kuma yana daya daga cikin masu zaben Sarki a wancan lokaci. Shi ne kuma Alkalin Mata a fada idan shari'a ta samu.
.
Sarautar Salanke ta ci gaba da matsayin da take da shi a lokacin Mulkin Fulani ta kasance mai kula da  harkokin shari'a kuma ta kasance saravar 'ya'yan Sarki a yanzu. A farkon lokacin Mulkin Fulani Salanke yana da kotu na musamman don shari'a a wancan lokaci. Wanda ya fara wannan sarauta a Daular Fulani shi ne Salanke Sidi a zuri'ar Sarkin zazzau Malam Musa.
.
=== KIRARIN SALANKE ===
SALANKEN SARKI
BABBAN ALKALI NA GABAN SARKI,
BUGAU ALKALIN YAKIN FADA
Wannan shi ne kirarin salanke. Ana nuna irin martabarsa da aikinsa, kamar yadda aka ce babban alkali ne gaban Sarki, bugau Alkalin yakin Fada. Ma'ana, Alkali mai shari'a a gaban Sarki kuma Alkalin Sarki. Wannan shi ne kirarin Salanke.
.
BARDEN ZAZZAU
Sarautar Barde, sarautar ce ta Habe wacce Fulani suka gada kuma sarauta ce ta Mayaka ko Jarumai. Ma'anar sarautar Barde ita ce, duk lokacin da sarki zai yi wata tafiya mai nisa, Barde zai kasance a gca har sai ya tabbatar da masaukin Sarki akwai kyakkyawan tsaro a wurin kafin Sarki ya iso ya sauka. Kuma yana binciken inda abokan gaba suke lokacin yaki sannan yana binciken inda abokan yaki suka buya don kawo harin samame. Wanda ya fara wannan sarava ta Barde shi ne Barde Zunnan a lokacin Mulkin Malam Musa Sarkin Zazzau.
.
=== KIRARIN BARDE ===
FASA GARI BATUYA,
KIBIYAR DAFIN MAZA,
GOBARAR GASHIN GARI,
GOBARAR GASA ARNA
SA TAKABA SA TAKABA
Wannan shi ne kirarin Barde da irin Jaruntakarsa
.
KARIN BAYANI : Saravar Barde ta kasu da dama a zazzau. Misali, akwai Barden zazzau da Barden Kankana da Barden Maidaki da Barden gabas da Barden Yamma da Barden Arewa da Barden Kudu. Sai dai kowane daga ciki akwai irin matsayinsa da dauka akan jaruntarsa kamar yadda aka yi bayani.
.
SARKIN YAKIN ZAZZAU
Wannan sarauta ta Sarkin yaki sarauta ce wadda ta sami asali tun lokacin Mulkin Habe. Kuma Fulani sun ci gaba da rike ta da matsayinta na Shugaban rundunoni na mayaka daban-daban. Wannan sarauta ana ba mutum ne jarumi. A lokacin Fulani, Sarkin Yaki shi ke tafe da rundunar mayakan Sarki, kuma yakan ja sansani daban na shi a lokacin yaki. Wanda ya fara wannan sarava a Daular Fulani shi ne Sarkin Yaki mai Zabo a zamanin Malam Musa Sarkin Zazzau.
.
=== KIRARIN SARKIN YAKI ===
KURAWA BA JINI ZUBA,
KWASAU MAI KERAN YAKI,
RIJIYAR TSAKAR DAWA BAKINDA TSANTSANI.
.
�TURAKIN ZAZZAU BABBA
Wannan sarauta ta Turaki sarauta ce da ta samo asali daga sarautun Habe, amma a lokacin Mulkin Fulani aka raba ta zuwa Turaki Babba da Turaki Karami. Kuma sarauta ce ta cikin gida, tana daya daga cikin sarautu masu kai da komowa a cikin Gidan Sarki a wancan lokaci na Mulkin Habe. To amma yanzu, a Mulkin Fulani sarauta ce wadda ake ba wani mahimmi a gari ko kasa. Aikinsa ya bambanta da lokacin Mulkin Habe. Wanda ya fara wannan sarauta ta Turaki Babba Shi ne Turakin zazzau Baidu a zamanin Malam Musa Sarkin zazzau.
.
=== KIRARIN TURAKI BABBA ===
TURAKI TURAKI,
SHURI MATATTARA KASA,
BUGAU ALKALIN YAKIN FADA,
TURKE MADAURA GIWA,
DAN UBAN GABASAWA.
Wannan shi ne kirarin Turaki Babba, shi ma a na nuna karfin sarautarsa da irin daukakarsa cikin kirarinsa, kamar haka: suri matattara kasa. Ma'ana, suri wani gini ne da gara take yi ko kuma kasa da take  tonawa daga kasa ta yi waje da ita kamar gini, to, shi Turaki mattara 'Yan Sarki ne a ka'idar sarautarsa.
.
MA'AJI BABBA
Sarautar Ma'aji ta kasu kashi biyu ne da babba da karami kusan kuma duk aikin su daya ne sai dai bambancin ciki da waje. Ma'aji Babba Hakimi ne mai kula da abin da ake samu a waje kuma suna hannunsa a duk lokacin da aka bukaci karba, sai a zo gare shi. Wannan sarauta daga baya ta zama sarautar Hakimci karkashin Daular Fulani inda ake ba da ita zuwa Hakimcin wata kasa, a cikin masarautar zazzau. Wanda ya fara wannn sarauta shi ne Ma'ajin zazzau Jibirin a zamanin Sarkin zazzau Malam Musa na gidan mallawa, amma a na kiran wannan sarauta Ma'aji saboda shi ke rike da dukiyar kasa.
.
=== KIRARIN MA'AJI BABBA ===
KAWATA SARKIN KAWATA
KAWATA RAKUMIN MASU GARI
KAWATA SARKIN MA'AJI
Wannan shi ne kirarin Ma'aji Babba a matsayin sarautarsa da kwarjininsa a Fada.
.
MA'AJI KARAMI
Wannan sarauta ta Ma'aji Karami ita ma ta sami asali ne daga Mulkin Habe aikin wannan sarauta shi ne ya ajiye duk abin da aka samu daga Kudancin Zazzau. Haka idan bukata ta zo sai a je gare shi a karbo. A lokacin Fulani an raba aikin Ma'aji Babba da Ma'aji Karami inda aka raba su. Ma'aji Babba na gida shi kuma Karami yana waje a kasar Kaciya. Wanda ya fara yin wannan Sarauta shi ne Ma'aji yahaya a zamanin Sarkin zazzau Malam Musa kuma shi ne Hakimin Kaciya shi ya sa ake masa lakabi da ma'ajin Kaciya.
.
=== KIRARIN MA'AJI KARAMI ==
KAWATA SARKIN KAWATA
KAWATA RAKUMIN MASU GARI
KAWATA SARKIN MA'AJI
Wannan shi ne kirarin Ma'aji karami. Kirarin Ma'aji karami da na Ma'aji Babba kusan duk daya ne.�

Post a Comment

0 Comments