TSARIN HAKIMAI DA AIKINSU DA KIRARINSU
.
KASHI NA BAKWAI (7)
.
MADAUCIN ZAZZAU
Wannan sarauta ta Madauci ita ma sarauta ce da ta sami asali daga Habe, kuma tana daya daga cikin sarautu na masu yi ma Sarki hidima a Gida a wancan lokaci amma a zamanin Fulani wannan sarauta ta sami daukaka inda aikin ya canja. Sarautar Madauci ta koma sarautar Hakimci kuma shi ne ke ajiye duk kayayyakin da ake ba Sarki idan Sarki ya rasu Kamar Takobi da Malfa da Kandiri da ma kayayyaki kamar sandan Girma da Tuta duk wadannan Madauci zai dauka ya ajiye. Amma an sami canji inda aka mai da wannan sarauta ta Hakimci kuma aka nada Madauci cikin Gidan Sarki wanda duk wannan ayyuka suka koma hannunsa. Shi kuma Madauci ya zama shi ke rike da kula da dukkan dabbobin Sarki wanda aka kawo ko aka samu a sakamakon yaki. Wanda ya fara yin wannan sarauta shi ne Madauci Muhammadu Uban Madauci Jibiril (KERAU) Kakan Madauci Ibrahim Bagudu, a zamanin Malam Musa Sarkin Zazzau.
.
=== KIRARIN MADAUCI ===
TSARA YA GAMU DA TSARI
MAGANIN GWAZA TOKA
MAGANIN KARARA SOSO
Wannan shi ne kirarin Madauci ana nuna jarumtakarsa a cikin kirarinsa tare da karfin Mulkinsa.
.
KARFEN DAWAKIN ZAZZAU
Wannan sarauta ta Karfen Dawaki tana daya daga cikin Sarautun Habe wanda Fulani suka gada a matsayin da take. Ita wannan sarauta ta Karfen Dawaki ana ba Babban Dan Madaki ne ko kuma Autan Sarki, watau dan da Sarki ya haifa na Karke. Wannan sarava har yanzu wannan matsayi take a kai karkashin Daular Fulani. Wanda ya fara wannan sarauta shi ne Hammada dan Sarkin Zazzau yamusa Kafin ya yi sarautar wali a lokacin da Mahaifinsa ke Madaki.
.
=== KIRARIN MADAKI ==
KARFEN DAWAKI SARKI
KARFEN DAWAKI DODO
KARFEN DAWAKI UBAN GABASAWA
.
DAN MASANIN ZAZZAU
Wannan sarauta ta Danmasani tana daya daga cikin sarautu wanda Fulani suka nada ta a kasar Zazzau. An fara nada wannan sarauta a zamanin Sarkin zazzau na goma sha bakwai (17) Alh. Muhammadu Aminu na Daular Fulani. Wannan sarauta ce da ake ba mutum Mai ilimi kuma Haziki kwarai. A yanzu wannan sarauta ana ba da ta ga kowane muhimmin mutum. Wanda aka fara nadawa wannan sarauta shi ne Malam Abbas Nuhu na Unguwar Kwarbai.
.
=== KIRARIN DAN MASANI ===
DAN MASANIN DODO
DAN MASANIN SARKI
DAN MASANIN UBAN GABASAWA
.
TAFARKIN ZAZZAU
Wannan sarauta ta Tafarkin sarauta ce wadda ta samu asali tun daga lokacin Habe kuma aikinta ya ci gaba har lokacin fulani suka karbi mulki. Tafarki shi ne wanda ke fitar da hanya kuma ya yi jagora zuwa ga inda za a. Wannan sarauta ta inganta kwarai lokacin Fulani ta zama sarauta ta Hakimci mai girma kuma ana ba da wannan sarauta ga 'ya'yan Sarki da kowane muhimmin mutum a yanzu.
.
=== KIRARIN TAFARKI ===
JA MAKAFI NA ALLAH
JA MAKAFI NA SARKI,
SARKIN TAFARKIN SARKI,
TAFARKI UBAN GABASAWA.
Wannan shi ne kirarin Tafarki ana nuna matsayin aikinsa da mulkinsa kamar haka ja makafi na Allah, ja makafi na Sarki. Ma'ana, shi ne ke da ilimin zuwa wuri don sa a fitar da hanya saboda haka, shi ke da ilimin tafiya.
.
Sarautar Tafarki tana daya daga cikin sarautu da ke da Hakimi a karkashinta. Wannan Hakimi Shi ne Madakin Tafarki. Itama wannan sarauta ce da ake nada ta a gaban Sarki kamar yadda ake nada Dangaladiman waziri, ko Galadiman Fada. Duk ana nada irin wadannan sarautu ne a gcan Sarki kamar yadda aka nada kowane Hakimi da Busa da Farai.
.
WAN'YAN ZAZZAU
Wannan sarauta ta Wan'ya tana daya daga cikin manyan sarautu a zamanin Habe, kuma ita ma sarauta ce da ake ba kawun sarki. Wannan sarauta an fara ta ne a lokacin da Fulani suka canza mata suna daga Wan'iya zuwa Wan'ya. Yanzu wannan sarava tana daya daga cikin manyan sarautun Hakimci a Kasar zazzau.
.
Wanda ya fara wannan Sarautana Wan'ya shi ne Malam Yero a zamanin Sarkin Zazzau Malam Yero na Gidan Barebari. An sami tsawon lokaci babu saravar Wan'ya har sai zuwa lokacin Yero sarkin Zazzau.
=== KIRARIN WAN'YA ===
DAN IYAN SARKI
DAN IYAN DODO
DAN IYAN UBAN GABASAWA
.
JISAMBON ZAZZAU
Wannan sarauta ta Jisambo Sarava ce wadda ta samo asali tun daga lokacin Mulkin Habe kuma yana daga cikin Hakiman Sarki masu kula da bangarori na gari. Wannan sarauta ta kara daukaka a lokacin Mulkin Fulani kuma sarauta ce da ake ba 'ya'yan Sarki da Muhimmin mutum a gari ko a kasa. Wanda ya fara sarautar Jisambo a Mulkin Zazzau a Unguwar Bishar. Aikin Jisambo na daya daga cikin ayyukan ofishin Sarki. Yana gabatar da ayyuka tare da yi ma Sarki bayanin aiki.
.
=== KIRARIN JISAMBO ===
JIRGI MAI ATA GWANNI,
BA A MAGAJI DA YARO,
BA A YI DA KARAMI DATTIJO,
JISAMBON UBAN GABASAWA.
Wannan shi ne kirarin Magaji Jisambo.
.
MARAFAN ZAZZAU
Wannan sarauta ta Marafan zazzau, sarauta ce da aka fara ta lokacin Mulkin daular Fulani a lokacin Sarki na sha bakwai (17) a mulki Daular Fulani. Wannan sarauta ta Hakimci ce kuma tana daya daga cikin sarautu na manyan Hakimai. Wanda aka fara nadawa shi ne Mal. Yusuf na Unguwar Iya.
.
=== KIRARIN MAFARA ===
MARAFAN SARKI,
MARAFAN DODO,
MARAFAN UBAN GABASAWA.
.
MAGAJIN MALAM ZAZZAU
Wannan sarauta ta Magajin Malam Sarauta ce ta Habe kuma ita ce sarauta da take wakiltar masaravar Barno a lokacin da Barno ta ci wasu kasashe da yaki har da zazzau. Wannan sarauta ta Magajin Malam daga nan ta sami asali a dalilin haka kuma tana cikin sarautu masu asali a zazzau. Daga baya lokacin Fulani aka karrama ta da daraja ana ba da wannan sarauta ce ga mutum mai ilimi da hazaka.
.
=== KIRARIN MAGAJIN MALAM ===
MAGAJIN MALAM SARKI,
MAGAJIN MALAM DODO,
MAGAJIN MALAM UBAN GABASAWA
0 Comments